2025-11-03@07:44:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4442

«Afrika ta Yamma»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce.   Shin ko sauya hafsoshin tsaro zai kawo karshen fargaban da al’umma ke yi? NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai. Domin sauke shirin, latsa nan
    A ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1945, wato bayan da kasar Sin ta samu nasara a yakin kin harin mayakan Japan, kasar ta Sin ta karbi yankin Taiwan daga hannun Japanawa da suka yi rabin karni suna mamayar yankin, inda suke aiwatar da mulkin mallaka. Sa’an nan zuwa ranar 25 ga watan Oktoban bana, babban yankin kasar Sin ya gudanar da biki na musamman don tunawa da dawowar yankin Taiwan cikin harabar kasar. Dangane da batun, dimbin kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suna ganin cewa, bikin da aka shirya ya nuna nasarar da Sinawa suka samu a yakin duniya na biyu, kana ya shaida cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wanda ba za a iya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing October 26, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai October 26, 2025 Daga Birnin Sin Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya October 26, 2025
    Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin tafiya kasar Koriya ta Kudu, domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabanni karo na 32, na kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar, an gudanar da wani taron tattaunawa, mai taken “Shugabancin duniya da samun wadata tare a yankin Asiya da Pasifik” a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da jami’ar Yonsei  da gidan talabijin na YTN na Koriya ta Kudu suka shirya tare.   Yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce “CMG na fatan yin hadin gwiwa mai zurfi tare da kasashen yankin...
    A Ivory Coastana ci gaba da kirga kuri’u bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Asabar. An kira sama da masu jefa kuri’a miliyan 8 zuwa rumfunan zabe a rumfunan zabe sama da 25,000 a fadin kasar. A kasar da ta fuskanci mummunan yakin basasa, zaman lafiya yana daya daga cikin manyan abubuwan da jama’a ke fata. ‘Yan takara biyar ne suka fafata a wannan zaben, ciki har da Alassane Ouattara, mai shekara 83 wanda ke neman wa’adi na hudu. Duk da cewa an cire shugabannin ‘yan adawa daga zaben, masu lura da al’amura sun yi imanin cewa shugaban da ke kan mulki ba tantama zai iya lashe zaben. A ranar Asabar da yamma, shugaban hukumar zaben kasar...
      Masu sharhi na wasanni sun bayyana cewa wasan na yau zai kasance mai cike da fasaha da kwarewa, musamman ganin cewa kungiyoyin biyu na da ‘yan wasa matasa masu zafin guiwa kamar Vinicius Jr., Jude Bellingham, da Lamine Yamal, wadanda ke son rubuta sunayensu cikin jerin manyan taurarin da suka taba buga El Classico. Dukkan idanu yanzu sun karkata zuwa Madrid, inda ake jiran ganin wanda zai yi nasara a wannan karon. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025 Wasanni Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya...
    Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru 40, ba kawai magana ce ta fafutuka ba, har ila yau kalubale ne ga shugabanni.   Matakin Dasuki ya kasance wani muhimmin lamari a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ’yan siyasa kalilan ke ja da baya daga mukaman su. Sanarwar sa an fassara ta sosai a matsayin wakilcin  gwagwarmayar adalci tsakanin tsararraki wanda ya taimaka wajen jagoranta, wanda ke nufin rage gibin da ke tsakanin tsofaffi...
    Waɗannan matsalolin, sun sanya ake yin jigilar  kayan ta kan hanya, a manyan motoci, wanda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a fannin ke ci gaba da kokawa, saboda kuɗaɗen da suke kashewa masu yawa, wajen jigilar kayansu wanda hakan ya saɓawa manufar ta kafa Tashodhin  Jiragen Ruwan ta kantudu. Injiniya Kayode Opeifa Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa na ƙasa ya tabbatar da waɗannan matsalolin a taron 2025 Ƙungiyar ‘Yan Jarida Wakilai  da ke ɗauko rahotannin ɓangaren sufuri TCAN, da aka gudanar a jihar Legas. A cewar Kayode, ƙalubalen rashin tsaro, a jihar Neja, hakan ya tilasta Hukumar dakatar da jigilar kayan ta hanyar amfani da Jirgin ƙasa zuwa Kaduna. Sai dai ya bayyana cewa gwamnonin jihohin...
    Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fadawa shugaban Amurka Trump cewa ya ci gaba da rayuwar cikin mafarkinsa! A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra’ila ta “Knesset”, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma kalmomi biyu kacal da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Iran, Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya furta sun isa su zame a matsayinsa mayar da martani. Ya zo cikin Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa: Alfaharin Shugaban Amurka cewa: “Hakika sun yi luguden wuta kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran tare da ruguza su, tabbas wannan da’awa ce kawai, amma Amurkawa su ci gaba da rayuwa cikin wannan ruɗunsu!” Martani mai ƙarfi...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Sakon wasikar da Iran, Rasha, da China suka aika ga Majalisar Dinkin Duniya alama ce ta hadin kai Shugaban Majalisar shawarar Musuluncin ya bayyana wasiƙar da ma’aikatun harkokin waje na Iran, Rasha, da China suka aika wa Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin tsaro a matsayin wata alama ta haɗin kai mai mahimmanci tsakanin waɗannan ƙasashe uku, yana mai cewa, “Da karewar kuduri mai lamba 2231, wa’adin Darakta Janar na IAEA na tabbatarwa da sa ido kan aiwatar da shirin makamashin nukiliya na Iran ya ƙare.” Mohammad Baqer Qalibaf ya ce a wani zaman jama’a na Majalisar Shawarar Musulunci a ranar (26 ga Oktoba) da kuma a jawabinsa ga Majalisar ya bayyana...
    Memba a Majalisar Tarayyar Turai ya bayyana cewa: Zaman lafiya na gaske yana buƙatar ɗaukar matakin hukunta Isra’ila Dan Majalisar Dokokin Turai ta Ireland (MEP) Barry Andrews ya jaddada cewa: Daukan matakin hukunta haramtacciyar kasar Isra’ila kan munanan laifukan da ta aikata a Zirin Gaza ita ce hanya daya tilo da za a cimma zaman lafiya na gaskiya da dorewa, yana mai kira ga Tarayyar Turai da ta ci gaba da zabar sanya takunkumi kan Isra’ila. Jawabin Andrews ya zo ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu na kasar Turkiyya, wanda ya yi daidai da taron Tarayyar Turai da aka gudanar a Brussels ranar Alhamis da ta gabata, wanda ya tattauna makomar dangantakar Tarayyar Turai da Isra’ila...
    “Yayin da ake gudanar da samamen bisa ga bayanan sirri daga wasu mazauna garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Shanono, jami’an hadin gwiwa na rundunar yaki da ta’addanci ta rundunar da kuma jami’an rundunar da ke Shanono, sun gudanar da samamen na kwarewa a ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 02:00 na dare. Hakan ta sa, an samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne,” in ji sanarwar.   Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Farin Ruwa, yana mai bayyana yadda suka bayar da bayanan sirrin a matsayin muhimmin abu ga nasarar aikin. Ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani...
