Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yaba Da Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka Zagaye Na Biyu A Birnin Roma
Published: 20th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tattaunawa da Amurka an yi ta ne cikin yanayi mai inganci da hangen nesa
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, wadda Oman ta shiga tsakani a birnin Roma na kasar Italiya, da cewa an gudanar da shi cikin yanayi mai ma’ana da hangen nesa.
A cikin wata sanarwa bayan tattaunawar, Araqchi ya yi nazari kan yanayin tattaunawar, inda ya bayyana cewa: “Sun gudanar da shawarwari na tsawon sa’o’i hudu a ci gaba da zaman da aka yi a baya, kuma sun samu kyakkyawar fahimta kan ka’idoji da manufofi da dama.”
Ya ci gaba da cewa: An amince da a ci gaba da tattaunawa, da shiga matakai na gaba, da fara taron kwararru. An shirya gudanar da tattaunawar fasaha a matakin kwararru a masarautar Oman daga ranar Larabar wannan makon.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar.
A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai 6 sannan wasu 22 suka ji rauni.
Yankin Sistan Baluchistan dai ya dade yana fama da hare-hare na wannan kungiyar, kuma tana da sansani a cikin kasar Pakistan wacce take makobtaka da kasar a kudu maso gabacin kasar.