2025-12-08@16:58:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12277

«Farida»:

    Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya bayyana cewa makamai masu linzamu na dakarun sun fada kan matatar man fetur na Haifa a HKI har sau biyu a yakin kwanaki 12 da ta fafata da Iran a cikin watan Yunin wannan shekara. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan kubutar da yan makaranta 100 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka sace a wata makaranta a jihar Naija a cikin watan Nuwamban da ya gabatata. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kubutar da yan...
    Firai ministan kasar Iraki Mohammad Shia Assudani ya bayyana cewa gwamnatinsa bata tushe asusun kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon da kuma Ansarallah ta kasar Yemewn ba. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran IP ya nakalto sudanina cewa gwamnatinsa tana kokarin hana tasowar wani riki a yankin sannan da kuma kaucewa duk wani rikicin siyasa...
    Daga Bello Wakili Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, domin wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rantsar da Shugaban Alassane Ouattara a wa’adinsa na hudu. Za a rantsar da Shugaban ne a yau Litinin, 8 ga watan Disamban 2025, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abidjan, wanda...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya. Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan.   Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na...
    Jami’an Rundunar Leƙen Asiri ta musamman a Jihar Kwara sun cafke wani tsohon ɗan gidan yari mai suna Godday Agaadi da bindiga ƙirar AK-47. An kama Emmanuel Okah ne bayan an same shi da bindigar AK-47 da harsashi guda 25 a jikinsa, a lokacin da yake sanye da kayan ’yan sanda. Dubunsa ta cika ne...
    Sojojin kasar Thailand sun sanar a yau Litinin cewa, son kai wani sabon hari akan iyakar da take da sabani da makawabciyarta Cambodia. Wannan sanarwar ta sojojin Thailand ya biyo bayan da kasashen biyu suka rika zargin juna da cewa sun keta dakatar da wutar yaki, da shugaban Amurka Donald Trump ya shiga tsakani. Sojojin...
    Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baghaie ya yi tir da kashe fararen hula a garin Kalogi dake Jahar Kurdufan na Sudan. Bugu da kari kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kawo karshen abinda yake faruwa a wannan kasar. Kusan mutane...
    Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi wa kasar Najeriya alkawalin taimaka ma ta domin ta fuskanci matsalolin tsaro, musamman ma dai ta’addanci a arewacin kasar. Shugaban kasar Faransan ya ce, takwaransa na Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci taimako domin fuskantar matsalar tsaro a arewacin kasar. Macron ya rubuta a shafinsa na X cewa;...
    Mai Magana da yawun fadar mulkin Rasha Dmitry Viskov ya ce; Fadar mulkin kasar tana maraba da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na bitar siyasar tsaron kasar, da ta kunshi cire kasar Rasha a matsayin barazanar da Amurkan take fuskanta. Viskov ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tass” cewa; a cikin sabon tsarin...
    Fitacce mai shirya fina-finai dan kasar Iran Majid Majidi ya sami kyauta ta musamman a wurin bikin fina-finai na Eurasia, saboda gagarumar rawar da yake takawa a fagen shiryafina-finai da su ka shahada a duniya. A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka bude bikin a birnin Moscow wanda ya sami halartar ministan al’adu...
    Masana harkokin siyasa, jakadu da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana cewa rashin shugabanci nagari da son mulki na dogon lokaci su ne manyan dalilan da ke haddasa yawaitar juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma. Wannan na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, wanda ya jefa...
    Aƙalla sojoji 13 aka cafke a ƙasar Benin bayan yunƙurin da juyin mulki da suka yi bai yi nasara ba. Majiyoyin tsaro da na soja sun bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama sojoji ne masu aiki a halin yanzu, sai mutum ɗaya da ya taɓa yin aiki a rundunar amma ya yi ritaya. Kama su...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan wasu sojoji sun bayyana hamɓarar da Gwamnatin Shugaba Patrice Talon. Gungun sojojin, sun bayyana cewa ta rushe gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki, da rufe iyakokin ƙasar. An gano gawar malamin Islamiyya da...
    An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja. Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata. ’Yan bindiga sun...
    Rahotanni daga Jamhuriyar Benin na cewa am kama wasu 12 bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da jijjibin safiyar Lahadin nan. Tun da farko dama fadar shugaban kasar ta ce har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin. Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin ya bayyana a gidan talabijin din...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa har yanzu Amurka ba ta nuna sha’awarta ta shiga “tattaunawa mai ma’ana ba,” yana mai sake nanata cewa dole ne Washington ta fara amincewa da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya na zaman lafiya a karkashin Yarjejeniyar hana yaduwar Makaman Nukiliya ta (NPT). A...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa Hamas ta bayyana cewa za ta mika makamanta ne kawai ” idan Isra’ila ta kawo karshen mamaya, tana mai jaddada cewa ba za a iya kwance damarar makamai ba a cikin yanayin da ake ciki na zaluncin soja da siyasa. Babban jami’i a ofishin siyasa na Hamas kuma babban mai shiga tsakani...
    Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana sabbin dabarun tsaron Amurka na cimma maradun gwamnatin Isra’ila ne. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce sabbin dabarun tsaron Kasa na Amurka (NSS) da ke bayyana ka’idojin Washington da muhimman manufofin harkokin waje a zahiri cimma maradun tsaro ne ga gwamnatin Isra’ila ne. Esmaeil Baghaei ya yi wannan...
    Kasar Masar ta sake jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da hanyar shiga iyakar Rafah don korar Falasdinawa daga gidajensu ba, tana mai jaddada bukatar sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza. Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya yi wannan furucin ne a wata hira da ya yi da Al...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5...
    Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a...
    Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a...
    Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta bayyana cewa ta dakile wani yunkurin juyin mulki, bayan da wasu sojojin ƙasar suka sanar da cewa sun hambarar da shugaba Patrice Talon a gidan talabijin na kasar. Talon, mai shekaru 67, tsohon dan kasuwa ne wanda aka yiwa lakabi da “Sarkin Auduga na Cotonou”, zai mika mulki a watan Afrilun...
    Wani jirgin Sojin saman Najeriya ya yi haɗari jim kaɗan bayan tashi daga sansanin Sojin ƙasar da ke Kainji a jihar Neja, sakamakon tangarɗar inji. Kakakin rundunar sojin saman na Najeriya Ehimen Ejodame lokacin da yake tabbatar da faruwar haɗarin ya ce babu ko mutum guda da ya rasa ransa sanadiyyar wannan haɗari, sai dai...
    Gwamnatin kasar Rwanda ta rattaba hannu a kan yarjeniya na dalar Amurka miliyon $228 a karkashin sabon tsarin taimako na gwamnatin kasar Amurka. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa tallafin zai taimakawa kasar Rwanda ta kyautata harkokin kiwon lafiya a kasar ta Rwanda a yayinda tallafin kudaden zai ci gaba a...
    Tom Barrack jakadan Amurka na musamman a kasar Siriya ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi kokarinkifar da gwamnatin JMI a baya har sau biyu amma ta kasa yin haka. Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Barrack yana fadawa wani kamfanin dillancin labaran UAE a ranar jumma’an da ta gabata, ya...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya yi tir da kungiyar kasashen larabawa na yankin tekun Farisa, wadanda suka fidda bayanin bayan taronsu a baya bayan nan suka allawadai da kuma nuna goyon bayansu ga kasar UAE kan mallakar tsibiran Tumb babba da tumb karami da Abu Musa. Kamfanin dillancin labaran IP na...
    Kungiyar Hamas wace take iko da yankin gaza ta bada sanarwan cewa, zata mika makamanta ne kawai ga gwamnatin Falasdinawa wacce take da cikekken iko a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, idan yahudawan sun kawo karshen mamayar da sukewa kasar. Shafin labarai na yanar Gizo ArabNews ya nakalto shugaban kungiyar Khalilul Hauua yana fadar...
    Sojoji a kasar Jamhuriyar Benin sun kifar da gwamnati a wani juyin mulki da suka sanar a ranar Lahadi. Sojojin sun bayyana ne a gidan talabijin na kasar inda suka sanar da tsige Shugaban Kasa Patrice Talon da kuma rushe duk hukumomin kasar. Dakarun, karkashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigiri, sun rufe iyakokin kasar da...