    Wani rahoto na kafar watsa labarun Birtaniya ya bayyana cewa; Da akwai fiye da fursunoni 90 da suke yajin cin abinci a gidan kurkukun kasar Bahrain suna neman a sake su. Rahoton ya kuma ce, mafi yawancin fursunonin da suke yajin cin abincin suna babban gidan yarin kasar ne, kuma an kama su da yi musu hukunci ne bisa dalilai na siyasa. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da fursunoni a kasar Bahrain suke yajin cin abinci bisa nema a kyautata yanayin rayuwarsu a inda ake tsare da su, ko kuma neman a sake su ba tare da wani sharadi ba. Wani sauti na daya daga cikin fursunonin da aka dano daga cikin gidan kurkuku, ya bayyana cewa;...
    Kafar watsa labaru ta “Afircanews” ta bayyana cewa, babu wani cikakken dalili da aka gabatar dangane da sauye-sauyen, tare da kuma kore jita-jitar da aka rika watsawa akan yunkurin juyin Mulki a kasar a watan Satumba, dda ya kai ga tsare sojoji 20 daga ciki har da Birgediya janar da kuma kanar. Mai Magana da yawun shugaban kasar ta Nigeria, ya bayyana cewa; shugaba Ahamd Tinubu ya salami manyan jami’an sojoji da su ka hada babban hafsan hafsoshi Emmanuel Ogalla, shugaban sojan ruwa, da Hassan Abubakar, shugaban sojan sama. Shugaba Ahmad Tinubu ya nada Olufemi Oluyedi, tsohon hafsan hafsoshin soja a matsayin sabon ministan tsaro.  Sabon shugaban sojan kasa shi ne Manjo janar W. Shaibu Shugaban sojan Sama kuma shi...
    A yau Asabar 25 ga wannan wata, ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar sun gudanar da liyafar murnar kebe ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, a dakin taro na Diaoyutai dake birnin Beijing. Wakilan bangarori daban daban na yankin Taiwan da na babban yankin kasar Sin masu halartar bikin murnar cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan da safiyar wannan rana sun halarci liyafar. Direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar...
    Jami’ar Tarayya ta Dutsinma ta zabi Farfesa Muhammed Khalid Othman a matsayin sabon Shugaban Jami’ar na dindindin, tare da amincewar Majalisar Gudanarwar Jami’ar. Da yake zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, Magatakardar Jami’ar, Dokta Musa Ajiya, ya bayyana cewa mai kula da jami’ar (Pro-Chancellor), Ali Abubakar-Jatau, ne ya sanar da nadin. A cewar Dokta Ajiya, Abubakar Jatau wanda shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa, ya bayyana hakan ne bayan taron na musamman karo na 36 da aka gudanar a daren Juma’a. Ya ce Farfesa Othman ya fito ne a matsayin wanda ya fi kowa cancanta bayan wani tsari na tantancewa mai tsauri kuma bisa gaskiya, a cikin mutane 17  da suka nemi mukamin 17. Ya ƙara da...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa Singapore a yau Asabar don ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar firaministan Singapore Lawrence Wong. Li ya bayyana cewa, a cikin shekaru 35 da suka gabata tun bayan kafa huldar diflomasiyya, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da kasancewa mai kyau da samun ci gaba, tare da zurfafa amincewa da juna a siyasance, da hadin gwiwa mai amfani da kuma mu’amala ta kut-da-kut tsakanin mutanensu, wanda ya kafa misali don koyo tare da hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare a tsakanin kasashe. Ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin aiki tare da Singapore don karfafa daidaita dabarun ci gaba, da fadada hadin gwiwa mai amfani ga dukkan...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15 October 25, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC October 25, 2025
    A yau Asabar al’ummar kasar Ivory Coast ke zaben shugaban kasa wanda ya raba kan kasar inda wasu ke son shugaba Alassane Ouattara ya yi tazarce, wasu kuma na ganin lokaci ne na samar da sabon shugabanci a kasar. Fargaba ta karu sosai tun bayan cire manyan ‘yan takara biyu na jam’iyyun hamayya – wato tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da Tidjane Thiam, wani kusa a fagen siyasa kuma abokin kawancen Ouattara kafin ya zama abokin hamayya. Rahotanni sun ce Shugaba Ouattara ya yi kira ga magoya bayansa su fito su zabe shi duk da yan kasar da dama na tunanin shi zai lashe zaben,  kafin zaben an samu rikici a sassan kasar da dama inda aka kama daruruwan mutane...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15 October 25, 2025 Daga Birnin Sin An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC October 25, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take October 24, 2025
    “Muna godiya ga sadaukarwar da sojoji da hukumomin tsaro ke yi. Wannan wasa tsakanin tsoffin ’yan wasan Barcelona da tsoffin ’yan wasan Afirka shaida ce ta nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu wajen dawo da zaman lafiya,” in ji shi. Tsoffin ’yan wasan Barcelona sun isa Nijeriya domin buga wasa da tsoffin ’yan wasan Afirka a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba, 2025. Yayin da Matawalle ke tarbarsu a ofishinsa, ya miƙa saƙon maraba da fatan alheri ga tawagar a madadin Gwamnatin Tarayya da al’ummar Nijeriya, inda ya yi musu fatanalheri. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Bai kamata a yi mummunan amfani da kwamitin tsaron ba ko kuma a yi amfani da shi don dalilai na siyasa Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya bayyana cewa: An gwada Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya sosai ta hanyar ayyukan ta’addanci da kuma amfani da dabarunta na siyasa. Ya ce: “Dole ne kwamitin tsaro ya cika nauyin da ke kansa da mutunci, inganci, kuma ba tare da son kai ba. Babu wani memba, komai karfi da zai iya amfani da wannan cibiyar ba bisa ka’ida ba ko kuma ya yi amfani da shi don dalilai na siyasa ko na bangare guda.” A jawabinsa a Majalisar...
    Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Yaƙin da aka ɗora wa Iran ya canza daidaiton da ke tsakanin Sahayonayya da Amurka Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Hussein Ta’ib, ya ce: Yaƙin kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyya ta ɗora wa Iran, ba wai kawai bai cimma komai ga Isra’ila ba ne, har ma ya canza daidaiton dabarun Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila gaba ɗaya. A lokacin taron tattaunawa na 31 na ƙungiyar Jaruman Musulunci a Qom, Hussein Ta’ib ya ce: “Dakarun kare juyin juya halin Musulunci da sojojin Iran sun kalubalanci masu girman kai inda suka kai wani mataki cikin saurin na zarce lissafin...
    Shugaban kasar Venezuela yayi tsokaci kan matakin sojin Amurka yana mai cewa Amurka tana son ƙirƙiro yaƙi a yankin Shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya zargi Amurka da yunkurin tayar da sabon yaki a kan kasarsa, bayan rahotannin da ke cewa; Amurka na gudanar da shirin soja na kai hari kan wuraren samar da hodar iblis a Venezuela. Maduro ya ce a cikin wani jawabi da ya gabatar ta gidan talabijin: “Suna kirkirar yaki ne domin tabbatar da ta’addancin da suke yi wa Venezuela… Suna son mayar da batun miyagun kwayoyi ya zama hujjar sabon mamayar sojoji a Latin Amurka.” Ya kara da cewa gwamnatinsa “ba za ta bari wani karfi na kasashen waje ya keta ikon Venezuela ba,” yana...
