2025-10-13@15:47:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5919
«lashe kyautar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su. Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai tabbatar da cewa, rahotannin ƙage ne kawai. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025 Labarai SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati October 9, 2025 Labarai An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba October 9, 2025
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da ƙwato bindigogi guda 4, da muggan makamai da dama. Ta kuma kama wani ɓangare na kuɗin fansa da ake zargin an biya masu garkuwa da mutane a wasu hari daban-daban a jihar. Nasarar kamen dai ya biyo bayan wasu jerin samame da jami’an ’yan sanda da na ’yan banga suka yi a tsakanin ranakun 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, inda suka yi ta kai farmaki kan gungun masu garkuwa da mutane da ke kai hari a ƙananan hukumomin Anchau, Ikara da kuma Makarfi. Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC Ma’aikatan jami’a sun yi zanga-zanga a Jami’ar...
Majalisar magabata a Najeriya ta amince da nada Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga jihar Kogi a matsayin sabon shugaban hukumar zaben kasar INEC. Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce Shugaba Tinubu ne ya gabatar da sunan Farfesa Amupitan ga majalisar domin neman amincewarta. Tinubu ya shaida wa majalisar cewa Farfesa Amupitan ne mutum na farko daga jihar Kogi da zai rike mukamin, kuma ba dan siyasa ba ne. Nan take kuma duka mambobin majalisar suka amince da shi ba tare da sabani ba. A yanzu shugaba Tinubu zai aika sunansa zuwa majalisar dattawan Nigeria domin amincewarta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Farfesa Amupitan, mai shekara 58, malami ne a Jami’ar Jos...
‘Yan majalisar dai sun amince da naɗin, inda Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya. Dangane da kundin tsarin mulkin 1999 (kamar yadda aka gyara), yanzu Shugaba Tinubu zai aika da sunan Amupitan zuwa Majalisar Dattawa don tantancewa. Amupitan, mai shekaru 58, daga Ayetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi, Farfesa ne a fannin shari’a a Jami’ar Jos, Filato, kuma tsohon ɗalibin jami’ar ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta October 9, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin October 9, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso...

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025 Daga Birnin Sin Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban ƙasar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, a ranar Alhamis. “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da Amupitan a matsayin wanda zai cike gurbin Shugaban Hukumar INEC, biyo bayan wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu.”
A yayin yanke hukuncin, kotu ta bayyana cewa: “Na farko (INEC) da na biyu (Farfesa Mahmood Yakubu) an yanke musu hukuncin tura su gidan gyaran hali saboda rashin bin hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Osogbo, Jihar Osun, ta bayar a shari’a mai lamba FHC/OS/CS/194/2024 a ranar 17 ga 5 Fabrairu, 2025.” Kotu ta kuma umarci Sufeton ‘yansanda na ƙasa da ya kama Yakubu tare da tabbatar da fara shari’ar hukuncin raina kotu cikin kwanaki bakwai daga ranar da aka yanke hukuncin. Bugu da ƙari, kotu ta ci tarar INEC da Yakubu Naira 100,000 domin biyan masu shigar da ƙarar saboda raina umarnin kotu. Masu shigar da ƙarar sun haɗa da Action Alliance, Farfesa Julius Adebowale, Injiniya Olowookere Alabi, Barrista...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya kiyasta cewa Najeriya ta yi asarar kimanin dala biliyan 10, kwatankwacin Naira tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana hakan a Maiduguri ranar Laraba yayin ƙaddamar da wani shirin farfaɗo da rayuwar yara da rikici ya shafa ta hanyar ba su horo da tallafi. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya An wakilta Saeed ta hannun Manajan Kare Yara na UNICEF, Shah Mohammad Khan, inda ta ce rikicin da ya daɗe ya rage girman tattalin arzikin ƙasar, ya kuma lalata...
Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya. Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Yusif Bashir da motar asibiti ƙirar Toyota Land Cruiser mai lambar ONG-0777, bayan ya shigo da ita ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar. Tahir, ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen miƙa sh ga rundunar ’yan sandan jihar, domin ci...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi, za su fuskanci martani mai tsanani Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi a mashigar tekun Farisa, da mashigar Hormuz da tsibirin Iran, za su fuskanci hukunci mai tsauri, nan take, murkushewa, da kuma nadama. A cikin sakon taya murnar zagayowar ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Pakpour ya bayyana cewa: “A jajibirin ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, yana mika sakon taya murna ga babban matsayi na kwamandoji da mayakan da suka yi...
Shugaban kasar Ecuador ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi Ministan Makamashi na Ecuador, Ines Manzano ya sanar a ranar Talata cewa: An yi yunkurin kashe shugaban kasar Daniel Noboa kuma an kama wasu mutane biyar da ke da hannu a ciki makarkashiyar. Manzano ya ce “Motar Noboa na kewaye da gungun mutane kusan 500 da suke jefanta da duwatsu a lokacin da yake tafiya a cikin ayarin motocin zuwa lardin Cañar, inda aka shirya zai sanar da jerin ayyukan samar da ababen more rayuwa.” Ta kara da cewa: “Daga baya an samu alamun harsashi a motar, amma Noboa bai samu rauni ba a harin.” Hukumomin kasar sun sanar da cewa: Wadanda ake tsare...
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed. Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba. Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari. Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan...
An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro. Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma. Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin. Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27. A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da kungiyar injiniyoyin ma’adanai ta Najeriya a matakin jiha da tarayya domin tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma a karshen taron kasa da kasa karo na ashirin da hudu. Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron shekara-shekara da taron kasa da kasa na shekara ashirin da hudu da aka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja. Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata Injiniya Idris Abubakar ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin dorewa da aikin hakar ma’adanai na da matukar muhimmanci wajen kare shirin makamashi maras illa a matsayin Jigon gwamnatin sa. A nasa...
Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara. Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin. Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun. Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
Majalisar Wakilai, ta yi watsi da zargin da Ƙasar Amurka, ta yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Wannan martani na zuwa ne bayan wani Sanatan na Amurka, Ted Cruz, ya gabatar da ƙudirin doka a Majalisar Dattawan ƙasar, inda ya ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya A yayin gabatar da ƙudirin ya buƙaci a ƙaƙaba wa wasu jami’an Najeriya takunkumi. Cruz ya ce: “ Ana kashe Kiristocin Najeriya saboda addininsu… lokaci ya yi da za a ɗauki mataki na gaske kan jami’an Najeriya da ke taimaka wa...
Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi. Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai dalar Amurka miliya 18. Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da...
Bankin Duniya ya ce har yanzu talauci na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar. A wajen ƙaddamar da rahoton ci gaban da aka samu a Abuja, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025. Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe Ya ce duk da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar...
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar iran Mohammad Eslami da manyan jami’a daga hukumar rasatom ta hadin guiwar ayyukan makamashin nukiliya sun gana a birnin Tehran kuma sun tattauna kan yadda za su yi aiki tare a bangaren shirin ta na nukiliya na zaman lafiya, Nikolai Spassky ya kawo ziyara iran ne a birnin Tehran tun bayan ziyarar da Eslami ya kai birnin mosko a ranar 24 ga watan satumba, inda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, na yin aiki tare wajen gina karamar tashar nukiliya iran. Haka zalika bangarorin biyu sun tattauna kan yarjejeniyar da aka kula lokacin da Eslami ya kai ziyara da ya hada da yin aiki tare a cibiyar nukiliyar iran...
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu Mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba. “Duk da cewa Najeriya na daraja...
Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci. Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta kasance mai zaman kanta, ba ta karkata ga wani ɓangare na siyasa ba, kuma tana iya gudanar da aikinta cikin gaskiya...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinBabban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025Daga Birnin SinYawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025
Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta...

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinSin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa October 8, 2025Daga Birnin SinSin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare October 8, 2025Daga Birnin SinKasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata October 7, 2025
Shugaban wanda ya samu wakilcin Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, Shugaban kasar ya ce tuni gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da al’ummar Ogoni domin magance duk wata matsala da za ta iya kawo cikas ga tashar domin fara samar da ɗanyen mai.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiKwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi October 8, 2025Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025
An kashe wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36, yayin da wasu ’yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a kusa da ƙauyen Inzon da ke yankin Fan, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato. Aƙalla shanu 49 kuma sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo. Ya ce ’yan bindigar sun buɗe...
Jaridar Daily Mail ta kasar Burtaniya ta nakalto firay ministan HKI Benyamin Natanyahu yana gargadin Amurka kan abinda ya kira, makamai masu linzami masu keta nahiyoyi wadanda JMI take ginawa barazana ce ga Amurka. Ya ce makaman suna iya isa biranen Amurka daga cikin har gidan Trump da ke ‘Mar-a-Lago’, a bakin ruwa na Palm Beach a jihar Florida. Daily mail ta nakalto Natanyahu yana fadar haka a hirar da ta hada shi da wani dan jirada mai suna Ben Shapiro. Ba tare da bada wata hujja ko dalili ba, Natanyahu ya ci gaba da cewa, makaman wadanda suke iya zuwa wurare masu nisan kilomita 800 zasu kai biranen washington da kuma NewYork har da kuma gidan shugaba Trump dake...
Dalibai da malaman Jami’o’i a kasar Burtania sun bar ajujuwansu don halattar ganganmi a cikin jami’o’insu, na goyon bayan al-ummar Falasdinu da kuma yin tir da gwamnatin kasar saboda goyon bayan da take bawa HKI a kissan kiyashi, wanda ya kai shekaru biyu kenan a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa zanga zangar bata takaita a jami’o’in birnin London kadai ba, sai dai an gudanar da su a manya –manyan biranen kasar duk tare da gargadin jami’an yansandar kasar kan cewa an haramta zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kasar. Sauran biranen da aka gudanar da gangamin dai sun hada Glasgow, Manchester, Bristol, Sheffield da Edinburgh. Daliban da kuma malamansu suna rera taken “Yanci ga Falasdinu...
Alkaluman da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin wato China Railway ya gabatar, sun nuna cewa, ana sa ran jigilar fasinjoji kimanin miliyan 21 da dubu 750, ta jiragen kasa a kasar Sin a yau Laraba. Kana tun daga ranar 29 ga watan Satumban da ya gabata, wato ranar da aka kaddamar da aikin jigilar fasinjojin da suka yi tafiye-tafiye, a lokacin hutun bikin tunawa da kafuwar kasa da na Zhong-Qiu, zuwa jiya Talata, an riga an kwashe fasinjoji fiye da miliyan 160 ta jiragen kasa a kasar Sin.Yau ce ranar karshe a hutun na wannan karo, don haka ake sa ran ganin karuwar zirga-zirgar mutane da suke kokarin komawa gidajensu daga wuraren da suka yi bulaguro. Hakan ne...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai. Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa. Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe. An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a. “Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA LabaraiGwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu October 8, 2025Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Labarai‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa October 8, 2025
Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025. Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban. Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25. kazalika, NERC ta ce...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu. Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20. Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rabon gidaje 72 ga malamai da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Mafa. Zulum ya ce Marbel ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke Mafa, kuma ba ta taɓa barin wurin ba ko...
Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...
