2025-09-18@01:00:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 19
«safarar ɗan Adam»:
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sanya tarar kuɗi kan masu aikata ayyukan da suka shafi rashin ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan salla, domin kare mutunci, tsaro da kuma zaman lafiya. Sabbin matakan, wanda za a fara aiwatarwa nan take, sun shafi masu sanya kaya marasa mutunci a bainar jama’a, da masu kunna kiɗa lokacin salla, da masu bahaya ko zubar da shara a wuraren da doka ta haramta. Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13 a Borno Hisbah ta kama mai safarar mutane da mata 12 A cewar sabuwar doka, duk wanda aka kama da kunna kiɗa a lokacin salla zai biya tara ta Riyal 1,000 (kimanin Naira 390,000) a karon farko, kuma idan aka sake kama shi, tarar...
Jam’iyyar NNPP wato New Nigeria Peoples Party, ta lashe zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da ke Jihar Kano. Babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Hassan Adamu ne ya bayyana hakan da misalin ƙarfe 12:36 na daren Asabar wayewar gari Lahadi. Farfesa Hassan Adamu Shitu, ya bayyana ɗan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 16,198, inda ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar APC —All Progressives Congress — wanda ya samu ƙuri’u 5,347. Dokta Ali Hassan Kiyawa na jam’iyyar NNPP shi ne ya yi nasara a kan Ahmad Muhammad Kadamu na jam’iyyar APC bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar
Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna. Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin. Dattijon ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa na zuwa gona, lokacin da wasu tankokin dakon gas biyu suka kama da wuta bayan su gogi juna. Mai auran babban ’yar marigayi Malam Abdullahi Magaji, ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru, akan rasuwar marigayin. ya ce, “A jiya da safe marigayin yana kan babur ne a kan hanyarsa na zuwa gona, sai waɗannan motocin ɗakon man gas...

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A CPC, Haruna Sa’eed Kajuru, Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Kisan ‘Yan Zariya A Filato
Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan. Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a Zaria, inda ya nuna alhini da ta’aziyya ga dangin waɗanda wannan al’amari ya shafa. Tsohon Akanta Janar na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Kajuru, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na kashe...
Datti Baba-Ahmed, wanda ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ADC za ta fuskanci babban ƙalubale wajen fitar da wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Sabuwar haɗakar ta haɗa da fitattun ’yan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Borno Kotu ta umarci a mayar da Sanata Natasha majalisa Sauran sun haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da sauran shugabannin jam’iyyun adawa. Sun ƙaddamar da sabuwar haɗakarsu a ƙarƙashin jam’iyyar ADC a ranar Laraba. A...
Ƙungiyar Palermo ta ɗauki Filippo Inzaghi a matsayin mai horas da ’yan wasanta bayan raba da gari da ƙungiyar Pisa wadda ya kafa tarihin jagorantar haurowarta gasar Serie A. Cikin wata sanarwa da Palermo ta fitar ta ce Inzaghi ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru da dama wanda zai soma aiki daga watan gobe. Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi Jirgin alhazai ya yi saukar gaggawa kan barazanar harin bom A cewar kafofin watsa labarai na Italiya, Palermo ta biya Pisa kusan dala miliyan 1.1 wajen ɗaukar Inzaghi. Pisa dai ta ƙare gasar Serie B a mataki na biyu a ƙarƙashin jagorancin kociyan mai shekaru 51, lamarin da ya ba ta nasarar haurowa gasar Serie A karon...
Dakarun Operation Haɗin Kai sun kama mut biyar da ake zargin suna taimaka wa ’yan ta’adda da kayan aiki. Daga cikinsu har da wani ɗan ƙasar China da ya ce shi mai harkar ma’adinai ne. Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu — Gwamnatin Tarayya An kama su ne a lokacin kai wani samame da aka gudanar daga 5 zuwa 7 ga watan Yuni a ƙananan hukumomin Kukawa da Ngala na Jihar Borno, da kuma Geidam a Jihar Yobe. A lokacin wannan aiki, dakarun sun ƙwato wasu kayayyaki da suka haɗa da mota, babur, wayoyin salula, fasfo na ƙasar China, da kuma kuɗi Naira 10,000....