    Ministan harkokin cikin gidan kasar Venezuela ya bayyana cewa al’ummar Venezuela ba ta tsoron barazanar da Amurka take yi ma ta, domin juyin juya halin kasar zai ci gaba, kuma azamar al’umma ce za ta yi nasara a gaban masu wuce gona da iri. Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Venezuela Diosdado Cabello Rondón wanda...
    Kungiyar ‘yan wasan  ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda...
    Rahotanni da suke fitowa daga birnin Pretoria sun ce, adadin mutanen da su ka kwanta dama sanadiyyar bude wuta ta kan mai uwa da wabi, sun kai 11 daga cikinsu har da karamin yaro dan shekaru uku. Jami’an ‘yan sandan kasar ta Afirka Ta Kudu ne su ka sanar da cewa an bude wutar ne...
    Rahotannin da suke fitowa daga  DRC sun ce fadan ya barke ne dai bayan kwanaki kadan da gwamatin DRC da ta Rwanda su ka amince da tabbatar da zaman lafiya. A can gabashin kasar an ga dubban mutane maza, mata, da kananan yara suka dauke da kayayyakinsu a lokacin da suke ficewa daga kauyukna da...
    Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026. Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin...
    Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaron kasashen pakistan da Afghanistan sun yi musayar wuta mai tsananin a iyakokin kasashensu, kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 5,  hakan na nuna irin rikicin dake tsakanin kasashen masu makwabtataka da juna, bayan sun cimma yarjejeniyar sulhu a kasar saudiya amma da alama babu ci gaban da aka samu. A...
    Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja. Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa. Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Majiyoyi sun ce...
    A wata tattaunawa ta wayar tarho da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da takwaransa na kasar masar Badr Abdelatty sun bayyana cewa isra’ila na ci gaba da kai hare-hare da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza da kuma kasar labanon, Ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude...
    Rahotanni na nuna cewar wani jirgin yaƙi na rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ya yi hatsari a Jihar Neja. Jirgin ya faɗi a sansanin NAF da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa. Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Majiyoyi sun ce...
    Fira ministan kasar Qatar shaikh mohammad bin Abdurrahaman al thani yayi gargadi game da ci gaba da kai hare-hare da kame falasdinawa da HKi ke yi a yankin gaza, ya jaddada cewa shirin da shugaban Amurka ya bullo da shi na zaman lafiya zai zama gaskiya ne idan isra’ila ta janye dukkan sojojinta a yankunan...
    Sabon bashin, ya nuna yadda Bankin ya bai wa kasar bashin da ya kai jimlar dala biliyan 5.1 tun daga ranar 31 na watan Okutobar 2025. Kazalika, wannan sabon bashin, zai taimaka wa kashi na biyu na shirin habaka tattalin arziki a bangaren samar da makamashi da  sauye-sauye, a fannin makamashin da cimma burin da...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin kare hakkin bil adama na yankin falasdinu sun yi gargadi game da makircin da isra’ila ke kullawa na kashe  Marwan bargusu daya daga cikin  shuwagabanin falasdinawa a inda take tsare da shi a gidan yari,  samakamon gana masa azaba da aka yi . Babban darektan kungiyar pps Amad Najjar yayi...
    Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya. Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a. Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Ranar Sabuwar...
    Hukumar Kwastam, ta kama kilo 25.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa na ƙasar Brazil mai suna MV San Anthonio a tashar jirgin ruwa ta Legas. An ɓoye hodar cikin ƙananan jakunkuna biyar. ’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista...
    Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar. Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar...
    An harbe wani jami’in ɗan sanda har lahira, yayin da yake tsaka da binciken ababen hawa a Benin a Jihar Edo. Kakakin rundunar, CSP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, lokacin da jami’an rundunar suka tsayar da wata baƙar mota ƙirar Lexus, amma ta ƙi tsayawa. ’Yan...
    Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa  dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada...
    ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su, masu shekaru hudu da biyar, a Jihar Borno. An ceto yaran ne a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai a Ƙaramar Hukumar Jere, inda masu garkuwar suka je karbar kuɗin fansa. Sanarwa da ASP Nahum Kenneth Daso, kakakin rundunar ya fitar...