HausaTv:
2025-07-09@07:26:05 GMT

Netanytahu Ya Fusta Da Furucin Kasar Canada Akan Kisan Kiyashi A Gaza

Published: 11th, April 2025 GMT

Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney  Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.

Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.

Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai.

Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa, bai ji kamlar kisan kiyashi ba, a cikin abinda aka ambata.

 Wannan bai hana Fira ministan na HKI sukar takwaransa na Canada ba,tare da bayyana shi a matsayin mai kin jinin yuhudawa.

Su kuwa kungiyoyin kare hakkin bil’adama na cikin kasar Canada sun bayyana ja da bayan da Fira minstan ya yi da cewa, ba abinda za a laminta da shi ba ne, ya zama wajibi a gare shi da ya goyi bayan MDD da kungiyoyin kasa da kasa na kare hakkin bil’adama akan cewa; Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne.

Alaka a tsakanin HKI da kuma kasar Canada suna kara kamari,a lokacin da kungiyoyin kasa da kasa suke kara yi wa Tel Aviv matsin lamba akan kawo karshen yakin da take yi a Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kisan kiyashi Fira ministan kasar Canada

এছাড়াও পড়ুন:

Al’ummar A sassan Duniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa

An sake gudanar da wani sabuwar zanga-zanga a manyan biranen duniya domin neman kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza

A jiya asabar ne aka sake gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a kasashe da dama na duniya domin nuna adawa da hare-haren da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa kan zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 192,000 tare da jikkata yawancinsu mata da kananan yara.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, mutane da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ma’aikatar harkokin wajen kasar a Quito babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a zirin Gaza.

Masu zanga-zangar sun yi kira da a kawo karshen yaki da kisan kare dangi a Gaza. Sun daga tutocin Falasdinawa da tutocin nuna kyamar yaki, yayin da wasu ke dauke da jajayen fulawa da aka lullube da fararen fulawa, wanda ke nuna alamar girmamawa ga yaran Gaza da aka kashe.

A Faransa, masu zanga-zangar sun yi maci a kan titunan birnin Paris, suna neman kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi kan al’ummar Falasdinu.

Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da rashin mutunta dokokin kasa da kasa tare da yin kira ga kasashen yamma karkashin jagorancin Faransa da su kakaba wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila takunkumi mai tsanani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Tabbatar Da Cewa Tana Iya Yakar Amurka Da HKI A Lokaci Guda
  • Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Godewa JMI Dangane Da Tallafawa Kungiyar Saboda Gwagwarmaya Da HKI
  • Iran Za Ta Yi Nazarin Sabuwar Gayyatar Da Amurka Ta Yi Mata Na  Sabuwar Tattaunawa
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
  • Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin HKI A Kasar Yemen
  • Falasdinawa Kimani 635 Amurka da HKI Suka Kashe A Cibiyoyin Karban Abinci A Gaza
  • China Ta Maida Martani da Haka Kayakin Kiwon Lafiya Na Tarayyar Turai Shigowa Kasar
  • Al’ummar A sassan Duniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Da Tawagarsa Sun Isa Kasar Brazil Don Halartar Taron BRICS Karo Na 17