Shugabar Cibiyar Nazarin Karatu da Ci Gaban Ilimi ta Najeriya (NCRRD) da ke Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Amina Adamu, ta bayyana damuwa kan yadda dalibai ke ƙara gujewa amfani da dakunan karatu, tana danganta hakan da dogaro da kirkirarriyar fasaha ta AI. Da take jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan nazarin karatu da nazari da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Amina ta ce da dama daga cikin ɗalibai yanzu suna kammala karatun jami’a ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ko sau ɗaya ba. Yadda zargin mallakar takardun bogi ya yi awon gaba da kujerar Ministan Tinubu Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC “Muna da daliban da ke yin rajista...
Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...
Ya gargaɗi masu aikata laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci, inda ya bayyana cewa waɗanda aka kama tuni aka miƙa su kotu.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Labarai‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025LabaraiCika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya October 7, 2025
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci Banki bayan harin, inda ya yaba da jarumtar mazauna garin tare da alƙawarin bunƙasa tsaro a yankin.Zulum, ya kuma sanar da shirin sake mayar da mazauna ƙauyuka uku; Kumshe, Tarmu’a da Bula Yobe, sannan ya tabbatar da cewa aikin gyaran hanyar Banki ya an fara shi.Ya buƙaci matasa su yi rajistar katin zaɓe, tare da jan hankalin ‘yan kasuwa su haɗa kai da jami’an tsaro domin ɗorewar zaman lafiya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025LabaraiCika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya October 7, 2025LabaraiSSANU, NASU Za Su Gudanar Da...
A faransa ana ci gaba da kira ga shugaban kasar Emmanuel Macron da ya yi murabus. Murabus na firaminista Sébastien Lecornu ya yi, jim kadan bayan gabatar da sabuwar gwamnati, ya haifar da zaman dar-dar ga makomar Emmanuel Macron a siyasance. Kiraye-kirayen rusa majalisa ko murabus na shugaban kasar na karuwa, yayin da jam’iyyar National Rally (RN) mai ra’ayin rikau ke kira da a gudanar da zaben wuri-wuri. Murabus din Lecornu, wanda aka amince da shi a ranar Litinin, ya haifar da kiraye kirayen ‘yan siyasa da ke neman a rusa Majalisar Dokoki ta kasar ko kuma murabus na shugaban kasar. Tun bayan zaben ‘yan majalisu da aka yi a shekarar 2024, babu wata jam’iyya dake da rinjaye a...
Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
Shirye-shiryen sun kammala domin Shugaban Ƙasa ya sanar da sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), bayan da Farfesa Mahmood Yakubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara goma a ranar Talata. Kafin Yakubu ya sauka daga mukaminsa, rahotanni sun nuna cewa fadar shugaban ƙasa na nazarin mutum uku da ake has ashen za su iya maye gurbinsa: Farfesa Joash Ojo Amupitan, Mai Shari’a Abdullahi Mohammed Liman da Farfesa Lai Olurode. Wata majiya a fadar shugaban ƙasa ta shaida wa Aminiya cewa an kammala nazari, kuma Farfesa Amupitan ne ke kan gaba a jerin waɗanda ake hasashen don maye gurbin tsohon shugaban INEC. Majalisa za ta yi dokar kula da harkar Crypto da POS Ya kamata a karɓe...
Ya gargadi masu kafa kungiyoyi daban-daban a Arewa, yana kiran irin waɗannan ƙungiyoyi “barazana ga haɗin kan Arewa.” Haka kuma ya yaba wa sojojin Nijeriya bisa kokarinsu da sadaukarwa wajen yaki da matsalar tsaro. Alhaji Dalhatu ya kuma yi Allah wadai da “ƙungiyoyin marasa kishin ƙasa” da suka jawo rikicin baya-bayan nan a matatar mai ta Dangote, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani. A cewarsa, kwanan nan an samu rikice-rikicen maganganu masu karo da juna daga wasu jami’an ACF a matakin kasa da jihohi, wanda hakan ya sa dole a kafa tsarin sadarwa mai tsauri. “Majalisar Amintattu tana da ikon da nauyin Ya bayyana cewa taron, wanda shugabannin jihohi, sakatarori, da mambobin Arewa 100% Focus Group suka halarta, zai...
Wannan sanarwar ta baya bayan nan da kasar Sin ta yi, ya samu yabo sosai, musammam daga sakatare janar na MDD, yana jaddada cewa, shirin na Sin na da muhimmanci matuka ga tunkarar sauyin yanayi. Su ma kafafen yada labarai na kasa da kasa da manyan jami’an hukumomi da kasashe da dama, sun yaba wa shirin, wanda ya nuna cewa, ana kara ammana da irin rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin da suka shafi duniya. Ba alkawari da gabatar da shirin kadai take yi ba, ta kasance mai aiwatar da su a aikace kuma ana ganin nasarorin da take samu a zahiri. Zuwa yanzu, babu wata kasa da ta bayar da gudunmuwa a wannan bangare kamar kasar Sin, kuma...
Takardar mai kwanan watan Oktoba 6, ta samu sa hannun Prince Peters Adeyemi, babban sakataren NASU, da Comrade Mohammed Ibrahim, shugaban SSANU na kasa.ShareTweetSendShareMASU ALAKA LabaraiƁatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci October 7, 2025LabaraiTinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk October 7, 2025Ra'ayi RigaCikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025
Jami’an kare hakkin dan’adam na MDD sun nuna jin dadinsu dangane da hukuncin da kotun duniya ta manyan laifuka ( ICC) ta yanke akan mutum na farko da aka tuhumka akan laifukan Darfur na kasar Sudan. A jiya Litinin ne dai kotun manyan laifuka ta duniya ta yanke hukunci akan Ali Muhammad ali Abd-Al-Rahman wanda ake yi wa lakabi da Ali Khushayb, bisa samunsa da laifi akan laifukan yaki a Darfur shekaru 20 da su ka gabata. Daga cikin laifukan da aka tabbatar da akan Ali Kushayb da akwai bayar da umarnin yi wa mutane da dama kisa, da kashe fursunoni biyu da gatari. Alkalai uku ne su ka yi zaman shari’ar da aka yanke hukuncin tare da samun wanda...
