Hatsarin mota ya kashe mutane 5 a Yobe
Published: 8th, April 2025 GMT
Aƙalla mutane biya ne suka mutu, 19 suka yi munanan raunuka a dalilin hatsarin mota da ya rutsa da su a Kasuwar Damagum da ke kan babbar hanyar Kano-Maidugri a Jihar Yobe.
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadi.
Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar Gobara ta laƙume ƙauyuka a BornoWani da lamarin ya faru a idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa, gudun wuce sa’a da wani direban bas ke yi ne ya janyo hatsarin, inda ya afka wa mutanen da ke tsaye a bakin titi ana tsaka da cin kasuwar.
“Direban ya ɗauko fasinjoji ne zuwa Damaturu, kuma da alamu Potiskum ya nufa,” in ji shi.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen Jihar Yobe, CC Livinus Longzen Yilzoom, ya tabbatar da mutuwar mutane biyar, yayin da 19 kuma suka samu raunuka.
Daga nan ne kuma ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, da kuma al’ummar Damagum da Jihar Yobe baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin mota
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno
Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno.
Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza.
Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000’Yan ta’addan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ke kan hanyar Marte zuwa Dikwa ta hanyar dasa bama-bamai.
Amma sojoji sun gano abubuwan fashewa guda 17 da suka dasa a ƙarƙashin gadar kuma suka cire su.
A yayin daƙile harin, sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram guda tara, sannan sun ƙwato bindigogi ciki har da AK-47 da bindigar PKT.
Kakakin rundunar sojin a Maiduguri, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya ce dakarun na ci gaba da kai farmaki da sanya ido kan ayyukan ‘yan ta’addan a yankin.
Ya ce wannan nasarar na nuna cewa sojoji sun ƙudiri aniyar hana ’yan Boko Haram da ISWAP aikata ta’addanci.
Rundunar sojin ta roƙi jama’a da su ci gaba da bayar da haɗin kai ta hanyar bayar da rahoton motsin duk wani mutum da suke zargi yana da alaƙa da ’yan ta’adda ga jami’an tsaro.