An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa
Published: 16th, April 2025 GMT
An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wani sabon harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Garaha Lar da ke jihar Adamawa. Shugaban karamar hukumar Hong, Honarabul Usman Wa’aganda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, wani mazaunin garin ya ɓata yayin da maharan suka lalata gidaje da kadarori.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe
Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki.
Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a Dam ɗin Dadin-Kowa.
Matsalar ta sa ɗan Majalisar Tarayya na Yamaltu Deba, Inuwa Garba, ya kai koke gaban Majalisar Wakilai, inda ya nemi gwamnati ta hanzarta kawo wa mazauna yankin ɗauki.
Ya ce, “Ta’addancin Dorinar ya yi yawa. Idan ba a taimaka mana ba, za ta ci gaba da kashe mutane da lalata amfanin gona.”
A makon da ya gabata, Dorinar ta farmaki wani matashi mai suna Sama’ila Garba (Mai Lasa), bayan ya faɗa cikin ruwa.
Shaidu, sun ce dabbar ta yi ƙoƙarin kashe matashin, ta yadda hanjin cikinsa sai da ya fito, kafin a ceto shi.
Garba Zafi, ɗan uwansa, ya ce Sama’ila ya je bakin ruwa ne kawai sai ya ji ya faɗa, daga nan Dorinar ta afka masa.
Wani mazaunin garin, Akilu Gyara Sa’a, ya roƙi gwamnati ta kai musu agaji duba da yadda rayuwar mutane ke da muhimmanci.
Ya ce: “Dorinar tana lalata gonaki, tana kashe mutane. Gwamnati ta hanzarta magance matsalar kafin abin ya ta’azzara.”
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce zai bincika domin samun cikakken bayani kan lamarin.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ƙarin haske kan lamarin ba.