Shugaban ofishin jagoran juyin musulunci na Iran, Hujjatul Islam Wal Muslimina Muhammad Gulpayagani ya bayyana yunkurin nan na: Goyon Bayan Iran.” Da cewa, aikin da suke yi yana a karkashin amsa kiran jagoran juyi ne wanda ya yi kira da a taimakawa waddanda su ka cutu daga hare-haren HKI. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Hujjatul-Islam Muhammad Gulpayagani yana bayyana muhimmin matakin da Ayatullah Khamnei yake dauka a fagen gwgawarmaya, yana mai kara da cewa; Shi ne wanda yake dauke da tutar gwgawarmaya akan wannan tafarkin cikin dogara da Allah madaukakin sarki da tafiya akan tafarkin Ahlul Bayti ( a.s). Hujjatul-Islam golpayagani ya ambaci wasu ayyukan da yukurin na Iran take yi wajen taimakawa wadanda su ka cutu daga hare-haren...
Tinubu, a cikin wata wasika da ya aikewa kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen wanda ya karanta a zaman majalisar a ranar Talata, ya kuma buƙaci majalisar ta amince da batun shirin Sukuk da zai kai kusan dala miliyan $500 a cikin ICM.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Ra'ayi RigaCikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka October 7, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025LabaraiGwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu October 7, 2025
Babban jami’in diplomasiya a fadar Vatican ya bayyana cewa sama da shekaru biyu ke nan hki tana kai hare hare kan falasdinawa fararen hula a yankin Gaza adaidai lokacin da kasashen duniya suka kasa tsayar da kisan kare dangi da take yi a yankin da ta killace Cardinal pietro parolin sakataren harkokin wajen fadar Vatican,shi ne yayi wannan bayani a taro na biyu da aka yi kan ambaliyar Aqsa mummunan harin da kuniyar Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan oktobn shekara ta 2023, Tun daga lokacin gwamnatin yahudawan sahyuniya ta kaddamar da harin kan fararen hula a yankin Gaza inda ta yi sanadiyar mutuwar dubban falasdinawa da suka hada da mata da yara kanana, tare da...
Hukumar kula da yan gudun hijirar a majalisar dinkin duniya ta jinjinawa kasar Iran game da kokarin da tayi wajen kulawa da miliyoyin yan gudun hijira kasar Afghanistan , da suka zauna a kasar na tsawon shekaru, Babban darakta na hukumar ta IOM shi ne yayi wannan bayani ga Mohammad Batgae mtaimakin ministan harkokin cikin gidan kasar iran a birnin janeva a jiya litinin, a wani taro da suka gudanar a bayan babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 76 da hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya take gudanarwa. Ana sa bangaren bathaei babban jami’I na kasar Iran ya bayyan yadda jamhuriyar musulunci suka bada kula ta musamman ga dubban yan gudun hijiran kasar ta Afghanistan...
Majalisar Wakilai ta fara yunkurin kafa dokar da za ta daidaita harkokin kudin zamani na Crypto da kuma harkokin POS a Najeriya. Shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, ya ce yin hakan ya zama dole saboda yadda damuwa ke karuwa kan zamba, laifukan intanet, daukar nauyin ta’addanci da cin zarafin masu amfani da irin wadannan hanyoyin kudi. Ya ce, “Akwai damuwa ta gaskiya kan yadda ake iya amfani da kudin zamani wajen daukar nauyin ta’addanci da safarar kudaden haram, la’akari da yadda tsarin yake da duhu, dole a yi tsayayyiyar doka doka ba, da kuma cikakken binciken yadda ake sarrafa kudaden.” Abba ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wani kwamitin wucin gadi a ranar Litinin domin nazarin tasirin tattalin arziki,...

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...
An yi wa yara miliyan biyu da dubu takwas allura, yayin aikin rigakafin cutar Polio, kyanda, da kuma Gaida a jihar Sakkwato. Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin da aka gudanar a garin Bodinga da ke karamar hukumar Bodinga. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai na ofishin mataimakin gwamnan jihar, Garba Muhammed, Alhaji Ahmed Aliyu ya raba wa manema labarai, ya bayyana cewa aikin polio din zai gudana ne a daukacin unguwanni 244 dake fadin jihar. Don haka ya yi kira ga shugabannin al’umma da na addini da kuma abokan ci gaba da masu ruwa da tsaki da su ba da himma wajen...

Wani Mai Rajin Kare Hakkin Dan Adam A Spaniya Yayi Tir Da Isra’ila, Ya Bukaci A Dauki Mataki Kanta .
Tsohon magajin garin Bacelona Ada collaou da sauran masu rajin kare hakkin dan adam yan kasar spaniya dake cikin jiragen ruwan agaji na Sumud Flotilla da Isra’ila ta kama a baya bayan nan, sun yi tir da irin azabartar da su da isra’ila ta yi kuma sun sha alwashin daukar matakin shari’a a kanta, Shi ma shugaban bangaren hagu na jam’iyar podemos ya sanar da shirye shiryen maka prime minister Isra’ila Benjamen na tanyaho a gaban kuliya manta sabo, Matakin shariya da kungiyoyinn farar hula da sauran jam’iyun siyasa a kasar Spaina ta dauka yana kara nuna yadda duniya ke yin matsin lamba kan gwamnatin yahudawan sahyuniya, kuma zai sanya bangaren sharia na kasar spain ya gudanar da bincike na...
