2025-09-17@23:30:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3660
«Afrika ta Yamma»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu. Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsaloli ga lafiya. Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin abubuwan da idan aka tara su a jiki na dogon lokaci, suna iya haifar da illa. NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?...
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke shirin tafiya wurin bauta a ranar Lahadi. “CLO ya je don ya tayar da shi daga barci amma sai ya gano cewa, ba ya numfashi, nan take ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yansanda ta Dambam,” in ji Wakil. Biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori-Aliyu, jami’in ‘yansanda na sashen ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin. An garzaya da Chukwuebuka...
Harin ya matukar tayar da hankalin al’ummar yankin, inda mazauna wurin suka tsere domin tsira da rayukansu. Rundunar ‘yansandan jihar Sokoto ba ta fitar da adadin waɗanda suka mutu ko suka ji rauni ko kuma aka sace su ba a yayin kai harin. Shugaban jam’iyyar APC a jihar Sokoto, Honarabul Isah Sadeeq Achida, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin harin dabbanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin jihar Kano ta gana da shugabannin ‘yan bangar siyasa da suka tuba a jihar tare da yi musu alkawarin tallafa musu ta hanyar sauya tunaninsu da horar da su sana’o’i da kuma kayan aikin fara sana’ar. Taron wanda ya gudana a ranar Talata a Kano ya samu halartar tubabbun ‘yan barandan siyasa da masu satar waya kusan 718. Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Kwangilar Hanyoyi 17 Akan Naira Biliyan 40.8 Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya ya yi kira ga mahalarta taron da su rungumi tuba da gaskiya tare da bayar da hadin kai ga shirin gwamnati na...
Ejodame ya rahoto CAS, yana cewa “Tare da ingantattun jirage da ke da ingantattun tsare-tsaren kai hare-hare na dare, jirgin NAF ya kai hare-hare guda 798”. A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya yabawa NAF bisa ci gaba da bayar da tallafi ta sama wajen gurgunta karfin ‘yan ta’adda da kuma kare al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya. Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista. “A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya...
Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo. Larijani ya kara da cewa a wani taron manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraki; “Dukkansu sun damu da tsaron yankin baki daya, kuma al’ummar Iraki ba sa bukatar wani takunkumi.” Larijani ya jaddada cewa: Rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasar Iraki na da nufin hana duk wata barazana ga tsaron kasashen biyu. A yayin da yake mayar da martani ga wasu nazari...
Hakan ya gudana a ƙarƙashin jagorancin hukumomin da ke lura da yadda ake tafiyar da gasar da kuma kare haƙƙin masu amfani da kaya (FCCPC), hukumar kula da tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), da hukumar kula da harkokin caca da wasanni ta Jihar Legas (LSLGA). Zaɓen ya kasance cikin gaskiya da adalci, inda waɗanda yi nasara suka bar Naira 10,000 a cikin asusun ajiyarsu na Stanbic IBTC ko @ease Wallet har tsawon kwanaki 30. Daga mata ‘yan kasuwa, zuwa ɗalibai, har zuwa ma’aikatan da suka yi ritaya, waɗanda suka yi nasara yanzu suna iya biyan kuɗin makaranta, fara ƙananan sana’o’i, ko kuma tafiyar da buƙatun gidajensu cikin sauƙi. An ƙara sanya wasu mutane takwas cikin farin ciki a zaɓen babbar garaɓasar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Babban abin kunya ne shirun da gwamnatocin yammacin Turai suka yi game da muggan laifukan ‘yan sahayoniyya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya dauki kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suka yi wa ‘yan jaridun Falasdinawa a matsayin wata shaida ta ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da take gab da rugujewa. A yayin da yake tsokaci game da kisan gilla da yahudawan sahayoniyya suke yi kan ‘yan jaridan Falasdinawa, Araqchi ya rubuta a dandalin sada zumunta na “X” a jiya litinin cewa: “Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wasu fitattun ‘yan jarida na Falasdinu. Shin wannan wata alama ce ta nuna karfi? Ko kuwa shaida ce ta ta’addancin gwamnatin da...

Babban Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace
Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo. Larijani ya kara da cewa a wani taron manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraki; “Dukkansu sun damu da tsaron yankin baki daya, kuma al’ummar Iraki ba sa bukatar wani takunkumi.” Larijani ya jaddada cewa: Rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasar Iraki na da nufin hana duk wata barazana ga tsaron kasashen biyu. A yayin da yake mayar da martani ga wasu nazari...

Ministan Harkokin Wajen Iraki Ya Bukaci Zaman Tattaunawa Tsakanin Kungiyar Larabawan Yankin Tekun Gulf Da Iraki Da Kuma Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya ba da shawarar gudanar da taron kasashen Larabawan yankin tekun Pasha da Iraki da kuma Iran Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein ya gabatar da shawarar gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Iraki, Iran, da kuma kasashen larabawan yankin Gulf, a tsarin na 6+2, a gefen taron majalisar dinkin duniya. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta fitar ta bayyana cewa: Mataimakin fira ministan kasar ta Iraki, kuma ministan harkokin wajen kasar Fuad Hussein ya gana da Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran. Sanarwar ta bayyana cewa, a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da aikin layin dogo da zai hada Shalamcheh...
Kasar Italiya ta janye jirgin ruwanta daga tekun Bahar Maliya bayan gazawarta a fage kwamawa da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Kasashen Turai sun ci gaba da janye jiragen ruwa da jiragen yaki daga tekun Bahar Maliya, lamarin da ke tabbatar da hukuncin da kasashen nahiyar suka dauka na cewa ci gaba da zamansu a cikin tekun ba shi da amfani bayan da Dakarun ‘yan gwagwarmyar Yemen suka yi gargadin cewa; Duk masu alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila zasu fuskanci hare-haren makamai masu linzami da na jiragen saman yaki. Kwanaki biyu bayan sanar da janye jirgin ruwan Faransa daya tilo, da rundunar Turai ta kafa don kare jigilar jiragen haramtacciyar kasar Isra’ila, “Aspedes,” ta sanar da janye jirgin ruwan Italiya...
