Pakisatan: An Kubutar Da Mutane 155 Sannan Yan Ta’adda 27 Suka Halaka A Garkuwan Jirgin Fasinja A Jiya Talata
Published: 12th, March 2025 GMT
Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27.
Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa Peshawar.
Manufar garkuwan dai ita ce neman gwamnatin Pakisatn ta bawa yankin Baluchistan na kasar Pakisatan yencin kanta a matsayin kasa mai zaman kanta.
Labarin ya ce yan bindigan sun ta da nakiya ne suka lalata layin dogon, kafin su tilastawa Jirgin tsayawa.
Ya zuwa yanzu dai yan bindigan sun kashe mutane 3 daga cikin har da direban jirgin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
Aƙalla sojoji 13 aka cafke a ƙasar Benin bayan yunƙurin da juyin mulki da suka yi bai yi nasara ba.
Majiyoyin tsaro da na soja sun bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama sojoji ne masu aiki a halin yanzu, sai mutum ɗaya da ya taɓa yin aiki a rundunar amma ya yi ritaya.
Kama su ta biyo bayan sanarwar da aka yi a talabijin na ƙasar da safiyar Lahadi, inda sojojin suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da rushe dukkan cibiyoyin gwamnati.
Jami’an da suka kira kansu Kwamitin Soja na Sake Tsarawa, sun ce sun karɓe mulki, sun rufe iyakokin ƙasar tare da dakatar da jam’iyyun siyasa.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Shugaba Talon yana cikin ƙoshin lafiya, kuma dakarun da suka tsaya kan gaskiya na dawo da doka da oda.
Gwamnati ta bayyana lamarin a matsayin aikin “tsiraru mutane” da ba su da tasiri.
“Wasu ’yan tsiraru ne kawai da ya mamaye talabijin. Rundunar sojan ƙasa na sake karɓar iko. Birnin da ƙasar gaba ɗaya suna cikin tsaro,” in ji sanarwar fadar shugaban ƙasa.