Sayyid Ali Khomaini jikan marigaya imam khomaini yardar Allah ta tababtar gareshi yayi kira ga alummar kasar iran da su kara kaimi da tsayin daka wajen kare kasar daga barazanar manyan kasashen duniya, yayi gargadin cewa akwai barazana sosai inda aka yi sakaci da shisshigin makiya. Wanan kiran yana zuwa ne a daidai lokacin da zaman tankiya yake kara Kamari tun bayan yaki kwanaki 12 da aka yi tsakanin iran da HKI bayan da ta kai wa iran hari, hadin kai alummar kasa da tsayin daka da suka nuna ya tunkude makircin makiya . Sayyid Ali khomaini ya kara da cewa wayewa da sanin abokan gaba da tsayuwa akan Imani,da ya bayyana a lokacin yakin Uhud mai cike da tarihi,...
Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da shugabannin tsaro bisa goyon bayansu wajen yaƙi da rashin tsaro a Kogi.Tags: KogiOdodoTsaroShareTweetSendShare Sadiq Related LabaraiMajalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya 1 hour agoManyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa 2 hours agoManyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 3 hours ago
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu. Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin. Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana. Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na...
Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa. Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar. Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare. Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael...
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
Ya ƙara da cewa kwamitin zai gudanar da zaman jin ra’ayoyi daga masana da sauran masu ruwa da tsaki kafin ya kammala rahotonsa.Tags: BincikeKiriftoKwamitiMajalisar WakilaiPOSShareTweetSendShare Sadiq Related Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa 1 hour agoManyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 2 hours agoManyan LabaraiKada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 14 hours ago
Takardun shaida na bogi na daya daga cikin matsaloli dake kara addabar Najeriya a fannoni da dama. A wasu lokuta ana samun mutane da ke amfani da takardun makaranta ko na ƙwarewa da ba su cancanta da su ba domin samun aiki, mukami, ko wasu fa’idodi da suka wajaba ne kawai ga waɗanda suka cancanta. Wannan dabi’a ta zama barazana ga ci gaban ƙasa da amincin al’umma gaba ɗaya, domin tana lalata tsarin ilimi, rage darajar masu gaskiya, da haifar da rashin inganci a wuraren aiki. Haka kuma, tana haifar da rashin amincewa tsakanin gwamnati da jama’a, da kuma tsakanin mutane da kansu. NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’ DAGA LARABA: Tasirin...
Ƙungiyar shugabannin jam’iyyun siyasa (IPAC) ta ce lokaci ya yi da za a cire ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) daga hannun Shugaban ƙasa. Ƙungiyar ta ce kamata ya yi a kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai riƙa yin naɗin shugaban INEC da kwamishinoni da sakatare na hukumar domin tabbatar da gaskiya da cin gashin kai na hukumar. Shugaban ƙungiyar IPAC, Dakta Yusuf Mamman Ɗantalle, ne ya bayyana haka a wani taro da suka yi da kwamitin Majalisar Wakilai da ke nazarin kundin tsarin mulki a Abuja. Ya ce tsarin da ake amfani da shi yanzu na bai wa shugaban ƙasa damar zaɓar shugaban INEC na iya rage amincewar jama’a da hukumar. Jerin...
Irabor ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta bi hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar tsaro, ba ta hanyar amfani da sojoji kaɗai ba.Ya ce ya kamata a samar da manufofi masu inganci da za su rage talauci, rashin aiki da yawan yara marasa zuwa makaranta.“Idan muka rage yara marasa zuwa makaranta da kuma marasa aikin yi, za mu rage yawan mutanen da ‘yan ta’adda ke iya ɗauka aiki,” in ji shi.Ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da su daina sa siyasa a batun harkar tsaro.A ranar bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa dakarun Nijeriya suna samun nasara a yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane, amma jam’iyyun adawa sun ce matsalar...
A yayin Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, Uche Nnaji, ke fuskantar matsin lamba bayan ya amsa a gaban kotu cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba, zargin sa da amfani da takardun bogi da kafar PREMIUM TIMES ta bankaɗo ya ƙara ƙarfi. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce za ta jira hukuncin kotu kafin ta ɗauki mataki kan batun Nnaji. Wannan ya sanya Mista Nnaji cikin jerin wasu ministoci da suka fuskanci irin wannan tuhuma: – Uche Nnaji Uche Nnaji, wanda Shugaba Bola Tinubu ya nada a watan Yuli 2023, ya gabatar da takardar digiri da kuma takardar kammala aikin NYSC a lokacin tantancewa. Amma jami’ar UNN da hukumar NYSC sun ce ba...

Iran ta ce Amurka da Isra’ila ne ke da alhakin duk abin da ya faru a hare-hare kan cibiyoyinta na nukiliya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, Iran na dora alhakin kai hare-hare ba bisa ka’ida ba kan cibiyoyin nukiliya a kan Amurka da Isra’ila. “Ba shakka muna la’akari da gwamnatin Isra’ila da Amurka a matsayin masu alhakin hare-hare a kan cibiyoyin nukiliya na Iran,” in ji Esmaeil Baqaei yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin. Ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da wakilin kamfanin illancin IRNA ya tambaye shi kan furucin na baya-bayan nan da Sakatare Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi ya yi, wanda ya ce bai ce Iran na kokarin kera makaman nukiliya a cikin rahotannin da ya bayar ba, a wani yunkuri na wanke kansa daga tuhumce-tuhumce...
Sakataren harkokin wajen Vatican, Cardinal Pietro Parolin, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa, “yakin da sojojin Isra’ila suke yi a yankin zirin Gaza yaki ne a kan mutane raunana marasa kariya.” Cardinal Parolin ya yi ishara da cewa “dole ne kasashen duniya su nuna shakku kan sahihancin ci gaba da samar da makamai wadanda ake amfani da su kan fararen hula a Gaza.” A lokuta da dama Paparoma Leo na 14 ya yi Allah wadai da yakin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza, yana mai yin kira da babbar murya ga kasashen duniya da su kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, wanda aka kwashe kusan shekaru biyu ana yi. Share 0 0...