‘Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da mutumin da giyar mulki ke ruɗawa, bayan ya ce zai tura jami’an rundunar tsaro ta ƙasar birnin Washington don yaƙi da laifukan da ake ganin sun gagari ƴansandan birnin. Magajiyar birnin Muriel Bowser, ta ce matakin bai dace ba, sannan ta musanta batun da shugaban ke yi cewa an gaggara daƙile masu aikata laifi. ‘Yan Democrats a majalisa, sun ce wannan mataki babu wani abin da zai haifar face ‘tsoro da hargitsi, kuma wannan yunƙuri ne kama hanyar kama-karya. Shugaban masu rinjaye a majilsar wakilai ya ce Mista Trump ya mayar da mulki kamar wata sarauta. Shi dai Trump ɗin ya ce birnin washington a cike yake da masu gararamba a...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne tare da kwato musu wasu abubuwa na bata gari a Ilorin. A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce, ‘yan sandan da ke aiki bisa sahihiyar bayanan sirri daga majiyoyin tsaron al’umma, sun dauki wami mataki kan wani harin fashi da makami da ya afku a wani dakin kwanan dalibai da ke unguwar Eleko, Ilorin. Sanarwar ta ce ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga, sun kai ga kama wasu maza biyu da ake zargi. Ta ce wadanda ake zargin sun hada da Ishola Adeyemi,...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da gargadi game da hawan keken masu kananan shekaru da rashin biyayya ga fitilun ababen hawa a cikin babban birnin Kano. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano. Gargadin na zuwa ne bayan an samu munanan hadurran kan tituna guda 16 a cikin watan Agustan 2025, wanda ya yi sanadin jikkata da asarar dukiyoyi. Rundunar ta lura cewa hawan keken ƙananan yara yana haifar da babban haɗari ga mahaya da sauran masu amfani da hanyar. An shawarci iyaye da masu kula...
Dakarun Operation FANSAN Yamma (OPFY) sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama a wani hari da suka kai ta sama da kasa a yankin Makakkari da ke dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara. Wannan farmakin wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2025, ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu cewa dimbin ‘yan ta’addan da ke biyayya ga marigayi Halilu Buzu da Alhaji Beti sun taru a cikin dajin inda suka shirya kai harin ramuwar gayya kan al’ummomin Addabka da Nasarawan Burkullu a garin Bukkuyum. Jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Fansan Yamma OPFY’ Kyaftin David Adewusi, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa, harin da suka shirya kai...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Dr. Muheeba Dankaka a matsayin shugaban hukumar kula da da’a ta tarayya (FCC) a wa’adi na biyu na shekaru biyar. Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce nadin na daya daga cikin alkawurran da shugaban kasar ya yi na “karfafa hukumar don tabbatar da adalci, daidaito da kuma hada kai a nade-naden na tarayya bisa tanadin tsarin mulki.” Shugaban ya kuma nada Mohammed Musa a matsayin sakataren hukumar sannan Kayode Oladele daga jihar Ogun a matsayin kwamishina. An nada Oladele, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne a hukumar a shekarar 2024 kuma ya rike mukamin shugaban riko bayan kammala wa’adin farko na Dankaka....
Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar. Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin biyu bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar a ranar Lahadi a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar. Taron ya yi nazari ne kan wa’adin da aka bayar tun da farko kan wasu kura-kuran da ake zargin an tafka a cikin ayyukan kwamitin tantance bayanan da gwamnatin jihar ta kafa. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da sakataren kungiyar NLC na jihar,...
Ana ci gaba da ƙoƙarin ceto su da kuma kama ’yan bindigar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna. Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin. Dattijon ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa na zuwa gona, lokacin da wasu tankokin dakon gas biyu suka kama da wuta bayan su gogi juna. Mai auran babban ’yar marigayi Malam Abdullahi Magaji, ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru, akan rasuwar marigayin. ya ce, “A jiya da safe marigayin yana kan babur ne a kan hanyarsa na zuwa gona, sai waɗannan motocin ɗakon man gas...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Samun matasan da ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’ummominsu abu ne da ba kasafai ake samu ba a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bayar da gudunmawarsu wajen ci-gaban al’ummarsu. NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin gudunmawar da matasa ke bayarwa wajen ci-gaban al’ummarsu. Domin sauke shirin, latsa nan
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, an gudanar da binciken sake tantance matsayin WHO daga 28 zuwa 30 ga Mayu, 2025, inda aka kimanta NAFDAC bisa ka’idojin ƙasa da ƙasa. Hukumar ta fara samun wannan matsayi na ML3 ne a 2022, inda ta zama hukumar farko a Afrika mai kula da ƙasashen da ba sa samar da magunguna da ta cimma wannan nasara. Wannan sabon...
Lee ya kara da cewa, fifikon musammam da Hong Kong ke da shi karkashin manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu’, ya ba yankin damar jan hankalin masu zuba jari na ketare domin su lalubo damarmakin kasuwanci a yankin da ma kasuwar babban yankin kasar Sin tare da taimakwa kamfanonin babban yankin shiga kasuwannin ketare. Bugu da kari, ya ce kamfanonin waje da dama sun samu damarmakin kasuwanci a Hong Kong, kuma suna ci gaba da fadada harkokinsu. Su ma kamfanonin babban yankin kasar Sin sun aminta da karfin Hong Kong kuma suna hada gwiwa da tawagar dake Hong Kong wajen lalubo damarmakin dake akwai a kasuwanni masu tasowa na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, Dr Ali Larijani ya gana da firai ministan kasar Iraki Mohammad Shia Assudani a birnin bagdaza inda bangarorin biyu suka tattauna al-amura da dama da suka shafi harkokin tsaro a tsakanin kasashen biyu da kuma matsalolin yankin wadanda suka hada da kasar falasdinu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya bayyana cewa Dr Larijani ya gana da shugaban kasar ta Iraki Abdullataf Rashid da kuma Qasin al-araji mai bawa shugaban kasa shawara a kan al-amuran tsaron kasa. A gaban shugaban kasan ne Larijani da Araji suka rattaba hannu kan wata sabuwar yarjeniyar tsaro mai muhimmanci tsakanin kasashen biyu. Dr larijani ya yabawa kasar Iran a kokarinda take yi don tabbatar da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar kula da albarkatun kasa ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, kasar ta kammala yin rajistar hakkin mallakar yankuna 5 na kare muhalli da halittu na kasar, a matsayin wani muhimmin mataki na daukaka aikin kare muhalli da halittu. Yankunan 5 na kasa sun hada da na Sanjiangyuan da na Giant Panda da yankin kare dabbar Tiger na arewa maso gabashin kasar wato the Northeast China Tiger da na kare Damisa da ake kira Leopard National Park da daji mai dumi da damshi na Hainan wato Hainan Tropical Rainforest da kuma yankin Wuyishan. Rajistar na bayyana ikon da matakai daban-daban na gwamnati ke da shi da bayyana hakkokin mallaka da aikin kula da yankunan da nauyin kula...
Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC na yin son zuciya tare da yin aiki a matsayin kayan aikin siyasa ga jam’iyyar mai mulki APC. Jam’iyyar ta gargaɗin cewa irin wannan mataki yana rage ingancin yaƙin da ake da cin hanci da kuma rage amincewar jama’a. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana cewa ayyukan EFCC na baya-bayan nan, ciki har da buɗe tsofaffin shari’o’i da kuma maida hankali kan ƴan adawa, sun nuna halayyar kamar ta “mai aiwatar da umarnin siyasa” maimakon hukuma mai aiki da gaskiya. Ta kuma zargi hukumar da kiran wasu shugabannin adawa kan shari’o’in da suka dogara da tsoffin zarge-zarge na siyasa. UEFA...
Kakakin NAF ya ce harin, an kai ne tare da hadin gwiwar runduna ta kasa, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu fitattun ‘yan bindiga rundunarsu da dama. Daraktan ya kuma jadadda cewa hadin kai tsakanin sassan sama da na kasa na Operation Fasan Yamma ya sa farmakin ya zama na musamman. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne sun kashe shugaban kungiyar mafarauta a kauyen Garjang da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno. Majiyoyi, a cewar Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ‘yan tada kayar baya, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar Lahadi. Kungiyoyin Kwadago Sun Tsunduma Yajin Aiki A Taraba Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19 Wanda aka kashe mai suna Habu Dala mai shekaru 53, ‘yan ta’addan ne suka dauke shi daga gidansa, inda suka bi da shi ta hanyar Mulharam zuwa kauyukan Forfot da ke karamar hukumar Damboa. An tattaro jama’ar kauye ne domin neman Dala amma daga baya suka tarar da gawarsa dauke da raunukan harbin...
Sojojin mamayar Isra’ila sun harba wata mugunyar ‘karfin wuta’ da jiragen saman yaki kan yankin kudancin Gaza Bayan tsakar dare ne jiragen yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da luguden wuta a kudancin birnin Gaza. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta nakalto majiyoyin da ta bayyana a matsayin na cikin gida na cewa: Jiragen saman sojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri, inda suka harba makamai masu linzami sama da 20 cikin ‘yan mintuna a kudancin mahadar Al-Musalaba da Dawla da kuma kusa da masallacin Ali, inda suka nufi kudu. Wakilin cibiyar ya ruwaito cewa, galibin hare-haren sun fi karkata ne a kan titin 8 da ke kudancin Gaza. Wadannan hare-haren dai na zuwa ne a...

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza
Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa na kwamitin tsaron Majalisar kan halin da ake ciki a Gaza. Suna Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na fadada ayyukanta na soji a Gaza. Ya kuma jaddada cewa: Hakan yana barazana tare da keta dokokin kasa da kasa, yana mai kiran gwamnatin mamayar Isra’ila da ta hanzarta janyewa daga wannan matsayi. Ya jaddada cewa: Duk wani matakin mamaye yankunan Falasdinawa...
Wani mutum ya ba da kyautar motarsa da ita kadai gare shi ga wani mai jan baki (alaramma) saboda ƙwarewarsa a haddar Al-kur’ani. Malam Yusuf Ɗan-Birni, ya kyautar da motar ce a taron wa’azin wata-wata da Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta shirya a garin Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya. Malam Yusuf Ɗan-Birni wanda ke sana’ar gyaran waya, ya bai wa jama’a mamaki a yayin da ake tsaka da karatun da misalin ƙarfe 10 nan dare inda ya miƙa makullan motarsa ga mai gabatar da wa’azin, Sheikh Mahmud Assalafi, ya sanar da shi cewa ya kyautar da ita ga majabaƙinsa, Alaramma Usman Nasidi Gusau. Wani ganau mai suna Malam Nuhu Abu-Huzaifa ya shaida wa Aminiya...
Kungiyar Kwadago da ta ‘yan kasuwa ta Nijeriya (NLC da TUC) reshen jihar Taraba sun bayyana shirin fara yajin aiki tun daga karfe 12 na daren Litinin 11 ga watan Agusta, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jihar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba. A cikin sanarwar da LEADERSHIP ta samu a daren Lahadi mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar NLC, Adamu-Buba, da sakatariyar kungiyar TUC, Polina Gani, sun yi kira ga mambobinsu da su ba da hadin kai ga matakin da kungiyoyin suka dauka domin neman hakkokinsu a wurin gwamnatin jihar ta Taraba. Kungiyar kwadagon ta ce, taron ya sake duba wa’adin da aka bayar...
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe wani fitaccen dan jarida na kafar yada labarai ta Al Jazeera Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa hudu a wani hari da ta kai Gaza. Isra’ila ta zarge shi da kasancewa wani jagora na Hamas sannan ta ce ta hallaka shi saboda irin rahotannin da yake bayarwa masu tsanani daga arewacin Gaza. Isra’ila ta hari ‘yan jaridar biyar – Anas al-Sharif wanda shi ne fitacce tare da Mohammed Qreiqeh masu aikawa da rahotanni ne sai kuma masu daukar musu hoto Ibrahim Zaher da Mohammed Noufal da kuma Moamen Aliwa wadanda dukkanin su suna aiki ne da kafar ta Al Jazeera. A lokacin da Isra’ila ta kai musu harin ta sama suna cikin wani...
Gwamna Oyebanji ya godewa ‘yan majalisar zartarwar jihar da abin ya shafa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba. Sai dai, umarnin bai shafi babban Lauyan jihar da kwamishinan shari’a ba. Har ila yau, daga cikin wadanda sallamar ba ta shafa ba, akwai Kwamishinonin Lafiya da Ayyukan Jama’a, Noma da Tattalin Abinci da Ayyuka. Bugu da kari, kwamishinan ciniki, saka hannun jari, masana’antu da kungiyoyin hadin gwiwa; Mai ba da shawara na musamman kan Ilimin masu bukata ta Musamman; da mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kasa, duk suna nan kan mukamansu. Haka kuma, duk Daraktocin da ke cikin majalisar zartarwa ta Jihar, za su ci gaba da rike mukamansu....
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya kaddamar da aikin sarrafa man kade tan dubu talatin a karamar hukumar Mokwa ta jihar tare da alkawarin samar da muhallin kasuwanci don bunkasa. Wani wuri mai daraja na duniya, wanda Salid Agriculture Nigeria Ltd ya gina kuma bankin NEXIM PLC zai samar da shi zai kawo sauyi ga tattalin arzikin matan karkara, kananan manoma, da kuma tattalin arzikin jihar Neja. Gwamna Mohammed Umar Bago ya samu rakiyar Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, Ministan Noma, Abba Bello, MD/Shugaban Bankin NEXIM, Alhaji Ali Sa’idu, MD/Shugaba na Salid Agriculture Nigeria Ltd da tsohon Gwamnan Bayelsa da kuma fitattun iyayen gidan sarauta da suka hada da mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar da...
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane shida da ake zargin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Doma da ke jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a lafiya, ya ce jami’an sun kuma kama wani makiyayi dauke da makamai a karamar hukumar Keana ta jihar. Sanarwar ta ce, jami’an sashin Doma da ke aiki da sahihan bayanan sirri daga wani dan kasa mai kishin kasa, karkashin jagorancin jami’in ‘yan sandan shiyya, sun kai samame a wata maboyar ‘yan ta’adda da ke Yelwa Ediya inda aka kama wadanda ake zargin. ...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta karfafa matakan tsaro a yankin Babanla biyo bayan harin da wasu da ake zargin mahara ne suka kai musu, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda Adejumo Wasiu. A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai daruruwa, a kan babura, sun mamaye al’ummar Babanla a karamar hukumar Ifelodun. A cewarsa wadanda ake zargin sun kai hari ne a hedikwatar ‘yan sanda inda suka kai farmaki cikin kasuwar. Ya bayyana cewa maharan sun yi ta harbe-harbe kai-tsaye, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda...
Kakakin ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Birtaniya, ya soki kalaman da kasashen kungiyar G7 suka yi, dangane da ganin baiken ‘yan sandan yankin HK, bayan da a ranar 25 ga watan Yuli da ya shude, ‘yan sandan suka fitar da takardar sammacen cafke wasu mutane 19, masu yunkurin haifar da tashin-tashina a kasar Sin da suka tsere zuwa kasashen ketare. A ranar Asabar ne ofishin jakadancin na kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kalamai marasa ma’ana da kasashe membobin kungiyar G7, ciki har da Birtaniya suka furta kan batun, yana mai cewa, wasu kasashe tsiraru ciki har da Birtaniya, sun tsoma baki a batun dokar tabbatar da tsaro, wadda ‘yan sandan yankin musamman na HK ke aiwatarwa,...

Sin Ta Gudanar Da Gwajin Farko Na Gagarumin Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Dakarun Japan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Damina lokaci ne da ɗan Adam yake matuƙar bukata. Da za ta yi jinkiri, sai a ga hankalin kowa ya tashi. A lokaci guda kuma, yadda damina kan hana wasu harkoki gudana kan jefa wasu mutane cikin wani irin yanayi. NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata don cika alkawuran zabe? DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda damina kan shafi rayuwar ƙananan ’yan kasuwa da masu ƙananan sana’oi. Domin sauke shirin, latsa nan
‘Yan jarida 4 Anas al-Sharif da Mohammad Qraiqea, da masu daukar hoto Mohammad Nawfal da Ibrahim Daher sun shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai kan wani tantin ‘yan jarida a arewacin zirin Gaza. Anas al-Sharif, shahharen dan jarida wanda ya sha bayar da rahotonnai da suke fallasa ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila take aikatawa kan fararen hula a Gaza, lamarin da ya Sanya sojojin Isra’ila farautar rayuwarsa. A baya Isra’ila ta bayyana cewa Anas mamba ne na kungiyar Hamas kuma kwararre a bangaren makaman kungiyar, a kan yana daga cikin wdanda take dako. Kwamitin Kare ‘Yan Jaridu (CPJ) ya fitar da wata sanarwa a ranar 24 ga Yuli, 2025, inda ya ce al-Sharif na fuskantar...
“Duk da cewa jama’a suna da ‘yancin nuna sha’awarsu kan siyasa, shirye-shiryen amincewa, yunƙurin tattarawa, da tallace-tallace irin na kamfen da nufin tallata ‘yan takara kafin lokacin yaƙin neman zaɓe na hukumance ba a amince da su ba. “INEC tunin ta nusar da wannan batun a lokacin ganawarta da jam’iyyun siyasa, ta kuma gargaɗin dukkanin ‘yan siyasa da su bi dokoki da ƙa’idojin zaɓe,” sanarwar ta shaida. Ya buƙaci ‘yan siyasa da magoya bayansu da su mutunta matakan zaɓe tare da jiran jadawalin yadda zaɓen zai gudana a hukumance kafin su fara harkokin yaƙin neman zaɓe. Wannan gargaɗin dai na zuwa ne yayin da ake ƙara samun yadda jama’a suke ayyana goyon bayan tazarcen Shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abba Aragchi ya bayyana cewa kara karfin da dangantaka tsakanin Iran da Saudia yake yi, yana taimakawa zaman lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya kara da cewa Aragchi ya bayyana haka ne a lokacinda ya gana da jakadan kasar Iran a Saudiya Ali Reza Enayati a jiya Asabar a nan Tehran. Jakadan ya gabatarwa ministan rahoto kan inda dangantaka tsakanin Iran da saudiya yake. A na shi bangaren ministan ya bayyana kara karfin da dangantaka tsakanin kasashen musulmi biyu yana taimakawa da zaman lafiya mai dorewa a yankin. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
Sojojin HKI sun shiga yankuna da dama a lardin Qunaitara na kasar Siriya a Jiya Asabar. Inda ta kafa shingaye a kan tituna a wasu garuruwa a lardin suka yi ta binciken ababen hawa, kafin su janye daga baya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, HKI tana shirin mamayar wadan nan yankunan na kasar Siriya shi ya sa bata son ganin an sami zaman lafiya a kasar ta Syriya gaba daya, har zuwa lokacinda zata mamaye yankin. Gwamnatin kasar Siriya mai ci ta tabbatar da cewa samuwar sojojin HKI a duk lokacinda suka ga dama a wadannan yankuna alamace ta rashin zaman lafiya a kasar. Kowa ya san cewa HKI ba zata taba barin kasar Siriya...
Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu. NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu Ta bayyana...
Wakilan LEADERSHIP sun lura cewa yanzu ana amfani da wasu daga cikin waɗannan ofisoshin hulɗa da jama’a na Jihar Legas a matsayin matsugunin ‘yan kasuwa na da masu safarar barasa. Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa jami’an tsaro da masu kula da waɗannan gidaje suna hayar wasu sassan gine-ginen da daddare don yin haramtattun ayyuka, inda suka mayar da su gidajen karuwai. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma ‘yan kasuwa a yankunan da ke maƙwabtaka da su, inda suka ce ayyukan na da matuƙar haɗari ga tsaro, suna jawo masu aikata laifuka, da kuma zubar da mutuncin wakilan Jihar a Legas. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da...
