HausaTv:
2025-12-07@15:40:46 GMT

‘Yan tawayen Sudan sun kafa tasu gwamnati

Published: 16th, April 2025 GMT

Yan tawaye a kasar Sudan sun sanar da kafa tasu gwamnati, bayan shekara biyu ana gwabza fada a kasar.

Shugaban rundinar kai daukin gaggawa ta (RSF), Mohamed Hamdan “Hemedti”, ya ce an kafa gwamnati a yankunan da kungiyarsa ke iko da su, musamman a yammacin Darfur.

Dagalo ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a ranar Talata, inda ya ce, “A wannan ranar tunawa, muna alfahari da ayyana kafa gwamnatin zaman lafiya da hadin kai.

 Ya kuma ce za a kafa majalisar shugaban kasa mai mambobi 15 da ke wakiltar dukkan yankunan Sudan.

Janar din wanda tuni Amurka ta kakabawa takunkumi bisa zarginsa da hannu a kisan kiyashin da aka yi a yankin Darfur, ya ce wasu kungiyoyi masu dauke da makamai kamar wani bangare na kungiyar ‘yantar da ‘yancin kai ta Sudan, sun shiga wannan gwamnatin.

Masana da daman a ganin wannan a matsayin koma baya ga duk wani yunkuri da ake na samar da zaman lafiya a wannan kasa.

Tun daga watan Afrilun 2023, ne fada tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa na FSR ya barke lamarin da ya jefa kasar cikin rudani.

Akalla mutane 24,000 ne aka kashe, sannan Sama da mutane miliyan 13 ne suka rasa matsugunansu, ciki har da miliyan 4 da suka yi gudun hijira zuwa kasashe makwabta.

 A kwanakin baya ne dai shugaban mulkin sojin na Sudan, Janar Al-Burhan, ya sanar da kwace iko da Khartoum babban birnin kasar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara.

Yayin da yake bayyana dalilin sauya sheƙar, Amaewhule ya ce sun bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin jam’iyyar.

Bugu da ƙari, a wani mataki da ake ganin na ƙoƙarin kaucewa gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 daga Gwamna Siminalayi Fubara ne, Kakakin ya sanar da dage zaman majalisa har zuwa watan Janairu 2026.

Ayyukan majalisar a kwanakin baya-bayan nan sun nuna cewa har yanzu tsugune ba ta ƙare ba tsakanin bangaren zartarwa da majalisar jihar.

A watan Maris 2025, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamna da majalisa wanda kusan ya jawo rugujewar tafiyar da mulki a jihar.

Shugaban ƙasa ya kuma tsige Gwamna Fubara, mataimakinsa da kuma dakatar da majalisar jihar.

Sai dai an dawo da gwamnan da ’yan majalisar a jihar bayan an ɗage dokar ta-bacin a watan Satumba, tare da fatan cewa zaman lafiya ya dawo tsakanin bangarorin biyu.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin
  • Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi
  •  Dubban Mutane Suna Guduwa Daga  Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada
  • Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan
  • Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati
  • Gasar FIFA: Iran Ta Fada Cikin Group Mai Sauki A Gasar Kwallon Kafa Ta FIFA 2026
  • Yaƙin M23 Ya ci Gaba a Congo Duk da Sulhu da Rwanda
  • Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
  • Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe
  • Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15