    Mazauna unguwar Tudun Wada da ke garin Shendam a Jihar Filato sun zargi wasu jami’an ’yan sanda da ba wa ’yan daba kariya wajen rusa gidajensu. Shaidu sun ce sama da ’yan sanda 100 ɗauke da makamai ne suka isa yankin da misalin karfe 5 na safiyar Laraba, suka ba wa wasu ’yan daba kariya yayin da suke lalata gine-ginen jama’a Lamarin ya jawo zanga-zangar da mazauna yankin, ciki har da mata da yara, suka gudanar don nuna adawa da abin da suka kira “cin zarafi daga jami’an tsaro.” Mazaunan sun bayyana cewa rushewar gidajen ta faru ne da haɗin gwiwar iyalan Fuanter duk da cewa ana shari’a a gaban kotun ɗaukaka ƙara kan mallakar filayen. Sun ce suna da...
    Rashin Biyan Yan-fansho Bisa Lokaci Ta tabbata a lokacin mulkin Kwankwaso, “yan fansho a Kano, kan jira tsawon Watanni zuwa Shekaru ba tare da an biya su hakkokinsu na barin aiki ba. Haka ɗan-jummai Ganduje, yakan dan fara biyan hakkokin “yan fanshon, sai kuma a ga ya watsar. Sai a dauki tsawon lokaci yana ɓaɓatun za a ci gaba da biya, amma sai a ji shiru. Sai aka wayi gari karɓar fansho, musamman giratuti, ya zama tamkar tafiya Lahira, yau ne? Gobe ne? Babu wata cikakkiyar amsa!. Haƙiƙa kwata-kwata babu tausai, mutane sun kwashe akasarin Shekarunsu na haihuwa suna masu hidimtawa ƙasa dare da rana, cikin yanayi na sanyi, ruwan sama da garjin rana, dole ne su fito, su aje...
    Shugaba Gustavo Petro ya ce, ba wai kawai ba ya wata mu’amala ta kasuwanci da Amurka ba ne, ba shi ma da koda dala kwaya daya a cikin wani asusu na bankunan Amurkan balle a ce an rufe shi. Gustavo ya kara da cewa; ko kadan ba zai taba rusunawa a gaban Amurka ba, ba kuma zai ja da baya ba. A jiya Juma’a da marece ne dai Baitulmalin Amurka ya sanar da kakaba wa shugaban kasar ta Columbia takunkumi. Gustavo ya kuma ci gaba da cewa; Yadda yake fada da yaduwar muggan kwayoyi na shekaru masu tsawo, shi ne ya sa Amurkan ta dauki wannan irin matakin akansa alhali kasarsa Columbia tana taimakawa wajen hana Amurkawan shan hodar Iblis....
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa October 24, 2025 Daga Birnin Sin An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan October 24, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Jagoranci Zaman Jin Ra’ayoyin Wadanda Ba ‘Yan JKS Ba Game Da Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15  October 24, 2025
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Jigawa 774, inda ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa na yaki da rashin abinci mai gina jiki da inganta yalwar abinci a fadin jihar. An gudanar da kaddamarwar ne yayin ziyarar Mrs. Uju Rochas-Anwuka, mai bai wa Shugaban Kasa shawara ta musamman kan lafiya ( Karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), wacce ta je Jigawa domin kaddamar da shirin Nutrition 774 da ke karkashin shirin sabunta kudurori na Renewed Hope Agenda. Gwamna Namadi ya bayyana cewa Jigawa ta kasance gaba a yaki da matsalar, tare da kafa shiri na musamman da aka yi wa lakabi da Masaki tun a 2020 domin fadakar da al’umma a...
    Limamin da ya jagoranci sallar juma’ar birnin Tehran ya bayyana cewa: Shugaban Amurka Trump ɗan ta’adda ne kuma mai fafutukar yada ayyukan ta’addanci Limamin da ya jagoranci sallar Juma’ar birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyed Ahmad Khatami, ya yi magana game da laifukan Amurka a cikin hudubarsa, yana mai cewa: Shugaba Trump ɗan ta’adda ne kuma mai haɓaka ayyukan ta’addanci a duniya. Ayatullah Khatami ya yi tambayar cewa: “Wa ya kashe shahidin Iran Qasim Sulaimani? Ba Amurkawa ba ne suka kashe shahidi Tehranchi ba, kuma suka kashe shahidi Abbasi. Hakika Amurka ce ‘yar ta’adda kuma mai haɓaka ayyukan ta’addanci. Wa ya ƙirƙiri kungiyar ta’addanci ta ISIS? Saboda haka, ikirarin Amurka na cewa tana son yaƙi da...
    Shugaban kasar Amurka Trump ya ce: Za su dauki matakin soji kan kasar Venezuela nan ba da jimawa ba Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da cewa kasarsa za ta iya fara yaki da “masu safarar miyagun kwayoyi nan ba da jimawa ba,” yana mai cewa, “Za su dauki mataki ta hanyar kutsawa ta kasa a kasar Venezuela,” yana mai nuni da yiwuwar shiga tsakani na soja ko ayyukan leken asiri. A martanin da ya mayar, Shugaba Trump daga baya ya musanta rahotannin cewa: Jiragen yakin Amurka sun yi shawagi a kusa da kan iyakar Venezuela, yana mai jaddada cewa: “Ba gaskiya ba ne cewa: Amurka ta aika da jiragen yakin sama kusa da Venezuela.” Trump ya shaida wa...
    Gwamnatin kasar Iraki ta yi Allah wadai da matakin da Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta dauka na mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da kuma gine-gine matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iraki ta bayyana Allah wadai da amincewa da kudurorin biyu na Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta yi da su da nufin sanya kwace iko da mallakar yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gudanar da matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba. Ma’aikatar ta ce a cikin wata sanarwa cewa: “Tana bayyana kakkausar suka da Iraki ta yi kan amincewar da Majalisar Dokokin Isra’ila ta yi da kudurorin biyu da nufin kwace iko da mallake yankin Yammacin...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya jagoranci wani taron karawa juna sani a ranar 27 ga watan Augusta, domin jin ra’ayoyin wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba, dangane da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar game da tsara shirin raya kasa na shekaru 5 karo na 15, da ke da nufin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. (Fa’iza Muhammad Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugaban Kasar Sin Zai Halarci Taron APEC Da Ziyarar Aiki A Korea Ta Kudu October 24, 2025 Daga Birnin Sin Fahimtar Sabon Tunani: Samar Da Wadata Ga Dukkan Jama’a Ta Daidaita Gibin Dake Tsakanin Hamshakai Da...
    Hammayo ya shawarce shi da ya gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci tare da haɗa kan ƙabilu don tabbatar da zaman lafiya. A baya-bayan nan ne Gwamna Bala Mohammed ya rattaba hannu kan dokar kafa sabbin masarautu 13 a jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya October 24, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu October 24, 2025
    Rundunar ’yan sanda ta kama wani matashi ɗan shekara 29, mai suna Abubakar Isah Mokwa ɗalibi da yake karatun digiri na biyu a tsangayar Tattalin Arziki na Noma a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja. An kama ɗalibin ne bisa zarginsa da sukar Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago. Rahotanni sun ce an an kama Abubakar Mokwa ne a wajen harabar jami’ar da yake da masauki a Lapai a ranar Alhamis bayan wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya caccaki gwamnan kan rashin aikin yi. ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu...
    Shugaba Tinubu, ya gode wa tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da sauran tsoffin hafsoshin bisa gudunmawar da suka bayar. Ya kuma bukaci sabbin hafsoshin da su tabbatar sun cancanci nadin da aka musu ta hanyar nuna ƙwarewa, haɗin kai wajen tsaron Nijeriya. “Shugaban ƙasa ya bukaci sabbin hafsoshin tsaro da su tabbatar da cewa sun cancanci nadin da aka musu ta hanyar nuna ƙwarewa, faɗakarwa, da zumunci wajen tsaron ƙasa,” in ji sanarwar. Sanarwar ta bayyana cewa dukkanin sabbin naɗin za su fara aiki nan take. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi October 24, 2025 Labarai Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule October 24, 2025...
    ’Yan Sanda sun sake kama dan gwagwarmaya kuma mamallakin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, bayan wata kotun Majistare da ke Abuja, ta bayar da belinsa.  An sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa tare da wasu mutum 12 a ranar Juma’a. Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike Alƙalin kotun, Abubakar Sai’id ne, ya bayar da belin Sowore da wasu mutum 12 da aka tuhuma da tayar da hankalin jama’a, sakamakon zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin. Lauyan Sowore, Tope Temokun, ya zargi ’yan sanda da yin amfani da karfi, inda suka yi awin gaba ba tare da wani bayani ba....
    Mahaifin Rukayya, Muhammad Adamu mazaunin ƙauyen Bayan Dutse da ke Wailo, a gundumar Kubi cikin ƙaramar hukumar Ganjuwa a ranar 17 ga watan Oktoba ya kai rahoton caji ofis ɗin Soro ya ke shaida cewar wani matashi mai suna Auwal Dahiru mai shekara 17, ya kai farmaƙi wa yarsa da ƙoƙarin kasheta da kwaƙule mata idanuwanta.  Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil a ranar Litinin, ya ce, lokacin da ‘yansanda suka samu rahoton faruwar lamarin cikin gaggawa a ƙarƙashin Baturen ɗansanda da ke kula da caji ofis ɗin Soro, CSP Aliyu Mohammad Goni, sun kai agaji inda lamarin ya faru. A lokacin da aka ɗauki Rukayya zuwa asibitin koyarwa na...
    Kafin ya zama gwamna, ya kasance Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, inda ya yi ƙaurin suna wajen yin adalci, kwanciyar hankali da kuma zurfin fahimtar shugabanci. Wannan gogewa ta aikin doka, ta zama ginshiƙin nasararsa na gudanarwa. Kazalika,ya ba shi damar daidaita hangen nesa da tuntuɓa tare da yin taka- tsan-tsan wajen aiwatar da ayyukansa. Ajandarsa Ta “MORE Agenda” Ajandarsa ta ayyukan da yake ƙuzun aiwatarwa, ƙarƙashin “MORE Agenda”, Gwamna Oboreɓwori, ba wai kawai taken ba ne; tsari ne na aiki wanda ya ƙunshi kowane ɓangare na ayyukan da son aiwatarwa ƙarƙashin mulkinsa A Ƙarƙashin Jagorancinsa: An kammala ayyukan tituna sama da 513 da suka shafe kusan kilomita 1,500, ban da kuma waɗanda ake kan ci gaba da gudanarwa a...
    ‘Yan sandan kasar Ghana sun sanar da cewa tserato da wasu ‘yan Najeriya 57 da aka yi faskwaurinsu, haka nan kuma wasu mutane 5 da suke aikata laifuka ta hanyar sadarwar na “Internet” Jami’an ‘yan sandan sun kwace nau’ra mai kwakwalwa 77 da wayoyin hannu 38, sai kuma wasu motoci 2, akwatin talbijin 3, da kuma wasu na’urori da suke amfani da su a yaudarar mutane. A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an ‘yan sandan kasar ta Ghana su ka sanar da kai farmakin a birnin Accra a ranar Laraba 22 ga watan nan na Oktoba. Shekarun mutanen da ake amfani da su wajen yaudarar mutane ta hanyar internet suna a tsakanin 18 zuwa 26,tuni kuma an kai su...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da kawi karshen tattaunawa da kasar Canada dangane da batun kasuwanci Shugabann a kasar Amurka ya  zargi Canada da yin amfani da kalmomin tsohon shugaban kasar Amurka Ronald Regan ta hanayar da ba ta dace ba a cikin wasu tallace-tallace akan kudaden fito, inda ya bayyana cewa; ” Saboda  la’akari da halayyarsu an kawo karshen tattaunawar kasuwanci da kasar Canada.” Shugaban kasar na Amurka ya ci gaba da cewa; Cibiyar Ronald Ragan ta sanar da cea, Canada ta murguda zancen Regan yana Magana akan illolin kudin fito, kuma an yi hakan ne domin yin tasiri a cikin matakin da kotun koli ta Amurka za ta dauka akan batun da ake jiran ta fitar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala October 24, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu October 24, 2025
    “Shirin gwamnan na aiwatar da sabon tsarin albashi duk da ƙalubalen tattalin arziki ya nuna tausayinsa, gaskiya, da girmama kimar ma’aikata,” in ji shugabannin kungiyoyin.   Kungiyoyin sun kuma yaba da kokarin gwamnatin wajen gyara da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya inda suka bayyana gyaran da sabunta azuzuwan karatu a dukkan kananan hukumomi 23, amincewa da tsarin ritaya bayan shekaru 65 ko shekaru 40 na aiki ga malamai, da kuma dawo da sama da naira miliyan 500 na ajiyar ( ENDWELL) da aka rike a baya, a matsayin muhimman nasarori.   Ma’aikatan sun kara jinjina wa dawowar tsarin biyan gudunmawar adashin gata na malaman makaranta wato (ENDWELL) na kowane wata, inda suka bayyana cewa tsarin yana taimakawa wajen inganta...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ƙara zuba jari a manyan cibiyoyin ilimi domin shirya ɗalibai su zama masu iya fafatawa a matakin duniya. Shugaban Ƙasan ya bayyana hakan ne a yayin bikin karrama masu kammala karatu na shekara ta 40 na Jami’ar Ilorin (UNILORIN) da ke Ilorin, Jihar Kwara. A jawabinsa, wanda Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya Akure (FUTA), Farfesa Temidayo Oladiji, ya karanta a madadinsa, Shugaba Tinubu ya yi alkawarin ƙarfafa ƙirƙira, bincike, da ilimin da ke gina ƙwarewa (skill-based education) a dukkan jami’o’in Najeriya. Ya yaba wa jami’ar bisa tsayin daka da ladabi da kuma ingancin ilimi da ta dade tana nunawa tun daga kafuwarta. Shugaban Ƙasan ya kuma sanar da cewa Jami’ar...
    Shirin karfafa ilimin ‘ya’ya mata a jihar Kano ya shirya taron tattaunawa da malamai da limaman masallatan Juma’a domin ƙarfafa haɗin gwiwa da shugabannin addini wajen inganta goyon bayan al’umma ga ilimin ’yan mata a fadin jihar. Taron, wanda yake ɗaya daga cikin dabarun haɗin kai na masu ruwa da tsaki na AGILE, yana da nufin ƙara samun damar karatu, tsayawa da kuma kammala karatun ’yan mata ta hanyar daidaita ayyukan shirin da dabi’u da imanin al’umma. A jawabinsa, Shugaban Shirin AGILE na Jihar Kano, Malam Mujtapha Aminu, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin fayyace wasu rashin fahimta da ake da su game da shirin, da kuma tabbatar da fahimtar juna tsakanin shugabannin addini. A cewarsa, “Shigar malamai...
    Sakatare-Janar na kwamitin hadin gwiwa na yankin Gulf Jassim Al-Badawi  ya yi kakkausar suka kan amincewa da wasu kudirori guda biyu a majalisar Knesset ta Isra’ila da ke da nufin kakaba ikon Isra’ila kan yankin yammacin kogin Jordan da ta mamaye. A rahoton talabijin ta Aljazeera, Jassim Al-Badawi a cikin wata sanarwa a jiya Alhamis ya jaddada cewa, matakin da majalisar Knesset ta Isra’ila ta dauka, wani mataki ne da ya saba wa kudurorin kasa da kasa, da kuma kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi na samun zaman lafiya mai dorewa. Haka nan kuma ya jaddada cewa ayyukan gina matsugunan da gwamnatin sahyoniyawan suke yi a fili take ga hakkokin tarihi na al’ummar Palastinu da dokokin kasa...
    Wasu daga cikin sojojin sun ji rauni amma suna cikin ƙoshin lafiya. Haka kuma, wasu gine-gine da motocin da ke kusa sansaninin sun lalace yayin artabun. Rundunar sojin ta yaba da jarumtar dakarunta, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare ƙasar daga duk wata barazana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 23, 2025 Manyan Labarai Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025
    Fadar mulkin kasar Rasha Krimlne ta sanar da cewa, shugaban kasar Valdmir Putin ne ya sa ido akan yadda rundunar dake kula da makaman Nukiliya ta gudanar da rawar daji a sansnain “Blisitiks”. Sanarwar ta kara da cewa, rundunar dake kula da muhimman makakan Nukiliyar kasar ta Rasha  ta yi amfani da makamai masu linzami samfurori mabanbanta. Haka nan kuma fadar gwamnatin Rashan ta ce, an gudanar da  dukkanin gwaje-gwajen cikin nasara, an kuma yi ne domin tabbatar da cewa rundunar tana cikin shirin ko-ta-kwana. A wani labari mai alaka da Rasha, ma’aikatar harkokin waje ta gargadi kasashen turai akan kokarin bai wa Ukiraniya kudadenta da suke a cikin bankunansu. MA’aikatar harkokin wajen Rasha ya fadawa kasashen turai din cewa...
    An tsara cewa a cikin wannan makon da aka shiga ne dai za a gana a tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha domin share fagen ganawar shugabannin kasashen biyu. Fadar mulkin Amurka “ White House” ta bayyana cewa an yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin ministocin harkokin wajen Amurka da Marco Rubio da Sergey Lavrov a shekaran jiya inda su ka cimma matsaya akan cewa, ganawar ba ta zama dole ba. A makon da ya shude ne dai shugabannin kasashen Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin su ka yi ttataunawa ta wayar tarho, inda su ka cimma matsaya akan ganawa a birnin Budaphast na kasar Bulgaria. A cikin watan Ogusta na wannan shekarar an...
    Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran wanda ya gana da tawagar masu shirya taron tunawa da Alamah Mirzai Na’ini ( R.A), ya ce; muhimman siffofi biyu da malamin ya kebanta da su, su ne kirkira a fagen ilimi da kuma a cikin ilimin siyasa. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana Allamah Na’ini a matsayin daya daga cikin fitattun malamai, masu tarin sani a cikin jami’ar Najaf mai tsohon tarihi; jagoran juyin na Iran ya yi ishara da yadda marigayin malamin ya samar da ka’idojin da aka gina ilimin usulu akansu, wanda ya kai ga sabunta shi. Daga cikin rukunonin tunanin Allamah Na’ini kamar yadda jagoran juyin ya ambata da akwai batun kafa tsarin musulunci akan ginshikin wilaya domin kalubalantar...
    A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
    Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, mako guda bayan Majalisar Dattawa ta amince da nadinsa a ranar 16 ga watan Oktoba. Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin? Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja  A yayin taron, Shugaba Tinubu ya buƙaci Farfesa Amupitan da ya tabbatar am gudanar da sahihancin zaɓe a Nijeriya tare da inganta INEC domin tabbatar da gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci. An tabbatar da naɗin Amupitan bayan Majalisar Dattawa ta...
    Alkalan kotu a Kamaru sun yi watsi da bukatar da jamiyyun adawa suka ka gabatar masu ta neman ko dai su soke wasu sakamakon zaben shugaban kasar ko kuma su soke zaɓen baki daya, inda suka ce za su sanar da sakamako a ranar Litinin, sai dai ta dage lokacin daga baya. Zanga-zanga ta barke a wasu manyan biranen kasar, inda ƴan adawa suka yi zargin an tafka kura-kurai a zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba. Alkalan kotun tsarin mulki sun yi watsi da korafi har takwas da aka gabatar masu, domin a cewar su babu cikakkiyar shaida mai tabbatar da su. Dan takarar ƴan adawa, Issa Tchiroma Bakary ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, wani...
    Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf.   Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar DSS kan nasarar da ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da miyagun laifuka a fadin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki  October 22, 2025...
    Sama da yahudawa 450 daga sassa daban daban na duniya ne suka yi kira ga majalisar dinkin duniya da sauran shuwagabannin kasashen duniya da su kakabawa gwamnatin Isra’ia takunkumin saboda kisan kare dangi da nuna rashin dan adamtaka da ta yi kan alummar gaza. Acikin wata budaddiyar wasika da suka rubuta sun bayyana cewa ba mu manta da cewa mafi yawancin dokoki da sharudda da kuma yarjeniyoyi da aka kafa an yi su ne don kiyaye da kuma kare rayukan yan adam, kuma don mayar da martani ga kisan yahudawa da aka yi na holocus. Wasikar ta bukaci a girmama hukumcin da kotun kasa da kasa  ta fitar da ta hana aikawa da isra’ila makamai, sanya takunkumi ga duk wanda...
    “Allah ya albarkace mu da shugaba mai tsoron Allah da kishin jama’a – mutum ne mai kaunar al’ummar jihar Kano da Nijeriya, kuma me aiki tukuru domin ganin ci gabansu,” in ji Yusuf.   Ya kuma jaddada kudirin sa na ciyar da jihar gaba bisa tsarin falsafar Kwankwasiyya, wanda ke jaddada hidima, rikon amana, da tallafawa.   A nasa jawabin, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar NNPP da na Kwankwasiyya na kasa baki daya da su ci gaba da hada kai da kuma jajircewa wajen ci gaban jam’iyyar.   Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban NNPP na kasa Dr. Ajuji Ahmed, da sauran shugabannin jam’iyyar daga jihohi sama da 30, da masu biyayya da suka halarci bikin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
    Shugaban Ƙungiyar ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya sallami dukkanin lauyoyinsa. A zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis, Kanu ya shaida wa kotu cewa a shirye yake ya kare kansa ba tare da taimakon lauya ba. DSS ta cafke mutum 3 kan zargin sayar wa ’yan bindiga makamai a Kaduna ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum Lauyoyin da ke kare shi ƙarƙashin jagorancin Kanu Agabi (SAN), sun yanke hukuncin cire hannunsu daga kare shi kan shari’ar da yake fuskanta. Daga nan sai Kanu ya fara magana kai-tsaye, inda ya ƙalubalanci ikon kotu na ci gaba da yin shari’arsa.   Cikakken bayani zai biyo baya…
    Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kwara, Barista Senior Ibrahim Sulyman, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da inganta adalci, kyakkyawan shugabanci, da samar da damar samun shari’a ga kowane ɗan ƙasa.   Sulyman ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai na watanni uku (quarterly ministerial briefing) da aka gudanar a birnin Ilorin.   A cewarsa, Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kwara tana daga cikin ma’aikatun da ke ba da muhimmanci ga hidima ga jama’a, wadda ke da alhakin gurfanar da masu laifi a kotu, kare gwamnati, tsara da tantance takardun doka, da kuma ba da shawarar doka ga sauran ma’aikatun gwamnati.   Ya bayyana cewa ma’aikatar na aiki ta hannun sassa guda shida (directorates)...
    Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar.   Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu.   Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen taron horaswa na kwanaki biyu mai taken “Leading Learning for Gender Equality in Education” wanda British Council ta shirya domin wakilai daga jihohin Kano, Kaduna, Plateau da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).   Dr. Makoda ya ce, jagoranci mai ƙarfi da tsari a cikin makarantu shi ne ginshiƙin cimma ingantaccen ilimi. Ya kara da cewa, shugabannin makarantu...
    Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars Football Club sabbin motoci uku domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri a yayin gasar Premier ta shekarar 2025/2026 da ke gudana.   Motocin sun haɗa da babbar motar Marcopolo mai kujeru 29 don ɗaukar ’yan wasa, motar samfurin Hummer, da kuma Sharon da za a yi amfani da ita wajen harkokin gudanarwa da sufuri.   A lokacin da yake mika makullai da takardun motocin a madadin Gwamnan, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Malam Ibrahim Umar Farouk, ya roƙi matasan jihar masu son wasanni da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da guje wa duk wani abu da zai...
    Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja. Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da tankar ta kife kuma ta kama da wuta yayin da jama’a ke ƙoƙarin ɗibar mai. Tun da PDP ta bar mulkin Najeriya maguɗin zaɓe ya ragu – Akpabio Dangote zai sayar da kaso 10 na hannun jarin matatar man shi Wasu da dama sun ji rauni kuma an garzaya da su Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Bida. Shehu, ya ce mata ne suka fi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026.   Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Sai dai, jama’a da dama ba su da cikakken bayani game da irin wadannan sabbin haraji ko menene suke nufi ba. NAJERIYA A YAU: Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ’Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Shin ko ta wadanne hanyoyi ne wannan sabon haraji  zai shafi rayuwar...
    Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 1.37, wanda ya karu da kashi 7 cikin dari bisa na watan Agusta. Yawan kudin shiga da na kashewa da ya shafi kudaden kasashen waje na kasar Sin a farkon rabu’i na uku na bana ya kai dalar Amurka triliyan 11.6, wanda ya kai matsayin koli a tarihi, kana ya karu da kashi 10.5 cikin dari bisa na makamancin...
    A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya sace mata kayanta.   “Abubuwan da aka sace, sun haɗa da iphone 13 Pro Max, an kimanta kudinta akan ₦800,000, kwamfutar ‘Apple MacBook’ da darajarta ta kai ₦250,000, da agogon ‘Apple’ da darajarsa ta kai ₦35,000, ‘power bank’ na Oraimo wanda darajarsa ta kai ₦30,000, da jakar makaranta akan darajar ₦25,000.”   Abdullahi ya ce, nan take jami’an ‘yansanda na shiyyar suka dauki matakin kama...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025
    Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kasuwar yawon shakatawa ta kasar tsakanin watan Janairu zuwa na Satumban bana. Kuma sakamakon binciken kididdigar da aka yi ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, adadin yawon shakatawa da mutanen kasar Sin suka yi a cikin gida, ya zarce biliyan 4.998, adadin da ya karu da miliyan 761 bisa na makamancin lokacin a bara, karuwar ma ta kai kaso 18 bisa dari. Daga ciki, adadin yawon shakatawa da mazauna birane da garuruwa suka yi ya kai biliyan 3.789, adadin da ya karu da kaso 15.9 bisa dari. Sai kuma adadin yawon shakatawa da mazauna yankunan karkara suka yi ya kai biliyan 1.209, adadin...
    Mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Qasim al-Araji, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya ci gaba da ziyararsa a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, inda ya gana da tattaunawa da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran. Qassem al-Araji mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya gana da Manjo Janar Seyyed Abdolrahim Mousavi, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi moriyar kasashen biyu. A yayin ganawar, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Cikakkiyar aiwatar da yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen biyu na da muhimmanci. Manjo Janar Mousavi ya kara...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari kan wasu muhimman wuraren da hatta kawayen haramtacciyar kasar Isra’ila ba su sani ba Tauraron dan Adam na Noor 3 ana daukarsa a matsayin dabara, soja, tauraron dan adam da Iran ta kera wanda ya samu gagarumin ci gaba na bayanai da leken asiri ga sojojin Iran. Masanin tsaro da dabarun yaki Laftanar Janar Abdul Karim Khalaf ya tabbatar da cewa: Tauraron dan adam Noor 3 na Iran yana wakiltar ingantaccen na’ura akan tauraron dan adam na Noor 2, wanda aka kara masa kilo 7 na karin kayan aiki. Tauraron dan Adam na Noor 2 yana da nauyin kilogiram 25, yayin da tauraron Noor 3 ke daukar nauyin kilogiram 32. Abin lura shi...
    Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba.   Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda ke bai wa ’yan kasuwa rancen har zuwa Naira miliyan 5 da kaso tara cikin ɗari (9%) a matsayin kudin ruwa, da kuma Naira biliyan 50 a ƙarƙashin shirin Shugaba kasa Bola Tinubu da ke bai wa ƙanana ’yan kasuwa tallafin kuɗi kyauta bisa wasu sharuɗɗa domin bunƙasa kasuwanci (Presidential Conditional Grant Scheme) da ke ba da tallafin Naira 50,000 ga ’yan kasuwa miliyan ɗaya...
    Bam din Mark 84 kirar Amurka shi ne ya kashe dubunnan mutane a Gaza a hare-haren kisan kiyashi da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai Bama-bamai na Mark 84 da Amurka ta kera ba su buƙatar karin haske, lallai sun kasance abin da ya fi daukar hankalin duniya a lokacin kazamin yakin da aka yi a zirin Gaza, saboda barnar da suka yi da kuma kashe-kashen jama’a da ba a taba gani ba. Wadannan bama-bamai su ne suka fi yaduwa a fagen yakin Gaza, kuma sun fi barna da halaka a lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare kan al’ummar Gaza. Tunawa da su yana da alaƙa da mummunan kisan kiyashi da al’amuran zubar da jini da suka girgiza duniya....
    Shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila ya jaddada cewa: Dole ne a gudanar da bincike kan sakacin Isra’ila har Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 Tzachi Hanegbi, shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila, ya yi kira da a gudanar da bincike kan bala’in gazawar da aka yi a ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023 har kungiyar Hamas ta yi nasarar aiwatar da gagarumar nasara kan Isra’ila. Wannan ya zo ne a cikin kalaman farko da Hanegbi ya yi tun bayan da Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kore shi daga kan mukaminsa. Hanegbi ya ce: “Netanyahu ya sanar da shi yau cewa ya kore shi daga kan mukaminsa.” Ya...
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da aniyarsa ta inganta daidaito tsakanin maza da mata da kuma karfafa jagorancin mata a fannin ilimi a Jihar Jigawa. Shugabar Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Mohammed, ya bayyana hakan a wani taron da HiLWA ta shirya tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai (EU) a Dakin Taro na Manpower Development Institute. Ya ce bincike ya nuna cewa ko da yake mata su ne mafi rinjaye a aikin koyarwa a Jigawa, suna da kaso 14 bisa 100 ne kacal a mukaman shugabanci, kamar shugabar makaranta ko mataimakiya. Wannan, a cewarsa, yana takaita gudunmawar mata wajen tsara manufofi da ci gaban ilimi. Rahama Ya bayyana cewa matsalolin al’adu, tsarin...
      A cewar ministan, shirin sake gina bangaren samar da kayayyaki da samar da ci gaba wanda na wucin gadi ne tsakanin manufar bunkasa ayyukan masana’antu ta kasar da wa’adinta ya kare da kuma sabuwar manufa ta shimfida tubali mai kwari ga ajandar bunkasa masana’antu ta kasar.   Ya kara da cewa, bangaren samar da kayayyaki wanda ya mamaye kaso 15.3 na alkaluman GDP na Zimbabwe a 2024, shi ne kan gaba wajen ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar. (Mai fassara: Fa’iza) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya  October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da...
    Ahmed maiyaki, ya dade yana bayar da gudummawa a harkar yada labarai a a fadin kasar nan bayan kasancewarsa tsohon ma’aikaci a sashin hausa na rediyon Faransa ( FRI).   Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma’aikatar yada labarai wacce tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta , sai bayan lashe zaben gwamna Uba Sani ya dawo da ma’aikatar wacce aka dorawa alhakin kula da yada manufofin gwamnatin jihar . ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince...
    Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara ta  gargaɗi direbobi da sauran jama’a game da rufe lambobin motoci, musamman a cikin garin Gusau, babban birnin jihar. Gargaɗin ya biyo bayan ƙaruwa da ake samu na rahotanni da kuma lura da direbobi da ke tafiya da lambobin motoci a rufe, wanda rundunar ta bayyana a matsayin karya dokokin hanya da ke kawo barazana ga tsaro da zaman lafiya. A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, rundunar ta bayyana cewa wannan dabi’a tana nuna ƙoƙarin kaucewa binciken jami’an tsaro tare da yiwuwar taimaka wa aikata laifuka. Sanarwar ta ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya jaddada cewa rundunar...
    A gefe guda kuma ta roƙi jama’a su yi watsi da rahoton jaridar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025 Labarai Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal October 22, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025
    Babaganaru, ya taɓa jagorantar ƙungiyar inda ya lashe kofunan gasar NPFL guda biyu a shekarun 2011/12 da 2012/13 a lokacin da ya yi aiki a baya. Ana sa ran zai kawo gogewa da a wannan sabon babi na horar da ƙungiyar. A halin yanzu Pillars tana matsayi na 18 a kan teburin gasar bayan wasanni takwas, inda ta samu nasara biyu kacal, ta yi canjaras biyu da kuma rashin nasara huɗu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025 Wasanni Kano Derby: Barau FC...
    Dr Majid Ghayour Mubarhan kwararre kuma farfesa a jami’ar kiwon lafiya ta birnin mashahada ya samu kyautar hukumar WHO na gabashin meditareniya saboda namijin kokarin da yayi na kirkiro abin da zai kula da kuma kare kamuwa da cututtuka da basa yaduwa, kamar cutar kansa ciwon zuciya da kuma ciwon Sugar. Wannan kyautar tana nuna irin ci gaban da Iran ta samu ne a bangaren kimiyyaa yankin duk da takunkumi da kuma takurawar da take fuskanta daga bangaren kasashen turai dake takaita halartar masana kimiyyar kasar  hallara a matakin kasa da kasa. A duk shekata hukumar lafiya ta duniya tana bada kyauta ga duk wani masanin kimiya da yayi kwazo wajen kirkiro wata fasaha a bangaren lafiyar gama gari,  da...
    Rahotanni su bayyana cewa gwamnatin birtaniya ta sanar a hukumance cire kungiyar tahrirush shams HTS daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wani yunkuri na ganin ta kara kusantar  sabuwar gwamnatin siriya bayan faduwar gwamantin Bashar Al-Asad. Gwamnatin birtaniya ta bayyana cewa wannan mataki zai sanya su kara kusanci da gwamnatin siriya da Abu mohammad Al-Jolani ke jagoranta wanda aka fi sani da Ahmed sharaa wanda shi ne shugaban kungiyar Al-Qaida kuma kwamandan Daesh. Wannan sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen birtaniya David lammy ya kai kasar siriya  a watan yuli, wanda ya sanya ya zama shi ne babban jami’in diplomasiya da ya kai ziyara kasar a tsawon shekaru. Kuma mataki yazo ne duk da hujjoji...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya October 21, 2025 Siyasa Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu October 20, 2025 Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025
    Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
    Piwuna, ya ce gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka duk da sanarwar kwanaki 14 da ASUU ta bayar tun a ranar 28 ga Satumba, 2025. Ya ce babu wani abin da aka cimma wanda zai hana ƙungiyar aiwatar da shawarar majalisar zartarwarta na fara yajin aikin. “Dukkanin rassan ASUU a faɗin ƙasar nan an umarce su da su janye ayyukansu daga misalin ƙarfe 12 na dare ranar Litinin,” in ji Piwuna Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin wannan lokaci, za ta ɗauki mataki mafi tsanani bayan kammala yajin aikin gargaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ta fara. Ƙungiyar ta kuma bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin wata ɗaya don biyan buƙatunta. Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe ASUU ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta gaza ɗaukar mataki cikin wa’adin da ta bayar, za ta iya komawa yajin aiki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe October 22, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas October...
    Labaran da suke fitowa daga birnin Khartum babban birnin kasar Sudan sun bayyana cewa jirgin yaki na kunan bakin wake ya fada kan wani yanki kusa da tashar jiragen sama na birnin kwana guda kafin gwamnatin kasar ta sake bude ta fiye da shekaru biyu da sufe ta. Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabNews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa an rufe tashar jiragen sama na Khurtum ne, jim kadan bayan fara yaki da a cikin watan Afrilun shekara ta 2023.  Yaki tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun  ‘ Rapid Support Forces (RSF), dakarun daukin gaggawa wanda ya lalata muhimman kayakin aiki a tashar, hakan ya sa aka rufe ta.   Wakilin kanfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya...