Jami’an tsaron kasar Iran sun murkushe ‘yan ta’adda da suka kai hari a ofishin ‘yan sanda a kudu maso gabashin kasar Wasu ‘yan ta’adda da ake kira “Rundunar Shari’a” sun yi yunkurin kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Saravan da ke lardin Sistan da Baluchestan na kasar Iran a wani tsararren harin wuce gona da iri kan jami’an tsaron Iran, amma jami’an tsaron da aka tura domin kalubalantansu sun yi nasarar mayar da martani mai gauni kan ‘yan ta’addan. A cewar majiyoyin Iran, an kashe ‘yan ta’adda uku tare da kame biyu a wadannan gumurzun. Wani dan sanda mai suna Khodadad Baqiri Saravan ya yi shahada a wani artabu da gungun ‘yan ta’adda a birnin Saravan. Share 0 0 votes...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da hakan a matsayin wani mataki na kammala shirin kisan gillar ga Falasdinawa da suke yi da kawar da asalin wanzuwar Falastinu. A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza da yankunan Falastinu da aka mamaye, ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matukar damuwarta da takaicin yadda ake ci gaba da...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
Ya bayyana cewa, gwamnatin da ta gabata ce ta rufe cibiyoyin da aka kafa a gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, amma gwamnatinsa ta yanke shawarar farfado da su domin magance matsalar rashin aikin yi. “Don haka ne a yau, kowane Dalibi wanda ya kammala karatun, ba kawai takardar shaida za a bashi ba har ma da kayan aikin sana’ar da ya koya” in ji Yusuf. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu da hana manoma zuwa gona ko kuma ƙaƙaba musu harajin zuwa gonakin. An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr Aminiya ta ruwaito cewa, a bana ma, maharan sun ci gaba da addabar mazauna ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 na Jihar Sakkwato. Majiyoyi sun tabbatar cewa a harin baya-bayan nan, ’yan ta’addan sun hallaka...
dimokuradiyya ta hanyar ba da umarni ga manyan wadanda ya nada na arewa su halarci taron. “Wannan aiki daya na sadaukarwar da shugaban kasa ya yi don tattaunawa da mutane Yana ishara da cewa, ba wai isa ce kadai a kan iya siyasa ba har ma da isa matuka wajen mutunta ka’idojin dimokuradiyya. Mahalarta taron sun hada da; Sakataren Gwamnati na Tarayya, Sanata George Akume, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribadu, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Christopher Musa, Hafsan Hafsan Sojin Sama Hassan Bala, Kwamanda Janar na NSCDC Dr. Ahmed Abubakar Audi, Shugaban Gwamnonin Arewa, Mai Girma Gwamna Inuwa Yahaya, Mai Girma Gwamnan Jihar Kwara Da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Hon. Abdulrazak...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa da ya rasu ba tare da ba da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba. A ranar Alhamis aka kashe Suleiman al-Obeid, wanda aka fi sani da Pelen Falasɗinawa – a hare-haren Isra’ila lokacin da yake jiran karɓan kayan tallafi a kudancin Gaza. “Ko za ku faɗa mana ta yaya ya mutu sannan a ina,” kamar yadda Salah ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar. Obeid wanda ɗan wasan gaba ne, ya zura kwallaye sama da 100 a tsawon rayuwarsa ta tamaula.
Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon saukar agajin da aka kai a zirin Gaza ya kai Falasdinawa 23 tare da jikkata wasu 124 Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon saukar da agaji ta hanyar jiragen sama tun bayan fara yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan zirin Gaza ya karu zuwa 23, yayin da wasu 124 suka samu raunuka, kamar yadda ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar. Ofishin ya tabbatar da cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Asabar, cewa: Akasarin wadannan kayan agajin da jiragen saman ke watsowa ta sama suna fadowa ne a yankunan da ‘yan mamaya suka mamaye, ko kuma a cikin unguwannin da...

Gwamna Yusuf Ya Amince Da Korar Wasu Mataimaka Biyu Bisa Hannu Akan Belin Wani Dilan Miyagun Kwayoyi
Gwamnatin jihar Kano ta amince da korar wasu manyan mataimaka na musamman (SSAs) ba tare da bata lokaci ba, sakamakon zarge-zargen da wasu kwamitocin bincike suka yi na gudanar da bincike kan wasu laifuka. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar. A wani gagarumin mataki da gwamnan ya dauka, ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa, bayan da kwamitin bincike na musamman ya tuhume shi a matsayin wanda ya shirya belin wani mai hatsarin gaske kuma dilan kwyaan maye, Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ya tabbatar da laifin Abubakar Sharada a cikin takaddamar belin ta hanyar kwamitin da ya gabatar a gaban...
Garima wanda har ila yau shi ne, and Jakadan Gwandu ya yi nuni da cewa, cibiyoyin na CNG da gwamnatin taraya ta samar a jihohin Kano da Kaduna, za su taimaka wajen samar da Iskar Gas ɗin a Arewa ta tsakiya da kuma Arewa ta Gabas. Kazalika ya ce, samar da cibiyar a jihar Sokoto wadda take kusa da Jamhuriyyar Nijar, hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar Garima ya sanar da cewa, Iskar Gas ɗin ta CNG tsafatattaciya ce kuma bata da wani tsada, inda kuma ta rage gurɓatar muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
Wani lokacin, yanayin shekaru da Jinsin Jini ne ke fayyace irin girma ko ƙantantar Ƙwan da Kajin za su yi. 2- Wajen Kwana: Kajin na buƙatar a tabbatar da ana samar musu da wadataccen ruwan sha a ɗakunan kwanansu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutuka da rage musu wahala da cunkoso da kuma zafi, wanda hakan na iya shafar Ƙwan da za su yi kai tsaye. 3- Abinci Mai Gina Jiki: Ciyar da su abinci mai gina jiki, wanda ke ɗauke da sinadaran ‘protein, amino acids’, waɗanda za su sanya su yi nauyi tare kuma da buƙatar a riƙa yi musu allurar ƙara musu lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
‘Yan sandan Birtaniya a birnin Landan sun sanar da kame mutane 365 a wata zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wadda kungiyar Palestine Action da gwamnatin Birtaniya ta haramta a watan jiya ta shirya. A cikin jerin rubuce-rubucen da aka yi a Shafin X, ‘yan sanda sun ce “sun dauki tsauraran matakai a kan wannan laari, tare da yin barazanar kame duk wanda ya nuna goyon baya ga Action Palestine. Masu zanga-zangar dai na dauke da alamomin da aka rubuta “Ku kawo karshen kisan kare dangi, ku goyi bayan matakin Falasdinu,” tare da rera taken “Ku kun ji kunya”. Kungiyar kare hakkibil adama ta “Lift the Ban”, ta bayar da rahoton cewa ‘yan sandan Biritaniya sun gaba da kame mutane kan...
