Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun hakkoki da muradun kasashe mambobin WTO, kuma ya matukar dagula ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da kuma tsarin tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa.

Bugu da kari, hukumar harajin kwastam ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, kasar Sin za ta kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, farawa daga ranar 10 ga watan Afrilun nan da muke ciki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam

Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani

A cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025.

Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu muhimman ayyuka da yake yi.

Waɗannan ayyukan sun haɗa da gyara da inganta harkokin Kwastam, kammala wani shiri da zai sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya, da kuma taimaka wa ƙasar wajen cika alƙawuran da ta ɗauka ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki ta Afirka (AfCFTA).

Shugaba Tinubu, ya yaba da ƙwazon Mista Adeniyi da yadda yake gudanar da ayyukansa.

Ya ce ƙarin wannan wa’adin zai taimaka wajen inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga a hukumar, da kuma tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam
  • Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar Kwastam
  • Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah
  • Za A Bude Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Koli Na 20 Na JKS A Watan Oktoban bana
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China
  • Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki
  • Gwamna Namadi Ya Biya Sama Da Naira Biliyan Daya Ga Tsofaffin Ma’aikata