2025-12-08@14:42:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7166

«kafafen sada zumunta na yanar gizo»:

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan kubutar da yan makaranta 100 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka sace a wata makaranta a jihar Naija a cikin watan Nuwamban da ya gabatata. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kubutar da yan...
    Daga Bello Wakili Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, domin wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rantsar da Shugaban Alassane Ouattara a wa’adinsa na hudu. Za a rantsar da Shugaban ne a yau Litinin, 8 ga watan Disamban 2025, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abidjan, wanda...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya. Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan.   Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na...
    Jami’an Rundunar Leƙen Asiri ta musamman a Jihar Kwara sun cafke wani tsohon ɗan gidan yari mai suna Godday Agaadi da bindiga ƙirar AK-47. An kama Emmanuel Okah ne bayan an same shi da bindigar AK-47 da harsashi guda 25 a jikinsa, a lokacin da yake sanye da kayan ’yan sanda. Dubunsa ta cika ne...
    Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi wa kasar Najeriya alkawalin taimaka ma ta domin ta fuskanci matsalolin tsaro, musamman ma dai ta’addanci a arewacin kasar. Shugaban kasar Faransan ya ce, takwaransa na Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci taimako domin fuskantar matsalar tsaro a arewacin kasar. Macron ya rubuta a shafinsa na X cewa;...
    Fitacce mai shirya fina-finai dan kasar Iran Majid Majidi ya sami kyauta ta musamman a wurin bikin fina-finai na Eurasia, saboda gagarumar rawar da yake takawa a fagen shiryafina-finai da su ka shahada a duniya. A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka bude bikin a birnin Moscow wanda ya sami halartar ministan al’adu...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan wasu sojoji sun bayyana hamɓarar da Gwamnatin Shugaba Patrice Talon. Gungun sojojin, sun bayyana cewa ta rushe gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki, da rufe iyakokin ƙasar. An gano gawar malamin Islamiyya da...
    An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja. Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata. ’Yan bindiga sun...
    Rahotanni daga Jamhuriyar Benin na cewa am kama wasu 12 bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da jijjibin safiyar Lahadin nan. Tun da farko dama fadar shugaban kasar ta ce har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin. Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin ya bayyana a gidan talabijin din...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa har yanzu Amurka ba ta nuna sha’awarta ta shiga “tattaunawa mai ma’ana ba,” yana mai sake nanata cewa dole ne Washington ta fara amincewa da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya na zaman lafiya a karkashin Yarjejeniyar hana yaduwar Makaman Nukiliya ta (NPT). A...
    Kasar Masar ta sake jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da hanyar shiga iyakar Rafah don korar Falasdinawa daga gidajensu ba, tana mai jaddada bukatar sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza. Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya yi da Al...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5...
    Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a...
    Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a...
    Wani jirgin Sojin saman Najeriya ya yi haɗari jim kaɗan bayan tashi daga sansanin Sojin ƙasar da ke Kainji a jihar Neja, sakamakon tangarɗar inji. Kakakin rundunar sojin saman na Najeriya Ehimen Ejodame lokacin da yake tabbatar da faruwar haɗarin ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar wannan haɗari, sai dai...
    Gwamnatin kasar Rwanda ta rattaba hannu a kan yarjeniya na dalar Amurka miliyon $228 a karkashin sabon tsarin taimako na gwamnatin kasar Amurka. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa tallafin zai taimakawa kasar Rwanda ta kyautata harkokin kiwon lafiya a kasar ta Rwanda a yayinda tallafin kudaden zai ci gaba a...
    Kungiyar ‘yan wasan  ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda...
    Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026. Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin...
    Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja. Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa. Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Majiyoyi sun ce...
    Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja. Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa. Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Majiyoyi sun ce...
    Sabon bashin, ya nuna yadda Bankin ya bai wa kasar bashin da ya kai jimlar dala biliyan 5.1 tun daga ranar 31 na watan Okutobar 2025. Kazalika, wannan sabon bashin, zai taimaka wa kashi na biyu na shirin habaka tattalin arziki a bangaren samar da makamashi da  sauye-sauye, a fannin makamashin da cimma burin da...
    Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya. Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a. Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Ranar Sabuwar...
    Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar. Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar...
    Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa  dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada...
    Wasu mutane uku sun rasu yayin da suke tsaka da aikin yasar rijiya a garin Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano.  A yayin da suke aikin haƙar rijiya, ɗaya daga cikinsu ya shiga domin yasowa biyu kuma na janyo ƙasar da aka haƙo. Ana cikin haka igiyar ta tsinke, inda nan take...
    Yanzu ƴan Najeriya za su iya cire naira 100,000 ta na’urar cire kuɗi ta ATM a rana, haka ma abin yake a ɓangaren cire kuɗi ta na’urar POS. A ɓangaren ma’aikatu kuma, za su iya cire kuɗi har naira miliyan biyar ne a duk mako. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabbin tsare-tsaren da Babban...
    Majiyar ma’aikatar tsaron kasar Rahsa ta bada sanarwan cewa garkuwan sararin samaniyar kasar ta kakkabo jiragen Drones na yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na kasar Ukrai har guda 116 a daren jiya kadai. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon tanakalto majiyar ma’aikatar tsaron na cewa, rasha ta kakkabo jiragen  116 ne a yankuna...
    Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya shigar da Sanata Natasha Akpoti ƙara a kotu kan zargin ɓata masa suna yana mai neman ta biya shi diyyar naira biliyan 200. Sanata Natasha mai wakiltar jihar Kogi ta tabbatar da karɓar sammacin a shafukanta na sada zumunta, inda ta nuna jin daɗinta tana mai cewa ta...
    Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin...
    Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa. Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da...
    Amurka ta faɗaɗa yawan ƙasashen da ta sanyawa haramcin samun bizar shiga ƙasar zuwa 32 ƙarƙashin jagorancin Donald Trump da ke tsaurara matakan shiga wannan ƙasa ta yammacin duniya saboda abin da ya kira barazanar ƙasashen ga tsaron Washington da kuma kange kwararar ƴan cirani. Sakatariyar tsaron cikin gida ta Amurka Kristi Noem yayin wasu...
    Pars Today – Hanieh Rostamian, jarumar harbin bindiga ta Iran, za ta fafata a wasan karshe na gasar cin kofin duniya. Za a fara gasar cin kofin duniya ta 2025 gobe, Asabar, a Qatar. A cewar Pars Today, tunda manyan ‘yan wasan harbi na duniya suna shiga wannan gasar, Hanieh Rostamian—wanda a halin yanzu yana...
    Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka...
    Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a...
    Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi, ya yi zargin cewa ƙasashen waje na taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda Najeriya. Sheikh Ahmad Gumi ya danganta ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya a baya-bayan nan da irin maganganun da ƙasashen waje suka riƙa yi a kai. A yayin wata hira da BBC Hausa, malamin ya bayyana...
    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026. Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026. Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike DSS ta...
    Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP. Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC. Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a...
    Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara. An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta  bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare...
    Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya...
    Pars Today – Vladimir Putin ya yi tafiya zuwa Indiya don ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu. Vladimir Putin, shugaban Rasha, ya isa New Delhi a ranar Alhamis, 4 ga Disamba, a ziyararsa ta farko zuwa Indiya tun bayan fara yakin Ukraine a 2022. Ziyarar ta kwanaki biyu na da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin tsaro da...
    Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya...
    Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka...
    Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda...
    Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wasu kudurori guda biyu da ke kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan na Siriya. Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Falasdinu ne suka gabatar da daftarin kuduri game da Falasdinu. Kasashe 151 ne suka kada kuri’a a kan hakan, yayin...
    Dan wasan taekwando na kasar iran  Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya  da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35, Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center...
    Jirgin Fadar Shugaban Kasa da Gwamnatin Najeriya ta saka a kasuwa da nufin sayarwa ya kasa samun mai saye kusan watanni biyar bayan ɗora shi a dandalin sayar da jiragen sama na duniya. A sakamakon haka, tuni ma kamfanin dillancin da ke kula da sayar da jirgin samfurin Boeing 737-700 Business Jet ya janye jerin...