Sisi: Samun zaman lafiya na gaskiya a Gabas ta Tsakiya ya dogara da kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi ya ce, “Za a samu zaman lafiya na gaskiya a yankin Gabas ta Tsakiya ne kawai idan an kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa ka’idojin kasa da kasa da kuma hanyar da za ta maido da hakkokin masu hakki.” A jawabin da ya yi na bikin cika shekaru 52 na nasarorin da larabawa suka samu a yakin watan Oktoban 1973, Sisi ya yi nuni da cewa, yin amfani da karfin tuwo domin aiwatar manufa ne ke haifar da tashin hankali, yayin da zaman lafiya da aka gina bisa adalci yana samar da daidaito na gaskiya da kuma dorewar zaman tare a tsakanin al’ummomi.” Ya yi nuni da cewa, tsagaita bude wuta, musayar...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 nan take, kuma ta fitar da sabon farashin cikin kwana biyu. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta sanar da rafin kimanin N200,000 a kan farashin da maniyyata suka biya a bara. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da umarnin shugaban kasa yayin wani taro da ya yi da shugabanni da mambobin hukumar NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Litinin. Shettima ya buƙaci a samu hadin kai tsakanin jami’an jihohi da na tarayya, ciki har da gwamnoni, wajen fitar sabon farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar. An fara...
Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai farmaki a wata gonar wake, inda suka kashe wani mai gonar yana tsaka da aiki a Ƙaramar Hukumar Monguno da ke Jihar Borno. Shaidu sun ce makiyaya kimanin 10 ne suka kai harin bayan sun kutsa da shanunsu suka yi kiwo a wasu gonaki da misalin ƙarfe 12:20 na ranar Asarar a Dajin Ngolom. Ɗaya daga cikin manoman da makiyayan suka kutsa gonarsu, Abatcha Abatcha da ke yankin Gana Ali Ward, manoman sun buƙaci makiyayan su bar gonakin, amma sai lamarin ya rikice zuwa tashin hankali. “Makiyaya sun kai mana hari da sanduna. Ɗaya daga cikin manoman da Allah Ya yi wa rasuwa, Bakulu Bafindi mai shekaru 30 daga unguwar Sabon Lamba...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyanawa kwamitin al-amuran harkokin waje na majalisar dokokin kasar iran kokarin da ma’aikatarsa take na kare muradun JMI na amfana da fasahar makamashin nukliya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taron ne, a ma’aikatar harkokin wajen kasar a jiya Lahadi. Kuma ministan ya bayyana wa kwamitin dalla dalla kan irin sabbin kokarin diblomasiyya wanda ma’aikatar take yi don ganin ta kare halattaccen shirin makamashin nukliya na kasar Iran. Ministan ya bayyanawa kwamintin, irin ayyukan da ma’aikatarsa ta yi a shekarar da ta gabata a bangaren makamashin Nukliya, kara kyautata dangantaka da kasashe makobta, da ci gaba da karfafa zumunci da manya-manyan kungiyoyi da kasa shen...
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki don ƙirƙirar yanayi mai sauƙin zuba jari, da zaman lafiya don masana’antu, da haɓaka tattalin arziki mai dorewa. A ƙarshe, ya kira masu ruwa da tsaki da su fifita tattaunawa a wajen neman mafita maimakon rikici, yana cewa, “Nijeriya ƙasa ce mai girma da ke neman mafita a abubuwa da yawa, ya zama dole ne mu haɗa kai wajen kare abin da ke amfanar ƙasa baki ɗaya.” Tags: Aliko DangoteShettima ShareTweetSendShare Abubakar Sulaiman Related Manyan Labarai Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5 4 hours ago Manyan Labarai Uba Sani Ya Amince...

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu
Manufofin da aka tsara sun karfafa kashe kudi. Kafin wannan hutu, gwamnatin tsakiya ta ware yuan biliyan 69 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9.7 a matsayin lamuni na musamman don tallafa wa hada-hadar kayayyakin masarufi, wanda hakan ya kai ga jimillar abin da ake warewa a shekara ta kai yuan biliyan 300. Daga watan Janairu zuwa na Agusta, shirye-shiryen ba da tallafi na hada-hadar kasuwanci sun jawo hankulan masu nema miliyan 330, wanda hakan ya haifar da cinikin sama da yuan tiriliyan 2. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare Sulaiman Related Daga Birnin Sin Karamin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas Ya Yi Bikin Bunkasa Al’adu Na Bikin Tsakiyar Kaka 1 hour ago Daga Birnin...
A zaman da aka yi a yau, lauyan Ministan ya shaidawa kotu cewa an isar da takardun shari’ar ga dukkan waɗanda ake ƙara, yana mai zargin Shugaban Jami’ar UNN da saɓa umarnin kotu ta hanyar rubuta wasika ga jaridar yanar gizo Premium Times, inda ya ƙalubalanci ikirarin Nnaji na cewa tsohon ɗalibin jami’ar ne. A cewar lauyan, wannan wallafa ta karya umarnin kotu na barin komai a yadda yake har sai an saurari shari’ar. Sai dai lauyan jami’ar ya musanta yin wani kuskure, amma ya ce za su ja hankalin jami’an su don bin umarnin kotu yadda doka ta tanada. Tags: MinistaNnajiUNN ShareTweetSendShare Naziru Adam Ibrahim Related Ilimi Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa...

Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5
A cewar Bankin Duniya, talauci a tsakanin mazauna karkarar Nijeriya ya kai kashi 75.5 cikin dari, wanda ke nuna ƙaruwar rashin daidaito da kuma tsananin matsin tattalin arziki a fadin kasar. Ministan ya ce, gwamnati ta kuma kuduri aniyar inganta hasashen tattalin arziki da inganta sauye-sauyen da zai sanya Nijeriya ta samu ci gaba mai ɗorewa. Bagudu ya jaddada cewa, gwamnatin da shugaban kasa Bola Tinubu ke jagoranta tana ba da fifiko wajen samar da ayyukan yi ta fuskar fasahar zamani, noma, tattalin arziki da ƙirƙire-ƙirƙire. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
“Akwai malamai da yawa da ba su cancanta da koyarwa ba. Muna da masu koyarwa a ajujuwa amma ba su da cancantar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta. Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da jikinsu da zuciyarsu, amma rashin amintattun shaidar koyarwa a hukumance ke hana basu aikin koyarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya “WFP” ta bayyana cewa: Rage agajin jin kai na barazana ga miliyoyin mutane da suke fama da yunwa a Somaliya Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta yi gargadin cewa: Miliyoyin mutane a Somaliya na cikin hadarin fuskantar yunwa da rashin abinci mai gina jiki, saboda tsananin karancin kudade da ya tilastawa kungiyar ta WFP rage yawan mutanen da take tallafawa da taimakon abinci na ceton rai da sama da kashi biyu bisa uku. A watan Nuwamba, za a tilastawa Hukumar WFP ta rage adadin mutanen da ke samarwa tallafin abinci na gaggawa zuwa 350,000 kawai, wanda ya ragu da miliyan 1.1 a watan Agustan da ya gabata. Wannan...
Sanarwar ta ce, hare-haren kakkaɓe maɓoyar ‘yan bindigar na zuwa ne a karkashin shirin ‘Operation Lafiya Nakowa’, da nufin fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar Taraba. Ya kara da cewa, harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a kusa da Tarhembe, Tornyi, TY Farm, da ɗaukacin yankin Kando da ke yankin Tati, karamar hukumar Takum, da kuma rahotannin lalata gonaki a karamar hukumar Ussa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga Abdullahi Usman, Kaduna Sardaunan Ikulu, Alhaji Dr. Isma’īl Yusuf Ashafa, ya kira mata da matasa a garin Ikulu da su shiga harkokin siyasa domin kawo ci gaba a yankinsu. Ya fadi hakan ne a lokacin Taron Ikulu da aka shirya a Kaduna karkashin jagorancin Ikulu Political Forum (IPF). Ya jaddada cewa babu wata al’umma da za ta bunkasa sai an samu hadin kai tsakanin jama’a da kuma cikakkiyar rawar da matasa da mata ke takawa a siyasa. Ya kara da cewa wajibi ne a wayar da kan matasa da mata, a ilimantar da su, sannan a motsa su su gane muhimmancin jagoranci ta hanyar jam’iyyun siyasa. Hakazalika, ya gargadi ‘yan siyasa a yankin da su guji “siyasar do ko...
Ya kara da cewa yan shekarun da suka gabata, an yi shakku kan dorewar wasan Hockey a Nijeriya, amma yanzu tawagarmu ta mata ita ce ta zo matsayi na 3 a Afirka, yayin da tawagar maza ke matsayi na 4, wadannan nasarorin sun nuna irin yadda muka himmatu wajen ganin mun kara inganta wannan wasa a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Firaministan ƙasar Faransa, Sebastien Lecornu, ya yi murabus daga muƙaminsa kwana guda bayan ya kafa gwamnatinsa. Fira Minista Sebastien Lecournu ya sanar da ajiye mukaminsa ne a safiyar Litinin ɗin nan bayan ya yi wata da Shugaba Emmanuel Macron. Ya yi murabus ne washegarin da ya kafa majalisar ministocinsa domin tafiyar da gwamnati, kuma ƙasa da wata guda bayan Shugaba Macron ya naɗa shi a kujerar. A jiya Lahadi ne ya sanar da sunayen mambobin sabuwar majalisar ministocinsa inda ya naɗa sabbin muƙamai, amma ya bar wasu da dama a kan kujerunsu, lamarin da bai yi wa ’yan adawa daɗi ba. Zargin takardun bogi: Jami’ar Nsukka ba ta taɓa ba ni takardar digiri ba — Minista ’Yan bindiga sun kashe...
Gwarzuwar gasr Big Brother Naija (BBNaija) ta wannan shekara, Imisi Eniola Ayanwalwe, ta ce ba ta san yadda za ta kashe Naira miliyan 150 da ta lashe a gasar ba. Imisi Eniola Ayanwale ce ta zama gwarzuwar BBNaija da aka kammala a daren Lahadi ne bayan kwanaki 70 ana fafatawa mai cike da ce-ce-ku-ce da nishaɗi. An sanar da sakamakon tare da karrama ta da kyaututtuka ne a babban bikin ƙarshe da Ebuka Obi-Uchendu ya gabatar, inda Imisi ta doke abokiyar takararta Dede a karshe. Ta tafi da tsabar kuɗi Naira miliyan 80 a matsayin wani ɓangare na kayatattun Naira miliyan 150 da ta lashe a matsayin gwarzuwar BBNaija karo na 10. A bana, masu shirya gasar sun canja tsarin...
Ana tsaka da Sallah ’yan bindiga suka karbe wani mutum har lahira sa’annan suka yi garkuwa da basarake a ƙauyen Rani Ramat da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara. Al’ummar yankin sun ce maharan sun kai farmaki ne a kan babura a yayin da ake Sallar Magariba ranar Lahadi inda suka rika harbi babu ƙaƙƙautawa. A yayin da jama’a ke guje-gujen neman tsira ne ’yan bindigar suka harbe wani mutum. Daga nan suka yi awon gaba da basaraken ƙauyen mai suna Alhaji Ndako, zuwa inda ba a sani ba. Mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka kafin su koma cikin daji. Kwamitin gwamnati ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13...
Kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin nazarin buƙatun ƙirƙirar sababbin masarautu da yankunan hakimai da dagattai, ya ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, da hakimai 2 da dagattai 113 a fadin jihar. Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya miƙa wa Gwamna Bala Mohammed a ofishinsa da ke Bauchi. Da yake miƙa rahoton, Akuyam ya bayyana cewa masarautu 13 da yankunan hakimai biyu da aka bayar da shawarar kafa su su ne suka cancanta daga cikin sama da buƙatu 100 da aka karɓa daga sassan jihar daban-daban. Kwamitin, an kaddamar da shi ne a ranar 4 ga Yuli 2025, da umarnin ya duba buƙatun al’ummomi, ya tantance dalilan tarihi, al’ada da...
A cewar Sakataren Zartarwa na Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna, Ibrahim Balarabe, yace sabon rukuni na biyan kudi zai amfanar da tsofaffin ma’aikata 661 da iyalan waɗanda suka rasu a matakan Gwamnatin Jiha da ta Kananan Hukumomi naira biliyan 1.736 za a biya ga tsofaffin ma’aikata 511 karkashin tsarin ( CPS) sannan kuma naira miliyan 585 za a biya ga tsofaffin ma’aikata 315 da iyalan mamata karkashin tsarin (DBS). Hukumar ta bayyana cewa, ga waɗanda ke karkashin fanshon hadin gwiwa na (CPS), hakkokin su za a tura kai tsaye cikin asusun fansho (Retirement Savings Accounts – RSAs) ɗin su, yayin da waɗanda ke karkashin tsarin (DBS) za a gayyace su nan gaba don yin tantancewa kafin a biya...
Iran ta sanar cewa tana goyon bayan “duk wani shiri” da zai ba da damar samar da ‘yancin kai ga al’ummar Falasdinu, gabanin tattaunawa da ake shirin farawa a Masar tsakanin Isra’ila da Hamas da nufin kawo karshen yakin zirin Gaza. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, iran ta ce “a ko da yaushe tana goyon bayan duk wani yunkuri na kawo karshen laifukan yaki, da cin zarafin bil’adama a Gaza da duk wani yunkuri na share fagen tabbatar da ‘yancin kai na al’ummar Palasdinu.” Sanarwar ta ce, tilas ne yanke duk wata shawara kan tsagaita bude wuta ko sasantawa ta siyasa ta rataya a wuyan Falasdinawa da kansu. Tehran ta ce tana maraba da...
Babban mai shiga tsakani na kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas Khalil Al-Hayya ya isa Masar, inda ya jagoranci tawagar da ake sa ran za ta fara tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Isra’ila, a cewar kungiyar. Hamas ta ce za a fara tattaunawar ce kan “hanyoyin tsagaita bude wuta, da janye sojojin mamaya, da musayar fursunoni.” yau Litinin ne aka tsara tawagar Isra’ila za ta isa wurin, kamar yadda ofishin Benjamin Netanyahu ya bayyana, a wani bangare na tattaunawar. Su ma wakilan Amurka, Masar da kuma Qatar zasu halarci tattaunawar a matsayinsu na masu shiga tsakani. A cewar majiyoyin diflomasiyya, tattaunawar tsakanin Isra’ila da Falasdinawa za ta gudana ne a birnin Sharm el-Sheikh. Ana sa ran tattaunawar za...

Yawan Mutanen Da Suka Yi Zirga-zirga A Rabin Farkon Hutun Bikin Kafuwar PRC Da Bikin Zhongqiu Ya Kai Biliyan 1 Da Miliyan 243
Bisa labarin da ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a kasar Sin ya kai miliyan 301 da dubu 291 da dari 1, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan mutanen da suka yi zirga-zirga a rabin farko na hutun bikin kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin PRC da bikin Zhongqiu ya kai matsayin koli a tarihi, wato ya kai biliyan 1 da miliyan 243, wannan ya shaida cewa, an fi yin zirga-zirga a lokacin hutun. Game da hanyoyin zirga-zirga a lokacin wannan hutu, an fi zabar hanyoyin mota. Game da yankunan da aka fi sha’awar ziyarta, an...
A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a yau Lahadi da samun galabar Iran. Tun da fari kungiyar kwallon ragar ta Iran ta sami nasarori har sau uku a jere, da a karshe ta kai ga samun nasara akan mai masaukin baki kasar Uzbakestan. Mai bayar da horo ga ‘yan wasan Li Du Hi, ta bayyana jin dadinsa da nasarar da su ka samu, musamman saboda wannan ne karon farko aka sami wannan...
Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan yahudawan kudin da sun kai Shakel miliyan 25 wanda shi ne kwatankwacin Dala miliyan 7.54, ta hannun lauyoyinsu. Haka nan kuma jaridar ta ce hukumar dake kula da haraji da ke karkahsin ma’aikatar shari’a ce ta aiwatar da raba kudin a matsayin abinda su ka kira diyyar ayyukan t’addanci.! Jaridar ta kuma ce tun a 2019 ne wadannan ‘yan sahayonioyar su ka bukaci a biya...
Wasu da ake zargin ’yan fashin daji ne sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin maharba a yankin Gangara da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a yau Asabar, 4 ga watan Oktoba, 2025, inda aka tabbatar da mutuwar Malam Kabiru, wanda yake ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar maharba ta ƙasa, reshen Giwa. Hukuma ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da N4bn a Kano An yi wata gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai Rahoto ya bayyana cewa Malam Kabiru ya rasu ne yayin aikin ceto wasu mutane da ’yan fashi suka sace daga yankin Danja na Jihar Katsina. Shugaban ƙungiyar maharba ta ƙasa, Kwamanda Usman Taju, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, jim kaɗan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp