Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ta Saki Bafalasdine Mafi Dadewa A Gidan Yarinta
Published: 26th, January 2025 GMT
Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa
Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas.
A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza.
Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke masa hukuncin daurin rai da rai kuma ya shafe shekaru 40 a jere a gidajen yarin haramtacciyar kasar Isra’ila.
An kama Al-Tous ne bayan an fafare shi a lokacin da yake cikin wata mota ta kungiyar Fatah da ta kai hare-hare da dama kan wasu wurare da dama a haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Beit Laham.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Karrama ‘Yan Wasan Kwallon Kwando Na Mata
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere.
A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mai wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kowane dan wasa zai karbi dala 100,000, yayin da koci da kungiyar kwararru za su samu dala 50,000 kowanne, tare da karramawar kasa ga daukacin kungiyar. Ya kuma yi alkawarin karin tukuicin da zai zo.
Shettima ya ce ba wai don murnar nasarar da kungiyar ta samu a cikin shekaru 78-64 ne kawai ba, har ma da sanin tsayin daka, aiki tare, da kuma alfahari da suka kawo wa al’ummar kasar.
Ya bayyana wannan nasara a matsayin wata alama ta hadin kai da kuma tabbatar da abin da Najeriya za ta iya cimma idan al’ummarta suka yi aiki tare.
Mataimakin shugaban kasar ya yabawa kociyan kungiyar Rena Wakama, wacce ta kafa tarihi a matsayin daya daga cikin mata masu horar da ‘yan wasan kwallon kwando na Afirka, inda ya kira ta a matsayin “masoya kuma abin zaburarwa ga ‘yan mata a fadin Najeriya.”
Ya kuma yabawa Amy Okonkwo, ‘Dan wasan da ta fi kowa daraja a gasar, da Ezinne Kalu, wanda ya fi zura kwallaye a wasan karshe, saboda irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar kungiyar.
Da yake karin haske kan muhimmancin nasarar, Shettima ya jaddada cewa, matan Najeriya a kodayaushe sun kasance abin alfaharin kasa a fagen wasanni daban-daban, tun daga Super Falcons zuwa wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, da kuma wasan kwallon kwando.
Ya ba da tabbacin cewa a karkashin gwamnatin shugaba Tinubu, za a mayar da wasannin motsa jiki a matsayin wani muhimmin ginshiki na ci gaban kasa—da ilimi, ababen more rayuwa, diflomasiyya, da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.
Ya kuma yabawa hukumar wasanni ta kasa karkashin Mallam Alabi, da hukumar kwallon kwando ta Najeriya karkashin jagorancin Malam Ahmadu Musa Kida, bisa gyara da jajircewa da suka yi wajen bunkasa hazikan ‘yan wasa da kuma tallafawa ‘yan wasa.
Bikin da aka yi a fadar gwamnati ya nuna ba tukuici ne ga D’Tigress ba, har ma da wani sako mai karfi wanda idan aka gane da kuma goyon bayansa, na iya sauya wasannin Najeriya da zaburar da tsararraki.
Bello Wakili