Rundunar ’yan sandan ƙasar Australia ta kama wata ’yar asalin Najeriya da ke ƙasar Australia, Binta Abubakar bisa zarginta da safarar ɗalibai daga ƙasar Papua New Guinea tare da tilasta musu yin aikin da ba a biya a gonaki a faɗin jihar Ƙueensland da sunan bayar da tallafin karatu. Binta mai shekara 56, an kama ta ne a ranar Laraba a filin jirgin saman Brisbane a lokacin da ta isa ƙasar Papua New Guinea, inda take zaune. Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8 Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi Kamen nata ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekaru biyu da ƙungiyar masu fataucin bil-Adama ta AFP ta...
Gobara ta tashi a Kwalejin Karatun Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci mallakin fitaccen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ke Rafin Albasa, a Jihar Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayan cikinta. Binciken wakilinmu ya gano cewa gobarar ta lalata bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan kwamfuta, da ɗakunan karatu. Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa An kuma rasa kayan sawa na malamai da ɗalibai, katifu, barguna da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Sai dai daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce sun...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman kayan aikin soja a barikin babban asarar...
Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa. “Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa...
Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na ƙasa karo na 27 kan safarar mutane da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, Babbar Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya ce dole ne Najeriya ta ɗauki mataki ta hanyar zamani daidai yadda matsalar take saurin faɗaɗa. Ministan shari’an ya ce, “Safarar mutane ta koma ta intanet. Dole ne mu gaggauta ɗaukar mataki ko kuma...
Akwai yiwuwar Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa wata dokar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) a wasan gasar La Liga wanda ta doke Osasuna. Rahotanni na cewa ƙungiyar Osasuna za ta shigar da ƙorafi kan wasan da Barcelona ta doke ta da ci 3-0, saboda zargin saɓa dokar FIFA kan amfani da ɗan wasan da bai cancanta ba. Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara A jiya Alhamis ce Barcelona ta karɓi baƙuncin Osasuna a wani kwantan wasa na gasar La Liga, inda to doke baƙin nata da ci 3-0. Wannan nasarar ta bai wa Barcelona damar yin zaman faɗi da tazarar maki 3 a...
Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar. A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar ranar 20 ga watan Maris, 2025, inda gobarar ta laƙume kayayyakin abinci da tufafi da dai sauran kayayyaki. Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa wuƙa ta mutu ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Wanda kawo yanzu ba a tantance adadin asarar da ta haifar ba baya ga salwantar rai guda. Hukumar kashe gobara ta Jihar Borno tare da haɗin...
Wata matashiya mai suna Aleysha Ortiz ’yar shekara 19 da ke Jihar Connecticut a Amurka ta dauki matakin shari’a a kan tsohuwar makarantar sakandaren gwamnatin da ta yi saboda gazawarta ta hanyar ba ta damar kammala karatu “da sakamako mai daraja” duk da ta kasance maras ƙoƙari. A watan Yunin shekarar bara ce, Aleysha Ortiz ta kammala karatu a Makarantar Hartford Public High School da ke Hartford, a Jihar Connecticut, inda aka karama ta, har ma ta samu gurbin karatu a kwaleji, amma yanzu ta kai karar tsohuwar makarantarta saboda sakacinta. Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya EFCC ta kama Murja Kunya kan wulaƙanta takardun Naira Matashiyar mai shekara 19 tana zargin makarantar da ta...
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 s gidan yari. Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas a bara, yana ƙoƙarin shigowa da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kusan kilogram 20, wadda kuɗinta ya kai biliyan 46. Tinubu ya bai wa Farfesa Jega muƙami a gwamnatinsa PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Sauran da aka kama sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (wanda aka fi sani...
Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Hukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya. “Rufewar jami’ar ya biyo...
Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe. Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya. Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu...
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...