‘Yansanda Sun Kama Mutane 157, Sun Ƙwato Bindigu Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Published: 17th, April 2025 GMT
Bakori ya ce, makaman da ake zargin an dauko su ne daga jihar Filato, ana shirin kaddamar da wani mugun nufi ne acikin Kano da kuma jihohin da ke makwabtaka da ita.
Ya kara da cewa, bisa ga sahihan bayanan sirri, jami’an sun kai samame a wata maboya da ke Kuntau da Gwale, inda suka bankado yadda kungiyar ke gudanar da muggan ayyukanta.
A wani samame da jami’an ‘yansandan suka gudanar sun kama wata babbar mota makare da buhunan siminti amma kuma an boye kwalaye shida wanda ake zargin kwayar tramadol ce da kudinsu ya haura Naira miliyan 150.
An kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu akan safarar kwayar da aka dauko daga Sokoto zuwa jihar Jigawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yan Daba
এছাড়াও পড়ুন:
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025
Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025
Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025