    Shugaban kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya bayyana cewa, ya bayyana cewa Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya zubar da jinin mutanen yankin yammacin Asia da dama, amma wannan bai bashi lamunin cewa haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) zata zauna lafiya a yankin nan gaba ba. Tashar tal;abijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kungiyar yana fadar haka a jiya Talata a wani bikin kaddamar da littafi wanda yake bayyana ra’yin Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaie dangane da wakoki da kidekide. Yace: Duk tare da zubar da jinin mutanen yankin a duk a lokacinda ya ga dama, Netanyahu ba zai ce yana da lamuni na zaman lafiya ga HKI a nan...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta? October 21, 2025 Daga Birnin Sin Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin October 21, 2025 Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025
      Gwamna Yusuf ya lura cewa, wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suna amfani da manhajojin su wajen yada “labarai masu raba kan addini da siyasa,” wanda a cewarsa, za su iya gurgunta hadin kan al’umma da kwanciyar hankali idan ba a magance su ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni October 21, 2025 Manyan Labarai Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi October 21, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja October 21, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka October 20, 2025
    Tattaunawar wacce aka gudanar a gidan gwamnati dake Kaduna, kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, da majalisar jihar Kaduna karkashin jagorancin Kwamared Ayuba Suleiman ne ta dauki nauyin gudanar da taron, kuma wakilan kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun ilimi na kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli, Zariya; Kwalejin Ilimi, Gidan Waya; da kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta jihar Kaduna dake da cibiyoyin karatu a Kaduna, Kafanchan, da Pambegua, duk sun samu halartar taron.   Kungiyoyin sun ayyana daukar wani mataki na yajin aiki ne a ranar 30 ga Satumba, 2025, kan batutuwan da suka shafi aiwatar da tsarin albashi na CONPCASS/CONTEDISS na 2009, fa’idodin ritaya, da jin dadin ma’aikata gaba daya a manyan makarantu mallakar Jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
    ‘Yan sanda a birnin Abuja sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa Zanga-zangar masu neman a saki jagoran ‘yan awaren Biafar Nnamdi Kanu wanda ake yi wa shari’a bisa tuhumarsa da ayyukan ta’addanci. Shi dai Kanu yana jagorantar kungiyar ‘yan asalin Biarafa ( Ipob) a takaice wacce a hukumance an haramta, saboda kiran da take yin a balle yankin kudu masu gabashin kasar da ‘yan kabilar Igbo suke da rinjaye domin kafa musu kasa mai cin gashin kanta. Jami’an tsaro sun rika yin sintiri a tsakiyar birnin Abuja, da motoci masu silke da kuma masu watsa ruwan zafi. Haka nan kuma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye akan masu goyon bayan kungiyar da su ka...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia October 21, 2025 Daga Birnin Sin Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka October 20, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar October 20, 2025
    Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da shirinsa na ɗaga darajar Kwalejin Jinya ta Nafisatu da ke Kwankwaso zuwa cikakkiyar Jami’ar Kiwon Lafiya albarkacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Taron na wannan Talatar, 21 ga watan Oktoban 2025, ya gudana ne a garinsa na Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, inda aka yaba da ci gaban da makarantar ta samu tun daga kafuwarta a 2019 zuwa yanzu. Tinubu ya naɗa sabon Minista Alƙaluman wucin-gadi na nuna Paul Biya ya lashe zaɓen Kamaru Kwankwaso ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin ƙara buɗe damammaki ga mata matasa su sami ilimin kiwon lafiya mai zurfi. Ya jaddada cewa makarantar ita ce ta farko a Najeriya da ke karɓar dalibai...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanyar Babban Sara zuwa Malam Bako zuwa Shabaru zuwa Kirgi zuwa Albasu, mai tsawon kilomita 28.2, a Karamar Hukumar Sule Tankarkar,wanda kudinsa ya kakaNaira Biliyan 4.47, a ci gaba da shirin Gwamnati da Jama’a. Aikin hanyar zai hada fiye da kauyuka 60 tare da karfafa harkokin kasuwanci da zamantakewa a yankin. Haka kuma, gwamnan ya bude sabuwar cibiyar kula da lafiya ta farko, da makarantar Tsangaya ta zamani, da kuma rukunin samar da ruwa a yankin. Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin Gwamnati da Jama’a hanya ce ta karfafa gaskiya, bayyana ayyuka da kuma baiwa jama’a damar fadin  ra’ayoyinsu. “Mun zo ne mu nuna abin da muka...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu October 21, 2025 Labarai An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole October 20, 2025 Labarai Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU October 20, 2025
    Harkokin kasuwanci sun tsaya cik a wasu sassan Abuja sakamakon zanga-zangar neman a saki shugaban ƙungiyar ’yan ta’addan IPOB da ke neman ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu, inda masu ’yan kasuwa da ma’aikata da dama suka yi asarar kuɗaɗen shiga. A yankunan Wuse, Banex da Mararaba, shaguna da kasuwanni da dama sun kasance a rufe saboda fargabar tashin hankali. Wasu ’yan kasuwa da suka gwada buɗe shaguna sun ce babu ciniki. “Na kasa buɗe shagona yau saboda kowa yana tsoron tashin hankali. Ko da ka bude, babu wanda zai fito saye da wannan yanayin tsoro,” in ji Peter Ayuba, mai sayar da na’urorin lantarki a kasuwar Wuse. A Smart Bridge Plaza da Zuma Garden da ke unguwar Utako, yawancin shaguna...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya bayyana cewa babu kuma wata tattaunawa da HKI, bayan da jakadan Amurka na musamman a kasashen Siriya da Lebanon Thomas Barrach ya isar da sako garesu kan cewa HKI ta ki amincewa da tattaunawa kan ficewarta daga wasu yankunan kasar Leabanon da ta mamaye da kuma shata kan iyakar kasashen biyu. Kakakin majalisar ya fadawa Jaridar Asharqul Awasat a jiya litinin kan cewa ba abinda ya rage a halin yanzu, sai kasashen da suke kula da tsagaita wutan da aka cimma da ita a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 su yi aikinsu. Yace su yi aikinsu na tabbatar da cewa HKI ta mutunta yarjeniyar mai lamba 1107 ta MDD wacce ta...
    A jiya litinin ce masu goyon bayan Nnamdi Kanu shugaban kungiyar neman kafa kasar Biafara (IPOP) daga tarayyar Najeriya, wanda ake tsare da shugaban kungiyar tare da tuhumar ayyukan ta’addan sun fito zanga-zanga suka kuma tushe wata babban titi a Abuja. ‘Yansanda sun jefa masu hayakin teargas don tarwatse su a jiya litinin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa Kanu wanda yake da Passport na kasar Burtania ya yi kokarin wanke kansa daga tuhumar da ake masa tun 2021 amma ya kasa. Kanu yana jagorantar kungiyar IPOP tun da dadewa, da nufin samar da kasar Biafara a yankin kudu maso gabacin Najeriya. Kafin haka dai yan kabilar Ibo sun yi kokarin bellewa daga tarayyar Najeriya a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar Cerebral Palsy, wato tsukewar ƙwaƙwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na ƙwaƙwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki. A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wasu lokutan kuma kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana, cutar na faruwa ne tun kafin a haifi yaro. Ko ta waɗanne irin hanyoyi wannan cuta take kama yaro? NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga shugaban Amurka Trump cewa: su ci gaba da mafarkinsu! Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a yayin da yake tsokaci kan kalaman shugaban Amurka a yayin ziyarar da ya kai yankunan da aka mamaye, ya ce Trump cikin alfahari ya ce kasarsa ta yi luguden bama-bamai tare da lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, yana mai mayar msa da martani cewa: “To, su ci gaba da yin mafarkinsu!” A yayin ganawarsa da safiyar yau da zakaran wasanni kuma wadanda suka lashe gasar Olympics ta kasa da kasa, Jagoran ya kara da cewa: Duk abin da kuke yi ana danganta shi da Iran da kuma al’ummar kasar  ne, kuma...