Hukumomin tsaro a kasar Venezuela sun kama wasu tarin bama-bamai a gabashin birnin Maturin na jihar Monagas, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin yunkurin da wasu bangarori masu tsatsauran ra’ayi suka yi na kai hare-haren ta’addanci da nufin kawo cikas ga gwamnatin shugaba Nicolas Maduro. Ministan harkokin cikin gida, Diosdado Cabello, ya sanar a jiya Asabar cewa, jami’an tsaro, bayan gudanar da ayyukan leken asiri, sun gano wasu kayyayakin fashewa da abubuwan harhada bama-bamai da aka boye a wasu shaguna biyu.Kayan sun dai sun hada da akwatuna 1,137 da ke dauke da wasu nauyin bama-bamai da ba a taba ganin irinsu a kasar ba, da rokoki 35, da igiyoyin tayar ta bama-bamai da ababen fashewa, na’urorin kashe...

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar
Jakadan kasar Sin da ke Najeriya, Yu Dunhai, ya gana a kwanan nan da ministar kula da harkokin masana’antu, da cinikayya, da zuba jari ta tarayyar Najeriya, madam Jumoke Oduwole. Jakada Yu ya bayyana cewa, tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar Sin tare da halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a watan Satumban bara, zuwa yanzu, Sin da Najeriya na kara samun fahimtar juna ta fuskar siyasa, tare da fadada hadin-gwiwa a bangarorin da suka shafi masana’antu, cinikayya da zuba jari, har ma kwalliya ta biya kudin sabulu. Ya ce kasar Sin tana fatan ita da Najeriya za su rattaba hannu kan yarjejeniyar raya dangantakar abokantaka a...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya yabawa yan jarida musamman a khidimar da suka gabatar a yakin kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a lokacinda ya kai ziyarar ganin ido a cibiyar hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa shugaban yay aba da ayyukan da yan jarida a kasar suka yi a lokacin yakin kwanaki 12, na samar da hadin kai tsakanin iraniyawa duk tare da banbanci-bambance da ke tsakaninsu da kuma fadin labaran gaskiyan abinda yake faruwa ga mutanen kasar da kuma duniya gaba daya dangane da yakin. Shugaban yay aba da yadda suka nuna zanga-zangar hadin kai...
Yansanda a kasar Burtaniya ta kama mutane fiye da 200 wadanda suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin London. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai a birnin London na cewa mutane kimani 600-700 ne suka fito suka kuma tsaya a wani wuri kusa da majalisar dokokin kasar wanda ake kira ‘ in Westminster’s Parliament Square ‘ inda suke dauke da kwalaye da rubuton ina son mutuncin ma’aikatar sharia, bana son zalunci. Kafin haka dai gwamnatinn kasar ta haramta zanga-zangar da aka saba gudanarwa a birnin na Lodun a dukkan karshen mako, wato ranar asabar na goyon bayan Falasdinawa da kuma yin allawadai da kasashen yamma musamman gwamnatin kasar Burtaniya wacce daga daga cikin...
Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sulhuntawa da kasashen Armedia da Azarbaijan a fadar white House, amma ta yi gargadin shishigin kasashen waje a yankin Caucasus, da ke makobtaka da Iran. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta ta nakalto wani bayani wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a yau Asabar na cewa, sasantawa tasakanin kasashen biyu wani ci gaba wanda zai iya kaiwa ga tabbataccen zaman lafiya a yankin da kuma ci gaba ga dukkan kasashen yankin. Amma a wani bangare kuma bayanin ya bayyana cewa akwai tsoron kasashen waje musamman Amurka tana iya amfani da wadannan kasashen don cutar da yankin ko wasu kasashe. Don haka ta yi kira ga wadannan kasashe biyu su yi...
Shugaban kasar Kwango democradiyya Félix Tshisekedi, a gabatar da sauye-sauye a gwamnatinsa a jiya jumma’a inda ya shigo da sabbin ministoci guda biyu daga bangaren yan adawa. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika News’ ya bayyana cewa gwamnatinn kasar kwango ta fara wannan sauye –sauyen ne tun farkon wannan shekarar kuma har yanzun akwai wasu sauye –sauyen da zai gabatar a dai-dai lokacinda ake ci gaba da tattaunawa da jam’iyyun adawa da kuma yan tawayen M23. A wannan karon dai shugaban ya shigo da sanannun yan adawa guda biyu cikin gwamnatinsa, kuma sune, Adolphe Muzito, wanda ya taba zama firay ministan kasar, ya bashi matsayi na mataimakin firay minister, kuma shi ne zai kula da kasafin kudin kasar. Sai kuma...
Gwamnatin Tarayya ta naɗa Farfesa Mathew Adamu a matsayin sabon mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, wadda aka sake wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon. Farfesa Adamu zai maye gurbin Farfesa Patricia Manko Lar, wadda ta riƙe wannan muƙamin na tsawon watanni shida tun daga Fabrairu 2025. Farfesa Adamu zai fara aiki daga ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, inda zai riƙe wannan muƙami na tsawon watanni uku. Farfesa Adamu ƙwararren masani ne a fannin likitancin dabbobi wanda ya fara karatunsa da digiri daga Jami’ar Maiduguri a 1998, sannan ya samu digirin digirgir a Jami’ar Pretoria, Afrika ta Kudu a 2012, an ɗaga darajar shi zuwa cikakken Farfesa a 2019. Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa Gwamnatin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta, yana da shekaru 78 a duniya, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar. A cikin wata sanarwa, iyalan sun ce: “Ya rasu cikin kwanciyar hankali, ya bar mana gado na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasa da al’umma. Mun sami kwanciyar hankali daga yadda ya shafi rayuka da kuma yadda ya kafa misali.” Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa Iyalan sun bayyana cewa za a sanar da yadda za a...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Shirin gwamnatin mamayar Isra’ila shi ne shirin share al’umma Falasdinu daga kan doron kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Shirye-shiryen da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take yi na mamaye yankin Zirin Gaza da kuma tilastawa al’ummar yankin gudun hijira wani karin shaida ne na musamman da wannan gwamnatin take da niyyar aikata kisan kiyashi a Falastinu da ta mamaye. Ismail Baqa’i ya bayyana shirin gwamnatin ‘yan sahayoniyya na mamaye garin Gaza da sojoji da kuma tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu a matsayin wani shiri na kammala kisan gillar da take yi wa al’ummar Falastinu, yana mai jaddada tofin Allah tsine da Allah wadai da wannan mummunan cin zarafi....
Kwamandan Dakarun Qudus na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Gudun da Amurka ta yi daga Yemen wani shan kaye na soji da ba a taba ganin irin sa ba Kwamandan Dakarun Quds na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ismail Qaani, ya kaddamar da wani kakkausar suka kan Amurka, yana mai bayyana sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na janyewa daga fagen daga a Yemen a matsayin “Halayen soja mafi wulakanci da kunya” a tarihin Amurka. A cewar wani faifan bidiyo da kafar yada labaran “Dakarun Qudus” suka wallafa a shafinsu na Telegram, Birgediya Qaani ya ce: Shugaban Amurka Donald Trump, da kansa ba wani ba—ba kawai kakakin...
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta janye shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya soki shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na kwace iko da birnin Gaza a jiya Juma’a, inda mai magana da yawunsa ya bayyana matakin a matsayin wani abu mai hadari. A nasa bangaren, Volker Turk, babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira a jiya Juma’a da a dakatar da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke da nufin wanzar da cikakken ikon soji a zirin Gaza ta hanyar mamaya. A cikin wata sanarwa da ta fitar sa’o’i kadan bayan da majalisar ministocin tsaron gwamnatin mamayar Isra’ila ta amince da kudurin...
Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Kasashe da kungiyoyin Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da majalisar ministocin gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka mai hatsari na sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kusan miliyan daya gudun hijira daga birnin Gaza da arewacin zirin Gaza zuwa kudancin kasar. A cikin sanarwar da suka fitar a jiya Juma’a, sun yi la’akari da wannan shawarar da kuma shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a matsayin mai hatsarin gaske da zai haifar da bala’in jin kai a zirin Gaza kuma ba za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin ba, suna masu...
Mai ba da Shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da tsohon fira ministan Iraki sun jadadda goyon bayansu ga kugiyoyin gwagwarmaya Mai ba da shawara kan harkokin kasa da kasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tattauna kan ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya a wata tattaunawa ta wayar tarho da tsohon fira ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki, kuma dukkansu sun jaddada goyon bayansu ga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa. A tattaunawar ta wayar tarho, Ali Akbar Welayati, mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasa, ya yi tambaya game da lafiyar tsohon Fira ministan Iraki Nouri al-Maliki. A cikin kiran, Velayati ya yi fatan samun koshin lafiya ga al-Maliki da samun sauki cikin gaggawa, inda ya...
Dortmund za ta buɗe kakar wasanta da Essen a zagayen farko na gasar cin kofin Jamus ranar 18 ga watan Agusta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun. ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga kowace ‘yar wasa ta tawagar ƙwallon kwando a tawagar, tare da ba su kyautar gida a Abuja, a lokacin da yake jawabi ga tawagar, Shettima ya ce nasarar da suka samu alama ce ta ƙarfin haɗin kai. “Wannan nasara ta nuna abin da ke faruwa iɗan muka yi aiki tare, matan Nijeriya ba su tama bamu kunya a ɓangaren wasanni ba,...
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Masu Karya Tattalin Arziki ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa yawancin gidajen da aka yi watsi da su a Babban birnin Tarayya, Abuja, an gina su ne da kuɗin da ma’aikatan gwamnati suka sace. Olukoyede ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba a wani taron tattaunawa da zauren lauyoyi na Law Corridor ta shirya, mai taken “Muhimman Matsaloli da ke Addabar Harkar Gidaje a Najeriya.” Ya shaida wa mahalarta taron cewa EFCC ta kafa wata tawaga ta musamman da za ta fara binciken irin waɗannan gine-gine. “Za mu fara bibiyar dukkan gidajen, ba a Abuja kaɗai ba, har da sauran sassan Najeriya. Muna son sanin wa ke da su,” in ji Olukoyede....
Waɗan nan sune suka keɓe makomar Nijeriya, kuma suka yi garkuwa da ita. Har ila yau, a cewar majalisar dattawa ta 9 da ta yi bincike na sayar da ƙaddarorin gwamnati, wanan ɓarnar dukiyar ƙasa ne a rana tsaka, kuma kamar yadda ɗaya daga cikinsu ya bayyana kafin ya koma cikinsu, ya ce: “PRIƁATIZATION” ba komai ba ce face “PIRATIZATION” — wato sata da rabon ganima ce a fili. Waɗannan su ne masu kuɗi na yaki haram -yaki halas ,da suka ƙwace jam’iyyu, suka wawure zaɓuka, suka yi watsi da kowa sai nasu, suka kashe baitul-mali, kuma yanzu suna neman dawowa bisa kan Karagar Mulki da sunan dimokuraɗiyya. Wannan cutar dimokuraɗiyyar Nijeriya ce da ke ƙara bazuwa, kuma yaudara ne...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, ta wayar tarho a yau Jumma’a 8 ga wata. A tattaunawarsu, Putin ya bayyana ra’ayin kasar Rasha dangane da rikicin Ukraine a halin yanzu, da yadda Rasha ta tuntubi Amurka kwanan nan, inda ya ce, Rasha ta yaba sosai da muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a fannin shawo kan rikici ta hanyar siyasa. A nasa bangaren kuma, Xi ya jaddada matsayin kasar Sin, tare da bayyana cewa babu wata dabara mai sauki da ke iya magance matsaloli masu sarkakiya. Ba tare da la’akari da duk wani sauyi da za a fuskanta ba, kasar Sin za ta tsaya ga neman sulhu da gudanar da shawarwari....

Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samun Biza
Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani. Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni. Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suka fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu. “Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan’uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari. “Wannan mu’amala mai ƙarfi tana...
Wannan irin jita-jitar tana kokain zana shi da kwatankwacin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sin ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na babbar kasuwar mutum-mutumin inji masu ayyukan masana’antu a duniya, wanda ta rike tsawon shekaru 12, kuma ita ce babbar kasa mai kera mutum-mutumin inji a duniya. Sin daya ce daga cikin kasashe masu samar da mutum-mutumin inji dake sahun gaba a duniya, kuma ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa a fannonin hidimar gida da masana’antu da kayan ajiya. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, daga cikin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa akwai mahaifiyar yaran wato Mariya Sani, ‘yar shekara 45 da kuma Mujahid Sani, ɗan shekaru 20, sai Zahariya Sani, ‘yar shekara 18. Sauran sun haɗa da Hauwa Sani, ‘yar shekara 15 da Amira Sani, ‘yar shekara 3 da kuma Nura Sani, ɗan shekara 5. Muhammad ya bayyana cewa yanzu haka akwai waɗanda suka samu raunuka, inda suke asibitin Katsina domin karɓar magunguna. Mahaifin yaran ya bayyana irin kaɗuwar da ya yi lokacin da ya samu labarin faruwar wannan al’amari, wanda ya ce ya yi wa Allah godiya, su kuma da suka rasu Allah ya jikansu. Yanzu haka dai ‘yan’uwa da abokan arziki na ci gaba da zuwa yi wa Malam...
Dabbobi 199 da aka sace (shanu 161 da tumaki 68) Motoci guda 3 da aka sace Babura 2 da ake zargi an sace su Miyagun ƙwayoyi da yawa ciki har da tabar wiwi Wayoyin wutar lantarki da aka lalata DSP Aliyu ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar saboda haɗin kai da suka bayar, yana mai cewa ba za a cimma nasarorin ba tare da taimakon jama’a ba. Ya buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa ‘yansanda goyon baya, tare da kai rahoton duk wani abun zargi ta waɗannan layukan gaggawa: 0815697777722, 0902220969033, da 07072722539. “Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina za ta ci gaba da ƙoƙarinta don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar,” in ji shi....

Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da batan wasu 33. Shugaba Xi Jinping na bada muhimmanci sosai ga yanayin ibtila’i da mamakon ruwan sama ya haifar a wasu yankuna ciki har da gundumar Yuzhong na Lanzhou, babban birnin lardin Gansu. Cikin umarnin da ya bayar, Xi Jinping ya ce aiki na gaggawa shi ne yin dukkan mai yuwuwa wajen bincike da ceton mutanen da suka bata da ganowa da sake tsugunar da...
Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu. Yakin duniya na biyu babbar masifa ce ga dan Adam, kuma irin ra’ayi da ake rike da shi game da tarihin yakin, ya zama wata jarrabawa ga dan Adam. A bana ake cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka samu nasarar yaki da mahara Japanawa, da ma...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar mutane a wajen cirar kuɗi a ATM. Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem, ya ce an kama Umar Abubakar mai shekara 24 da Abdulaziz Mohammad mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano. PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu An kama su lokacin da suke ƙoƙarin yaudarar wani mutum a wajen ATM na bankin Fidelity da ke Damaturu. Ana zargin matasan da amfani da wasu dabara wajen damfarar mutane ta hanyar nuna kamar suna taimaka musu, amma daga baya sai su sauya musu katin ATM. A wani...
An samu mummunan iftila’i a garin Pulka na ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno, inda fashewar Gurneti ya kashe yara uku a yammacin jiya Alhamis. Yaran da suka mutu sun haɗa da Fati Dahiru, Aisha Ibrahim da Fati Yakubu. Rahoton wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa, wani ɗan ƙungiyar CJTF, Buba Yaga, ya ce yaran na wasa da wani bam da ake zargin Boko Haram sun bari, kafin ya fashe da misalin ƙarfe 2:20 na rana. Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno Bayan faruwar lamarin, jami’an kunce bam (EOD) na Ƴansanda, da Sojojin Operation Haɗin Kai, da...
Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara A cewar Goɓspend, an kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu a tsakanin Afrilu da Agusta 2024 wajen kula da jiragen saman shugaban ƙasa. Farkon kashe kuɗaɗen a ranar 14 ga Yulin 2023, lokacin da aka biya naira miliyan 846.03 a matsayin kuɗaɗen tafiye-tafiyen shugaban ƙasa na wucin gadi. Kwanaki biyu daga bisani, an sake kashe naira miliyan 674.82. A wannan watan kaɗai, jirgin ya laƙume sama da naira biliyan 1.5. A watan Agusta, kashe kuɗaɗen sun ƙaru. An kashe...
Sayyid Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya ja kunnen Amurka da HKI kan kara tada hankali a yankin Asia ta kudu. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Alhamis, a lokacinda yake jawabi ga mutanen kasar jawabinsa na mako mako. Sayyid Huthi ya bayyana cewa kasashen biyu suna son ci gaba da yiwa wadan nan kasashen mulkin mallaka, da kuma mamayarsu. Yace: HKI ba abinda take so in kara fadada kasarta don kaiwa ga gurinta na Isra;ila babba, ya kamala da cewa kasashen biyu suna son tababatar da cewa tunaninsu na mulkin mallaka da kuma ci gaba da sace arzikin yankin. A wani bangare na Jawabinsa, Sayyid Huthi ya bayyana cewa, sojojin ...
Sakamakon kama Mu’azu Ɓarga, yanzu haka abokan ta’asar tasa sai tsallakewa suke domin tserewa kamun rundunar ‘yan sanda, duk da gudun da suke rundunar na ci gaba da farautarsu har kuma an samu nasarar ƙara damƙe mutane biyu cikin sama da mutane arba’in da Ɓarga ya bayyana wa ‘yan sanda. Wannan tasa a ranar Juma’ar da ta gabata Al’ummar Sheka ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Muryar Jama’ar Sheka ta ziyarci Shelkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai domin jinjina wa ƙoƙarinsu. Cikin shahararrun mafaɗatan da suka gamu da ajalinsu alokacin arangama daban-daban akwai matashin da ya addabi al’ummar Unguwar Ɗorayi mai Suna Barakita, sai kuma wani mai suna Khalufa ɗan unguwar Ƙofar Mazugal Da kuma wani guda da ke tafka irin wannan...
Sayyid Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya ja kunnen Amurka da HKI kan kara tada hankali a yankin Asia ta kudu. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Alhamis, a lokacinda yake jawabi ga mutanen kasar jawabinsa na mako mako. Sayyid Huthi ya bayyana cewa kasashen biyu suna son ci gaba da yiwa wadan nan kasashen mulkin mallaka, da kuma mamayarsu. Yace: HKI ba abinda take so in kara fadada kasarta don kaiwa ga gurinta na Isra;ila babba, ya kamala da cewa kasashen biyu suna son tababatar da cewa tunaninsu na mulkin mallaka da kuma ci gaba da sace arzikin yankin. A wani bangare na Jawabinsa, Sayyid Huthi ya bayyana cewa, sojojin ...
Wa jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hatsari ya kuma fadi a kan gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya a jiya Alhamis.AMREF Flaying Doctor, jirgi ne karamin samfurin XLS ya tashi daga tashar jiragen sama na Nairobi da nufin zuwa wasu yankuna a kasar Somaliland ya fadi jim kadan bayan tashinsa. An ce matukin bai yi korafin ko akwai Malala a cikin jirgin ba, kuma wani wani gargadi sai kawai anji ya fadi. A halin yanzu dai ba’a san sababin faduwarsa ba, kuma jami’an tsaro basu bada wani bayani har yanzun yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba, ku kuma sunaye da kamanin ko matsayin mutanen da suke cikin jirgin ba. Har’ila...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah, ya bayyana haka yayin mika kayan kayan abincin na musamman da aka sayo ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da UNICEF a shirin Child Nutrition Match Fund, wanda aka gudanar a Cibiyar Kiwon Lafiya (PHC) ta Karamar Hukumar Takai. Mista Rahma, wanda Daraktan Lafiya na UNICEF, Dakta Serekeberehan Seyoum Deres ya wakilta, ya ce kashi 51.9 bisa 100 na yaran Kano suna fama da mat girma...