2025-08-01@20:55:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 157

«Makiyayi»:

    Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wani saurayi da budurwarsa bisa zargin yin aure a wajen wani taro ba tare da amincewar iyayensu ba. A cewar Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, matasan sun yi auren ne a wajen shaƙatawa bayan wani da ba su da alaƙa da shi ya biya sadakin...
    Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 537 tare da kama wasu mutum 46 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024. Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Yobe, Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana hakan...
    “Ƙungiyar Al-Hilal ta gode wa Neymar bisa gudunmuwar da ya bayar, kuma tana masa fatan alheri a nan gaba,” in ji ƙungiyar. Wannan matakin ya zo ne yayin da ya rage wata bakwai kafin ƙarshen kwantaragin Neymar, wanda ya kai shekara biyu da ƙungiyar. A Al-Hilal, ana biyan Neymar Yuro miliyan 150 a shekara. Lokacin...
    Wata nakiya ta fashe a Sabon-Pegi da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata da kuma jikkata wasu mutum shida. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na safe....
    An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 18 sakamakon hatsarin wata tankar mai da ta yi bindiga a Jihar Enugu. Alƙaluman da mahukunta suka fitar ya nuna cewa hatsarin ya rutsa da mutum 31 ciki har da mutum 10 da suka samu raunuka daban-daban yayin da aka ceto wasu uku da suka tsallake rijiya da baya...