2025-11-03@13:03:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 174
«haɗin gwiwa»:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Ta ce cikin ƙasa da shekara biyu, Kaduna ta fito daga durƙushewar tsari zuwa zama jihar da ake ganin tsari. Haka kuma, gwamnatin ta yi zargin cewa El-Rufai ya ƙara ƙoƙarin tayar da rikici bayan abokan siyarsarsa sun sha kaye a zaɓen cike gurbi na ranar 16 ga watan Agusta. Ta ce sakamakon ya nuna...
Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace. El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin...
Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini. Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai...
Dakta Abdullahi Idris, ya bukaci sabbin shugabannin da zage damtse wajen ganin an samu nasarar abinda suka sanya a gaba wajen samar da zaman lafiya da hadin kan ‘yan Arewa. Akan hakan, ya bukace su da su zama jakadu na gari a jihohinsu wajen kare martabar kungiyar da kuma lalubo hanyar da za’a kara...
Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar. Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza...
Bayan samum rahotom faruwar lamarin, jami’an tsaro suka bazu cikin dazuka domin ceto waɗanda suka sace. Kwamishinan ’yansandan jihar, Monday Agbonika, ya jagoranci aikin a kan titin Benin zuwa Akure. Ya ce sun yi amfani da sabbin fasahohi ciki har da jirage marasa matuƙa, wanda ya taimaka wajen samun nasara. Agbonika ya yaba wa jami’an...
“Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi. Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali. “Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi. Shugaban ASUU ya...
Wani mutum ya ba da kyautar motarsa da ita kadai gare shi ga wani mai jan baki (alaramma) saboda ƙwarewarsa a haddar Al-kur’ani. Malam Yusuf Ɗan-Birni, ya kyautar da motar ce a taron wa’azin wata-wata da Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta shirya a garin Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya....
“Kuma za a yi hakan ne saboda a matsayinmu na al’umma, muna ci gaba da ƙoƙarin canza abubuwan da ‘yan siyasa ba sa son canzawa,” in ji shi. Ya kuma bayyana cewa ba yau aka fara aikin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar kan batun cin gashin kan ƙananan hukumomi ba. Ejah ya ƙara da cewa...
Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi maƙarrabansa cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin da aka ɗora masa, ya yi murabus. Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya yi biyo bayan belin wani da ake zargin dilan miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Danwawu. Manoma sun koka kan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da tsawa na kwaki uku a faɗin ƙasar daga ranar Litinin. NiMet ta fitar da wannan hasashen ne ranar Lahadi a Abuja, lamarin da ke ƙara barazanar ambaliya a wasu jihohin ƙasar. Shirin kashe N712bn kan...
Gwamnan ya bukaci kamfanin da ke aikin da ya bi ka’idoji da tsarin tsaro, tare da roƙon al’ummomin da abin ya shafa da su ba da haɗin kai ga masu aikin da kuma kare rayuka da kayan aiki. “Wannan aiki wani ɓangare ne na kudirin Gwamnatin Jihar wajen samar da ci gaban ababen more...
A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki. Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP). Ya ce: “Kwarewa...
Gargaɗin ya yi daidai da irin wannan sanarwar da ofisoshin jakadancin Amurka a Jamaica da Uganda suka fitar kwanan nan, a wani ɓangare na yaƙi da dabi’ar karya ƙa’ida shige da fice. A cikin watan Janairun 2025, hukumomin Amurka sun sake jaddada aniyarsu na ƙarfafa ikon kula da iyakoki kan yin amfani da damar zama...
Bugu da ƙari, Hukumar ta NPA ta bayyana cewa, tana kan ƙoƙarin inganta kayan aiki Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar, wanda ta zuba dala biliyan daya, domin fara gyaran Tashoshin Jiragen Ruwa ta Tin Can Island tare da yin ayyukan kwakwarima, a Tashoshin Jiragen Ruwa na, Apapa, Riɓers, Onne, Warri da kuma Kalaba. Ita kuwa a...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta...
A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai. A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam...
A cewar ministan: “Aikin haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin Ma’aikatun Noma, Muhalli, Albarkatun Ruwa, Bunƙasa Kiwon Dabbobi da kuma Tattalin Arzikin Ruwa yana da matuƙar muhimmanci domin cika manufofin Ajandar Sabunta Fata.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa tun daga shekarar nan ta 2025 har zuwa 2026. IMF ya bayyana sabon hasashen a watan Yulin da muke ciki wanda a ciki ya yi ƙiyasin samun ƙarin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya. Manyan makarantu 2 ne...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau. Sakataren Gwamnatin Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar a Talatar nan. Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China ’Yan bindiga...
Babban sufeton ƴansanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya sake tabbatar da ƙoƙarin rundunar wajen tabbatar da cikakken tsaro a faɗin ƙasar nan ta hanyar samun bayanan sirri daga jami’ansu. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan ya ce rundunar ta duƙufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan, sannan ya buƙaci al’umma da...
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Jihar Jigawa (ALGON) ta yi alkawarin kafa kyakkyawar haɗin gwiwa da ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar, domin inganta ƙwarewar jami’an hulɗa da jama’a a fadin jihar. Shugaban ALGON, Farfesa Abdurrahman Salim ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi shugabannin NUJ a wata ziyarar girmamawa da suka...
Sanata Yemi Adaramodu, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, ya ce matsalar tsaro a Najeriya na raguwa, kuma tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa. Ya yaba da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda. Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila WFP ya dakatar da tallafin abinci...
Ya ce: “Ba mu kai inda muke so ba a fannin tattalin arziki, amma muna iya gani cewa abubuwa suna tafiya a hankali. Shugaban Ƙasa ya faɗa sau da dama cewa mun fara fitowa daga ƙunci. “Na san mutane da yawa za su ce ba mu kai ga cikakken cigaba da jin daɗin tattalin...
“Wannan yajin aiki ba wata sabuwar tattaunawa ba ce,” in ji shi. “Abin da muke yi kawai martani ne ga halin ƙunci da mambobinmu ke ciki. Ofishin Akanta-Janar na ƙasa ne ke jinkirta biyan albashin da gangan.” ASUU ta ce ta riga ta gana da hukumomin gwamnati don bayyana matsalolinta, amma ba a ɗauki mataki...
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar ce ta tabbatar aukuwar hatsarin. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta...
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga...
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar...
’Yan sanda sun kama wani matashi mai mai shekara 24 kan zargin ya kashe mahaifinsa mai shekaru 70 a ƙauyen Uzum da ke Ƙaramar Hukumar Giade ta jihar Bauchi. Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce matashin ya yi amfani da sanda ne ya bugi mahaifin nasa a kai, nan...
Gwamna Abba ya bayyana gamsuwarsa da ƙwarewar sabbin jami’an da aka naɗa, inda ya bayyana cewa za su taka rawar gani wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsa. Ya ce jajircewa da ƙwarewarsu na daga cikin dalilan da suka sa aka zaɓe su domin su taimaka wajen ci gaban Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen. Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond. Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.76, kwatankwacin...
Ya ce: “Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, ciki har da na Amurka, na fitar da gargaɗin tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasar su, yana da muhimmanci a faɗa a fili cewa Abuja tana da tsaro ga ‘yan ƙasa da mazauna da kuma baƙi baki ɗaya.” Ya bayyana...
Gonar ta ‘AA Dibine Agro’, ta kasance a yankin Pasali Karshi da ke cikin karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa. Kazalika, kudirin shi ne; nomawa da kuma samar da isasshen Filanten din da za a rika kai wa har zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin sayar da shi. A cewar tasa, abin da gonar ke...
Aminu Boyi ya kara da cewa ido ba mudu ya san kima, idan dai batun nagarta da kwarewa da jajircewa, lallai Shettima ya yi zarra, wannan tasa ba za su laminci wani ya sauya sunansa ba a takatar 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne...
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne...
Hukumar Kula da Yanayi (NiMet), ta sake fitar da gargaɗi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin a daminar bana. A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta bayyana cewa Jihar Akwa Ibom ce ke fuskantar barazana mafi tsanani a halin yanzu. Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a...
Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki. Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman...
Tinubu ya bayyana cewa, aikin titin, wanda aka yi watsi da shi tuni duk da muhimmancin titin a cikin taswirar Abuja, amma yanzu ya kammalu a karkashin jagorancin Ministan babban birnin tarayya. Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya bai wa babban birnin tarayya zaman lafiya, da ci gaban Nijeriya, da kuma bai wa...
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe zaɓe shi kaɗai. “Ku bai wa Kudu tikitin, ku ga sakamako. Amma idan PDP ta ci gaba da tafiya a kan wannan kuskure, to, za ta fuskanci babbar matsala a 2027,” Yusuf ya bayyana. Ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar ba ɗa jam’iyyar...
Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin...
Ministan Bunƙasa Harkokin Ƙarafa, Shuaibu Abubakar Audu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na samun ci gaba wajen farfaɗo da tsohon kamfanin ƙarafa na Ajaokuta da ke Jihar Kogi. Ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na Jihar Kogi a garinsu Ogbonicha da ke Ƙaramar Hukumar Ofu. Mutum...
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aika da sakon taya murnar Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi, yana kira gare su da su rungumi darajoji na sadaukarwa, biyayya da hakuri irin wanda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna. A wata sanarwa da Daraktan Yada labarai na gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Gwamnan ya yi...
“Saboda haka, rundunar ‘yansandan ta nanata cewa, dokar hana duk wani nau’in hawan Sallah a jihar yana nan, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin bukukuwan Sallar Layya ta bana ta 2025 da ake shirin yi domin har yanzu, akwai barazanar tsaro mai karfi a jihar. “An yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa...
