2025-09-17@23:11:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1786

«kungiyar asiri»:

    Mayakan ‘Yan ta’adda na  kungiyarAl-Qaeda sun karbe ikon garin Farabougou da ke tsakiyar kasar Mali, mako guda bayan da suka kwace sansanin sojojin da ke garin, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa. Kungiyar ‘yan ta’adda ta (JNIM) ta sanar a wasu jerin sakonni da ta fitar cewa,  ta kwace garin tare da kafa abin da...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa mutun daya dan kasa yayi shahada a yau Jumma’a saboda makami masu linzami wadanda jiragen yakin HKI suka cilla a kan motarsa a kauyen Sair cikin lardin Nabadiyya. Tashar talabijin ta Al-mayaddeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, sojojin yahudawan sun jefa boma-bomai har guda...
    Ajayi-Kadri ya ce kungiyar ta yi cikakken nazari kan sake gabatar da harajin na FOB wanda ta tabbatar zai kara dagula lamura ne kawai da sake jefa masana’antu cikin mawuyacin hali.   “Gaskiyar lamarin ita ce, farashin kashi hudu cikin 100 na kamfanonin ya yi yawa fiye da yadda aka samu karin kashi bakwai cikin...
    “Ban ga dalilin da ya sa ba a raba fifikon fasaha na Brazil da Afirka ba. Mun tabbatar wa junanmu cewa mune kawai za mu iya bunkasa tattalin arzikinmu don taimakawa kasarmu,” Tinubu ya shaida. Tinubu ya kuma bai wa masu zuba hannun jari tabbacin cewa manufofin farfado da tattalin arzikin Nijeriya na haifar da...
    Kasar Sin ta gabatar da ‘yancin samun ci gaba a matsayin hakkin dan Adam mafi muhimmanci. Ta hanyar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), ta zuba jari mai yawa a fannin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da fasahohi a fadin nahiyar Afirka. Ayyuka irin su hanyar dogo na Addis Ababa...
    Sanata Kabiru Garba Marafa tsohon ɗan Majalisar Dattawa da ya wakilci yankin Zamfara ta tsakiya jigo a Jam’iyar APC a jihar ya fice daga jam’iyar. Sanata Marafa ya bayyana ficewarsa a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook a ranar Jumu’a ya ce bayan tattaunawa da magoya bayansa sun cimma matsayar barin Jam’iyyar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Jibrin Ado bisa laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita a unguwar Gerawa da ke jihar. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne a ranar Alhamis daga wata sanarwa ta manhajar X ta wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama. Ambaliya ta raba...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto.   Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU:...
    A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika...
    An kafa ta a cikin 1955 kuma tana da hedikwata a Tokyo, IAPH kungiya ce ta duniya mai dauke da tashoshin jiragen ruwa fiye da 190, kuma tana gudanar da kasuwanci a cikin ƙasashe 89.   Mambobin kungiyar IAPH suna kula da sama da kashi 60 cikin 100 na cinikin teku da kwantena na duniya....
    Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani ta kimanin dala biliyan 2.5. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. Sanusi Mikail Sami ya zama...
    Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani na kimanin dala biliyan 2.5. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. Sanusi Mikail Sami ya zama...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban gamayyar masu goyon bayan Gwagwarmaya a kasar Lebanon suna tare da kungiyar sannan wadanda suke nanata cewa sai an takaita makamai a hannun gwamnati sun aiki ne wa HKI da Amurka . Tashar talabijan ta Al-Manar ta kungiyar ta nakalto shugaban gamayyar Mohammad Ra’ad yana fadar haka ya kuma kara da cewa abinda ya...
    Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba. Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya...
      Dakta Abdullahi Idris, ya bukaci sabbin shugabannin da zage damtse wajen ganin an samu nasarar abinda suka sanya a gaba wajen samar da zaman lafiya da hadin kan ‘yan Arewa. Akan hakan, ya bukace su da su zama jakadu na gari a jihohinsu wajen kare martabar kungiyar da kuma lalubo hanyar da za’a kara...
    Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya (ACF) ta bayyana matuƙar damuwarta kan rushe kasuwar Alaba Rago mai ɗimbin tarihi a Legas, inda ta bayyana hakan a matsayin babban koma baya ga dubban ’yan kasuwa. A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, Ƙungiyar ta bayyana cewa duk da...
    Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna  ya sanar da cewa: An sake dawo da ayyukan IAEA a cibiyar Bushehr Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikhail Ulyanov, ya sanar da dawo da ayyukan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a...
    Tawagar Sudan karkashin jagorancin babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa (NISS) Manjo Janar Ahmed Mufadal ta isa Mogadishu babban birnin kasar Somalia a wata ziyarar aiki da ta kai kasar, inda ta gana da shugaban kasar  Hassan Sheikh Mohamud a fadar shugaban kasa dake Mogadishu. Jagoran tawagar ta Sudan Mufadal Sheikh Mohamud ya aike...
    Masu zanga zanga za wasu yankunan kudancin kasar Lebanon sun tilastawa jakada na musamman na gwamnatin Amurka a kasar Siriya da Lebanon Tom Barrack ya fasa ziyarar da yake son kaiwa wasu yankuna a kudancin kasar Lebanon. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya bayyana cewa mutane a garin Sur sun yi gangami a...
    Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin hanzarta aiwatar da ci gaban Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar kere-kere da tattalin abinci don samun nasarori irin na sauran ƙasashe masu tasowa kamar Brazil. A yayin da yake jawabi a ranar Talata a lokacin da ya gana da wasu ‘yan Nijeriya mazauna kasar Brazil, shugaba Tinubu ya...
    Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ba za ta duba wuraren da aka lalata na cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran ba a hare-haren Amurka Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, a halin yanzu hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ba za ta binciki cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran...
    Ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya bayyana jin dadinsa ga hadin kai da goyon bayan Iran ga kasarsa A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Iran, ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya yabawa irin hadin kai da goyon bayan Iran ga ‘yancin kai, yana mai jaddada aniyar Iran na kare ta daga...
    Rasha ta ba da shawarar tsawaita kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran Mataimakin wakilin dindindin na kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Dmitry Polyansky ya sanar da cewa, Rasha ta gabatar da shawarwarin a Majalisar Dinkin Duniya na tsawaita sahihancin kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan yarjejeniyar...
    Maharan da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a ranar Talata sun sace mata da miji tare da ’yarsu mai shekara ɗaya a cikin birnin Katsina. An dai kai harin ne a gidan ma’uratan, Anas Ahmadu, da matarsa Halimatu, da kuma ’yarsu Jiddah a Unguwar Kanada a yankin Ƙofar Ƙaura a Katsina. DAGA LARABA: Abin...
    A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka gana da Sarkin Cambodia Norodom Sihamoni, da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk a birnin Beijing.   Xi ya yi kyakkyawar maraba da zuwan Sarki Norodom Sihamoni da mahaifiyarsa Sarauniya Norodom Monineath Sihanouk kasar Sin, kana ya yi lale maraba da halartar...
    An yi kiciɓus da gawar wata budurwa mai shekaru 14 a cikin gidansu da ke unguwar Dandinshe a Ƙaramar Hukumar Dala da ke Jihar Kano. Lamarin dai ya ɗugunzuma mazauna unguwar yayin da Aminiya ta riski iyaye, ’yan uwa da kuma maƙwabta cikin alhini a yayin ziyarar da ta kai har gida. Hisbah ta haramta...
    Har yanzu babu tabbaci ko zai iya buga wasan. Arsenal na fatan cewa Saka da Odegaard ba za su daɗe suna jinya ba. A kakar da ta wuce, Saka ya sha fama da rauni har ya yi watanni uku ba ya wasa. Sai dai a bana Arsenal ta ƙara wasu sababbin ‘yan wassan gaba kamar...
    Za’a gudanar da wani taro tsakanin Iran da kasashen Turai E3 ko Troiko a kasar Switziland a gobe Talata 26 ga watan Augusta da muke ciki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa  tattaunawar Iran tare da kasashen Jamus, Burtaniya da Faransa zata kasance na kan shirin Nukliyar kasar Iran da kuma...
    Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na...
    Kwamandan sojojin Iran ya yi barazanar mayar da martani mai muni da zai haifar da nadama ga makiya Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran da jarumtarsu suna tsayawa da dukkan karfinsu wajen fuskantar barazanar makiya. A yayin ziyarar da ya kai Jami’ar Kimiyyar Sojin Ruwa ta...
    Dakarun Kai Daukin Gaggawa sun kai hari kan ƙungiyar ba da agaji ta Red Crescent a Kordofan da jirgin sama maras matuki ciki Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) sun kai hari kan tawagar kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Sudan (SRCS) a yankin Andaraba na jihar Kordofan ta Arewa,...
    A nasa ɓangaren, Farfesa Usman Yusuf Bugaje ya gargadi gwamnati cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar za ta iya bazuwa zuwa manyan birane a jihar. A ƙoƙarin gwamnati, rundunar sojin Nijeriya ta sanar da shirin kafa sabuwar bataliya a ƙaramar hukumar Malumfashi domin ƙarfafa yaƙi da tashe-tashen hankulan ƴan bindiga a jihar...
    A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II.   Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya...
    Matasa da dama a garin Kafanchan, da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sun yi aikin gayya domin gyara hanyar garin. Sun yi amfani da gatari, fatanya, diga da sauran kayan aiki wajen yi wa hanyar gyara. Ɗaliba ta haɗu da ajalinta a hatsarin mota a Yobe Japan za ta bai wa Najeriya rancen...
    Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata haɗala a Cibiyar Fasahar Sufuri ta Kasa (NITT) da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Kano. Mataimakin Kwamandan Hukumar, Mujahid Aminudeen, ya ce mutane — maza 27 da mata 35, “A ranar Lahadi, jami’anmu tare da haɗin gwiwar NDLEA suka su su 62 a cibiyar...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian na gudanar da ziyarar aiki a kasar Armeniya domin sanya hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyin da suka dace da moriyar kasashen biyu, da kuma tattauna muhimman batutuwa dangane da kasantuwar Amurka a yankin. Yayin da yake jagorantar wata babbar tawaga, Pezeshkian ya isa Yerevan a ranar litinin a matakin farko...
    Kungiyar M23 da ke dauke da makamai a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, ta yi watsi da tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin kasar, tana mai cewa ba za ta koma tattaunawa ba, sai dai idan hukumomi sun cika sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya. Rikicin da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da...
    Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ta rasu. Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Filato, Shittu Bamaiyi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Lahadi. Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood...
    Mama Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ta rasu. Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Filato, Shittu Bamaiyi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos ranar Lahadi. Jirgin ruwa ya nutse da mutum 30 a Sakkwato Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya aika da jajensa ga mutane da Firai ministan kasar Pakisatan kan ambaliyar ruwa da ta faru a kasar bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 300 da kuma bacewar wasu. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban y...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk. Ya kara...
    Jami’an tsaro sun kama manyan shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru, ciki har da shugaban ƙungiyar, Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Baraa. An daɗe ana zarginsa da kitsa hare-hare masu yawa a Najeriya. ’Yan sanda sun kama matashin da ya yi garkuwa da kansa a Ondo Majalisar dokokin Gombe ta fara...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci. Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da...
    Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta mayar da martani da cewa: Shigar da ƙungiyar cikin jerin “baƙin littafi’ na Majalisar Dinkin Duniya ba shi da inganci Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana rashin amincewarta da kakkausar suka ga rahoton da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya fitar kan cin zarafin mata da ke...
    Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a cikin al-amuran sharia da kuma na harkokin kasashen waje, yana tir da da allawadai da mataimakiyar shugaban hukumar ICJ mai hukunta manya-manyan laifuka ta duniya, Julia Sebutinde wacce ta bayyana a fili tana goyon bayan HKI a yakinn Gaza....
    An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka bayyana taron a matsayin mai matukar amfani. Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi, yayin da manzon musamman na Rasha Kirill Dmitriev ya bayyana cewa yanayin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari, yace ziyarar kwamatin a kananan hukumomin jihar 27 tana bada damar ganawa kai tsaye a tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa dabi’ar aiki tare da juna da kuma kyautata alaka a tsakanin bangarori daban daban. Ya yi wannan tsokaci ne lokacin da...