Aminiya:
2025-09-18@00:43:30 GMT

El-Rufai da Ribaɗu na cacar baka kan biyan ’yan bindiga kuɗaɗen fansa

Published: 1st, September 2025 GMT

Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace.

El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ta ƙara ƙamari, duk da cewa gwamnati ta yi ƙoƙarin rage yadda ake rahoto a kafafen watsa labarai.

Har yanzu ina kan bakata cewa waɗannan ’yan bindiga a halaka su baki ɗaya, ba a rika lallashi ko yin sulhu da masu ta’addanci ba. Wannan bai taba aiki a ko’ina ba,” in ji shi a yayin tattaunawar.

Martanin ONSA

A martanin da aka fitar da safiyar Litinin, Ribadu ya bayyana zargin na El-Rufai a matsayin “karya kuma mara tushe.”

An sashe mutum 5 da sace limamai da hakimi a Sakkwato Kwana 70 da ƙaddamar da taraktoci 2,000, har yanzu gwamnati ba ta raba wa manoma ba

Ya ƙara da cewa babu wani lokaci da ofishinsa (ONSA) ko wani ɓangare na gwamnatin Tinubu suka taɓa biyan kuɗaɗen fansa ko bayar da wani irin tallafi ga masu aikata laifuka.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Shari’a na ONSA, Zakari Mijinyawa, ya sanya hannu a madadin Ribadu, an ce, “Wannan iƙirarin ba shi da tushe. A kowane lokaci ONSA na kira ga ’yan Najeriya da su guji biyan kuɗaɗen fansa. Waɗannan zarge-zargen sun saɓa da hujjojin da ake da su a ƙasa.”

Ribadu ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki dabara mai kaifi biyu wajen yaki da ’yan ta’adda — amfani da ƙarfin soja da kuma tattaunawa da al’umma don shawo kan ƙorafe-ƙorafen cikin gida.

Matsalar ysaro a Arewa

Najeriya na fuskantar ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga, waɗanda kan sace mutane don neman kuɗaɗen fansa, su kashe ko su ƙone ƙauyuka, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

A cewar cibiyar nazari ta SBM Intelligence da ke Legas, sama da mutane 4,000 aka yi garkuwa da su a 2023 kacal, inda biya kuɗaɗen fansa na biliyoyin Naira.

Haka kuma ƙasar na fama da matsalar Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, wanda ke ƙara dagula lamarin tsaro.

Ribadu ya kare nsarorin sojoji

Ribaɗu ya ce sojoji da jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara a wasu sassan Jihar Kaduna, ciki har da Igabi, Birnin Gwari da Giwa, inda aka kashe ko kama wasu daga cikin manyan shugabannin ’yan bindiga.

“A Kaduna kaɗai, an halaka manyan kwamandoji kamar Boderi, Baleri, Sani Yellow Janburos, Buhari da Boka. Haka kuma an kama jagororin Ansaru da suka kafa sansanoni a jihar, inda wasu daga cikin jaruman sojojimmu sun rasa rayukansu,” in ji Ribadu.

Ya ce ikirarin El-Rufai na cewa gwamnati na biyan kuɗaɗen fansa bai dace da irin waɗannan sadaukarwa da aka yi ba.

Siyasa ko tsaro?

Wasu masu sharhi sun bayyana cacar bakan tsakanin Ribaɗu da El-Rufai a matsayin wani sabon babi na rikicin siyasa tsakanin tsofaffin abokan hulɗa.

El-Rufai, wanda ya yi wa Tinubu kamfe a zaben 2023, ya daɗe yana sukar gwamnatin, musamman a fannin tattalin arziki da tsaro, yana mai cewa ba ta taka rawar da ake sa ran za ta taka ba.

Ribadu, wanda tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ne, ya yi kira da a guji sanya siyasa cikin al’amuran tsaro, yana mai cewa, “Yaƙi da ’yan ta’adda yaƙi ne na kowa, ba wurin yin siyasa ba ne. Duk wanda ke da matsala ya kamata ya bayar da shawara maimakon yaɗa bayanan ƙarya.”

Me da ke tafe?

Tsaron Najeriya ya kasance babban kalubale ga gwamnatin Tinubu tun hawansa mulki a watan Mayun 2023.

Duk da rahotannin cewa wasu wurare sun samu natsuwa, har yanzu ana kai hare-hare a kauyuƙa, inda ba a samun isassun jami’an tsaro.

Ƙungiyoyin farar hula sun buƙaci gwamnatin ta ƙara saka jari a fannin tsaro, ta ƙara ɗaukar sojoji da ’yan sanda tare da samar musu isasshen horo da kayan aiki na zamani.

Masana kuma sun ja hankalin cewa biyan kuɗaɗen fansa yakan ƙarfafa gwiwar ’yan bindiga wajen ci gaba da sace mutane.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan ta adda Arewa kuɗaɗen fansa Ribaɗu Tsaro biyan kuɗaɗen fansa yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin