Gargaɗi kan zagin Sahabban Annabi Muhammad (SAW)
Published: 1st, September 2025 GMT
Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini.
Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai a Jihar Kwara da wasu sassan Yammacin Najeriya sun shiga ce-ce-ku-ce saboda irin waɗannan kalamai a jan sahabban Annabi (RA).
NASFAT ta ce addinin Musulunci ya umarci a yi biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW) tare da girmamawa da ƙaunar sahabbai baki ɗaya.
Sanarwar da kakakin NASFAT, Alhaji Shamsideen Owolabi Oseni, ya fitar ta ce,“Sahabbai ne suka fara yaɗa addinin Musulunci, suka kare shi, suka adana Alƙur’ani da Sunnah, sannan suka watsa shi ga al’ummomin da suka zo bayan su.”
Yadda aka yi jana’izar ’yar Sarkin Katsina Trust Radio zai fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar LitininƘungiyar ta bayyana cewa yin batanci, ƙyama ko zagin sahabbai babban zunubi ne da malamai suka bayyana tun fil azal a matsayin alamar taɓewa, wanda masu aikatawa suna iya shiga kafirci.
Ta ambaci manyan malaman Musulunci kamar Imam Ahmad, Imam al-Ɗahhaawi, Abu Zar’ah al-Raazi da Ibn Taymiyyah a cikin waɗanda suka yi gargaɗi cewa irin yin ɓatanci ga Sahabbai na girgiza tushen addinin Musulunci.
NASFAT ta ƙara da cewa ƙaunar sahabbai alama ce ta imani, yayin da ƙin su ke nuna munafunci ko kafirci. Ta ce Allah Ya yaba musu a cikin Alƙur’ani kuma Ya nuna yardarsa da su.
Kungiyar ta buƙaci malamai su kiyaye minbarorinsu daga kalaman rarrabuwar kawuna, tare da jaddada koyarwar da za ta ƙarfafa haɗin kai da gina al’umma ta fuskar addini da rayuwar yau da kullum.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɓatanci
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.
Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabalaA cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.
“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).
“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.