2025-09-17@23:30:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3660

«Afrika ta Yamma»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Matasa da dama a garin Kafanchan, da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sun yi aikin gayya domin gyara hanyar garin. Sun yi amfani da gatari, fatanya, diga da sauran kayan aiki wajen yi wa hanyar gyara. Ɗaliba ta haɗu da ajalinta a hatsarin mota a Yobe Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Aikin ya haɗa da haƙa da faɗaɗa magudanan ruwa don kaucewa ambaliya da kuma hana hanyar ƙara lalacewa. Shugaban ƙungiyar Kafanchan Youth Forum, Injiniya Sa’adu Bako, ya ce sun yi aikin ne domin rage wahalar da jama’a ke sha, musamman wajen zuwa jana’iza, musamman a lokacin damina. Ya kuma yi kira ga gwamnati ta gyara hanyar, kasancewar ba maƙabarta kaɗai...
    Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude. Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi). Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe Malamin ya rasu a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarsa a unguwar Jan Kai da misalin ƙarfe 5 na yamma. Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ta bakin Daraktan Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli. Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga ɗariƙar Tijjaniyya, iyalansa da kuma al’ummar jihar. “Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan marigayi, ɗariƙar Tijjaniyya, Fityanul Islam...
      An gabatar da dukkan shirye-shirye bisa tsari da inganci kuma ba tare da tangarda ba, inda aka cimma dukkan abubuwan da ake buri.   An shirya gudanar da katafaren taron wanda zai kunshi faretin soja ne a ranar 3 ga watan Satumba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Amma abin takaici, duniya ba ta san laifukan da Japan ta yi wa kasar Sin a lokacin yakin ba sosai. Har yanzu gwamnatin Japan ba ta nemi afuwar Sin da sauran kasashen Asiya da ta jefa cikin ukuba ba. Har ma, ‘yan siyasar Japan masu tsattsauran ra’ayi na ci gaba da gurbata wannan tarihi, a yunkurin gujewa hukunci da al’ummar duniya za su yi musu.   Mace macen da aka samu a yakin duniya na 2, abun bakin ciki ne ga dukan bil’adama. Al’ummomin kasashen duniya suna da makoma da tarihi na bai daya, wanda ba za a iya mantawa da shi ba, balle a gyara shi.   A bana ake cika shekaru 80 da nasarar yakin kin harin...
    Yakasai ya kawo misalin tattaunawa da aka yi da kamfanoni a kasar China lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, inda aka kawo tawaga Kano don duba yiyuwar saka hannun jari amma rashin wutar lantarki ya kawo cikas, ganin cewa dokar gwamnatin tarayya a wancan lokaci ta hana jihohi samar da wutar lantarki ta kansu. Ya bayyana roƙo ga gwamnatin Kano ta yanzu da ta mayar da hankali wajen tabbatar da isasshiyar wutar lantarki, musamman ta hanyar wutar solar ko haɗin gwuiwa da manyan kamfanoni kamar Dangote da BlackRhino, don farfado da masana’antun jihar. A cewar Yakasai, damuwa mafi girma ita ce yadda albarkatun Arewa ake dauka zuwa wasu jihohin kudu don a sarrafa, daga bisani kuma a dawo da su a sayar...
    Sanarwar ta kara da cewa, “Da isar rundunar, ta fara artabu da ‘yan bindigar, inda ta samu nasarar kashe Uku, tare da kwato bindiga kirar AK-47,” in ji sanarwar.   Kwamishinan ‘yansandan jihar Kebbi, CP Bello M. Sani ya yabawa babban jami’in da jami’ansa bisa wannan namijin kokarin da suka yi. Ya bayyana nasarar a matsayin shaida na kudurin rundunar na kawar da masu aikata munanan laifuka a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Taron na Gusau, ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kuma tattauna kan halin da ƙasar ke ciki, matsalolin tsaro, raguwar darajar Dimokraɗiyya, da shirye-shiryen babban taron PDP mai zuwa.   Gwamnonin sun buƙaci mambobin ƙungiyar da su kaurace wa yunƙurin kawo cikas ga taron, inda suka bayyana jam’iyyar PDP a matsayin hanya ɗaya tilo wajen saita Dimokraɗiyya, kuma za ta iya maido da Nijeriya kan turbar shugabanci na-gari da ci gaba.   “Zauren ya sake tabbatar da cikakken ƙudurin da aka yi na taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 101 na Yuli 2025 dangane da babban taron ƙasa na ranar 15 ga Nuwamba.   “Muna kira ga mambobin ƙungiyar da su bijire wa duk wani yunƙuri...
    Wasu majiyoyi na kusa da Putin dai sun bayyana cewar, ya na fatan ganawar da za su yi ta gaba da Zelensky da Trump zai jagoranta ta kasance a Mo scow.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Fluminense Fabio a ranar Talata ya zama mutum na farko a tarihin wasan kwallon kafa na maza da ya buga yawan wasanni a tarihi, lokacin da dan Brazil din ya buga wasa karo na 1,391. Dan wasan mai shekaru 44 a ranar Asabar ya yi daidai da tarihin da tsohon dan wasan Ingila Peter Shilton ya rike na wannan adadin ya samu wannan nasarar a wasan da suka doke America de Cali da ci 2-0 a filin Maracana dake Rio de Janeiro. Kafofin yada labaran Fluminense da na Brazil sun ce a yanzu Fabio ya kasance shi kadai a tarihin kwallon kafa, duk da cewa FIFA ko hukumar CONMEBOL ba ta bayyana hakan...
    A yayin zaman majalisar dokokin jihar Katsina, Babban Mai Tsawatarwa na majalisar, Hon. Ibrahim Umar Dikko, ya fashe da kuka a gaban takwarorinsa, yana bayyana yadda ’yan bindiga suka mamaye mafi yawan yankunan da ke cikin Ƙaramar Hukumar Matazu da yake wakilta. Hon. Dikko ya bayyana cewa daga cikin gundumomi 10 da ke cikin Matazu, guda 8 sun faɗa hannun ’yan bindiga, inda ya ce manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda tsoron harin da ake kai musu. “A jiya da safe, a bakin garin kusa da makarantar sakandare, sun kashe wani matashi sannan suka sace shanu hudu da ake amfani da su wajen noma,” in ji shi cikin hawaye. Ya kara da cewa a cikin kwanaki biyu da suka...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Armenia ta yi alkawalin cewa babu wani sojojin Amurka da zai shiga yankin kaukas ta kudu kusa da kanika da kasar Iran. Musamman ta san cewa Iran bata son haka hakama kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Arachi yana fadar haka, bayan tattaunawa da jami’an gwamnatin Armenia a lokacin da shugaban Iran masoud Pezeshkiyan ya kai ziyarar kasar ta Armenia. Kafin haka dai a makon da ya gabata ne shuga Trump a fadar “White House” ya gana da shuwagabannin kasashen Armenia da Azerbaijan inda suka rattaba hannu a kan yarjeniyar sulhu a tsakanin kasashen biyu, tare da amincewar Armenia ta bawa Azerbaijan damar...
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yaki da zauna da Trump da Kuma Putin a gefe guda don tattaunawa da kuma kawo karshen zabar da jinin mutanen kasashen su. Tsahar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnatin kasar Ukraine na fadar haka, ta kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump a dayan bangaren ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga tsakanin kasashen biyu don fita daga wannan yakin wanda ya gajiyar da dukkan bangarorin. Kafin haka dai Donal Trump ya bayyana cewa idan Zeleski yana bukata to zai iya kawo karshen yakin a rana guda, amma da sharadin ya yi watsi da gurinsa na shiga kungiyar tsaro ta Nato sannan ya...
    Jakadann Amurka na musamman a kasar Lebanon Tom Barrack ya bayyana cewa ya yarda da matakan da gwamnatin kasar Lebanon take dauka don kwance damarar kungiyar Hizbulla ta kasar, Shafin yanar gizo na Alarabia na kasar Saudiya ya bayyana cewa Barrack ya shaidawa gwamnatin kasar Lebanon kan cewa yana kirin kungiyar Hizbullah da kuma kasar Iran wadanda dukkaninsu mabiya mazhabar shia ne da sun a cewa su yi aiki da gwamnatin kasar don sasantawa. Kafin haka dai a ranar 7 ga watan Augusta da muke ciki ne gwamnatin kasar Lebanon ta yanke shawarar kwance damarar kungiyar Hizbullah, sannan ta bawa sojojin kasar umurnin wannan aikin. Kuma ta bawa sojojin kan cewa su kammala wannan aikin zuwa watan satumma mai zuwa....
    Majiyar gwamnatin Hamas a Gaza ta bada sanarwan cewa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila(HKI) sun kashe wani dan jirida a Gaza, wanda ya kawo adadinn yan jaridan da ta kashe tun farkon watan octoban shekara 2023 zuwa 239. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar kiwon lafiya a gaza na cewa a jiya litinin sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa a unguwar Sabra na birnin Gaza, daya daga cikinsu dan jarida ce wanda ake kiransa Islam al-Koumi. Majiyar ta kara da cewa an kashe Koumi cikin makonin da suka gabata, amma ba’a gano gawarta ba sai jiya litinin. Sannan wata Marwa Musallam an binneta karkashin burbushin gine gine, duk kukanta na neman taimaka ba wanda ya ji kararta har...
    A yau ake gurfanar da wani majinyaci mai shekaru 40, zai gurfana a kotu, bisa zargin cin zarafin wata likita mai suna Fatima Umar Gamsa a asibitin Ƙwararru na tunawa da marigayi Janar Sani Abatch da ke Damaturu Jihar Yobe. Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya reshen Jihar Yobe, Dakta Umar Aji, ya ce kungiyar ta kai ƙara gaban ’yan sanda kuma tana jiran hukuncin da kotu za ta yanke. “A yanzu shari’ar tana gaban kotu, kuma ƙungiyar ba za ta ce komai ba har sai ta ji sakamakon hukuncin kotun,” Aji ya jaddada. Wanda ake zargin, Ahmed Usman mazaunin rukunin gidajen Abba Ibrahim da ke Damaturu an tsare shi  a gidan yari na Potiskum har zuwa lokacin da za a saurari...
    Yara 2 sun mutu wasu 6 sun jikkata bayan tashin bom a yankin Ƙofa Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno. Shaidu a garin sun shaida wa wakilinmu cewa bom ɗin ya tashi ne bayan yaran sun kawo shi gida bisa rashin sani. Sun shaida wa wakilinmu cewa yaran sun kawo bam ɗin cikin gari ba tare da sanin hatsarinsa ba, suna ɗauka ƙarfe ne da za a sayar. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Lahadi. ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa An rage kuɗin wankin koda da kashi 76% a asibitocin tarayya NAJERIYA A...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ‘Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya faru a garin Kojiyo dake karamar hukumar Goronyo a jihar sakkwato sun samu kansu cikin damuwa.   Yayin da kalilan daga cikin wadanda abun ya rutsa dasu suka tsira da ransu, wasu da dama sun mutu, a gefe guda kuma an kasa gano inda sauran da abun ya rutsa dasu suke. Wannan lamari ya tayar da hankulan jama’a, musamman ‘yan uwan waɗanda abin ya shafa, waɗanda yanzu ke cikin damuwa, jimami da rashin sanin makoma. NAJERIYA A YAU: Dalilan Karyewar Farashin Hatsi A Kasuwanni DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Shirin Najeriya  A Yau na wannan...
    Mutum 333 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a yayin zaben cike gurbi da aka kammala a Jihar Kano. A ranar Asabar aka gudnar da zaben na cike gurbi a mazabun Majalisar Tarayya da akamaimaita a ranar Asabar a mazabar Ghari/Tsanyawa da kuma zaben cike gurbi na Bagwai/Shanono. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da karuwar adadin mutanen daga 288 a ranar Litinin a hedikwatar rundunar da ke Kano. A cewarsa, zaben ya fuskanci barazana sakamakon “shigo da ’yan daba da dama daga cikin da wajen jihar” da suka yi yunkurin dagula tsarin zaben, amma an samu nasarar shawo kan lamarin ta hanyar haɗin gwiwar hukumomin tsaro.   ...
    Wani mutum ya soka wa budurwarsa mai suna “Ima” wuka har lahira a unguwar Okereke Street da ke garin Fatalkwal na Jihar Ribas. Mutumin, wanda ake wa lakabi da “Doctor” ya daba wa budurwar tasa mai suna “Ima” wuka ne bisa zargin tana cin amanarsa. Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, wanda shaidu a unguwar suka ce ya samo asali ne daga zargin da Doctor ke yi wa Ima, wanda ya rikide zuwa tashin hankali. Mai kula da gidan da lamarin ya faru ya kai rahoto ofishin’yan sanda na Azikiwe Division, Mile 2 Diobu, wanda hakan ya kai ga cafke wanda ake zargi. ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa Mutane 62 da aka sace sun tsere...
    Wasu masu garkuwa da mutane sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa rabon kudin fansar mutanen da suka sace a Jihar Nasarawa. Jami’an tsaro sun kwato bindigogi uku da tsabar kudi Naira miliyan 6.9 daga motar ’yan bingidar bayan hatsarin motar a yankin Garaku, daura da wani shingen bincike na Jami’an Kula da Lafiyar Ababen Hawa (VIO) Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta ce ta kwato makamai masu haɗari da kuɗi sama da naira miliyan shida, bayan wani haɗari da ya faru a kusa da Angwan Mayo. ’Yan sanda daga yankin Garaku sun ce da misalin ƙarfe 9:08 na safe, suka samu kiran gaggawa dangane da haɗarin motar kirar Opel Vectra wadda shaidu suka ce mutane biyu da ke...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Iran ba za ta amince da duk wani sauyi a kan iyakokin yankin siyasa ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce gabanin ziyarar shugaba Masoud Pezeshkian zuwa kasar Armeniya cewa tabbatar da yanayin siyasar yankin bai canza ba, shi ne batun tuntubar da shugaba Pezeshkian ke gudanarwa a birnin Yerevan fadar mulkin Armeniya. A cikin wata sanarwa ta musamman ga kamfanin dillancin labaran IRNA dangane da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Jamhuriyar Azarbaijan da Armeniya, karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump, da jajayen layukan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gindaya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce: A gobe, shugaba Pezeshkiyon zai ziyarci birnin Yerevan, inda zai zauna...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya barazana ce ga wanzuwar tsaron yankin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya suna wakiltar wata barazana ga wanzuwa tsaro da zaman lafiyar yankin da kuma kasashensu. Idan ba a dakile wannan barazanar ba, to babu shakka yankin zai fuskanci yake-yake marasa iyaka. A yayin taron manema labarai na mako-mako a ranar Litinin, Baqa’i ya yi ishara da zagayowar ranar 28 ga watan Mordad (19 ga Agusta, shekara ta 1953, yana mai cewa: Ba za a iya mantawa da wannan lamari mai zafi ba, juyin mulkin da ya hambarar da zababbiyar gwamnatin al’ummar Iran tare da hadin gwiwar Amurka da Birtaniya. Dangane da ci...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a mazabu 16 a jihohi 12 na ƙasar nan. Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa shugaban ƙasa ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bisa gudanar da zaɓen lafiya ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba. A cewar sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe kujeru 12, yayin da jam’iyyar APGA ta samu biyu. Jam’iyyar PDP da jam’iyyar NNPP kowanne ya samu kujera ɗaya. Shugaba Tinubu ya taya sabon shugaban jam’iyyar APC na...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar jihar bisa rasuwar Sarkin Zuru, Mai Martaba, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (Gomo II). A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana rasuwar Sarkin  a matsayin “babban rashi ga ƙasa,” inda ya tuno irin hidimar da marigayin ya yi a matsayinsa na tsohon gwamnan soja na Jihar Bauchi da kuma  hidimarsa a matsayin basarake. Shugaba Tinubu ya lura cewa Najeriya za ta daɗe tana tuna gudummawar tsohon janar ɗin, wanda kuma ya yi yaƙi a matsayin ƙaramin hafsan soja lokacin Yaƙin Basasa. Shugaban ƙasa ya kuma yabawa jagorancin...
    Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba zasu yarda wasu kasashe su shiga tsakanin Iran da Iraki ba Yayin da yake magana game da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakanin Iran da Iraki, babban sakataren majalisar koli na tsaron kasar Iran Ali Larijani  ya yi nuni da cewa: Bai kamata a bar kasashe uku su tsoma baki cikin fahimtar juna da tsaron da ke tsakanin kasashen biyu ba, ko kuma su yi amfani da yankin wata kasa a kan wata kasa. Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya tattauna da shirin “Tehran-Tel Aviv” da aka watsa a gidan radiyo da talabijin na kasar Iran kan ziyararsa ta farko a wannan matsayi a kasashen...
    Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da neman kasashen da za su karbi ‘yan gudun hijiran Falasdinawan Gaza! Jaridar Wall Street Journal ta buga wani rahoto da ke cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da gudanar da tattaunawar da ta bayyana na zaman natsuwa domin tura ‘yan gudun haijiran Falasdinawa daga Gaza. Kasashen da suka hada da Libiya, Siriya da Sudan ta Kudu. Rahoton wanda Samar Sa’ed, Robbie Gramer, da Omar Abdel Baqi suka shirya, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da Amurka suke yunkurin tura dubban daruruwan Falasdinawa daga zirin Gaza zuwa gare su, matakin da suka gabatar cewa akwai hanyoyin jin kai, amma gwamnatocin yammacin Turai da kasashen...
     Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa shuwagabannin kasashen turai kan cewa ya amince da shawara shugaba Putin na musayar kasa don samar da zaman lafiya. Majiyoyi biyu wadanda basa son a bayyana sunayensu kuma kusa da Trump a taron na Alaska ya bayyanawa jaridar ‘The guardian’ ta kasar Burtania a jiya Asabar kan cewa, Trump ya fadawa masu kan cewa Zeleski ya amince da mikawa Putin Dombasa sannan rasha kuma zata tsaya inda take, ba zata karbi sauran yankunan Donbas da suke hannun Ukraine ba. Don haka putin ya dage kan cewa dole Ukraine ta fice daga Dobas Kwata-kwata. Labarin ya ce har yanzun Ukraine tana iko da Kramatorsk da Sloviansk a yankin Donestk. Sannan yankunan kudancin Ukraine Kherson...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani matashi mai suna Azeez Bello, mai shekaru 29, wanda ya kitsa garkuwa da kansa domin karɓar kuɗin fansa Naira dubu 500 daga hannun iyayensa. Kakakin rundunar, Ayanlade Olushola, ya bayyana cewa Bello, ɗan asalin garin Ipele da ke Ƙaramar Hukumar Owo, ya yi haka ne bayan mahaifinsa ya ƙi ba shi kuɗin da ya nema don yin kasuwanci. Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13 Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya A ranar 11 ga watan Agusta, Bello ya shaida wa iyayensa cewa zai tafi Ibadan, amma maimakon haka ya ɓoye kansa a Ipele. Daga nan ya riƙa kiran iyayensa da abokansa yana...
    Kasashe 31 na duniya sun yi Allah wadai da kalaman fira ministan Isra’ila na shirin mamaye yankunan kasashe don kafa ‘Babbar kasar Isra’ila Kalaman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbare kasar Isra’ila” ta janyo suka daga Larabawa da Musulunci. Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi 31, tare da manyan sakatarorin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da kuma kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha, sun yi Allah wadai da kalaman Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbar Isra’ila”, tare da la’akari da furucin a matsayin rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma barazana kai tsaye ga tsaron kasashen Larabawa da...
    Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa ya mayar da martani ga son zuciya da wani jami’in kasa da kasa ke yi game da mamayar ‘yan sahayoniyya Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya yi tsokaci game da kalaman mataimakiyar shugaban kotun kasa da kasa (ICJ) na goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila, yana mai cewa: “Wannan wani lamari ne mai ban mamaki da ya saba wa ka’idojin shari’a da kuma ka’idar rashin son kai na shari’a.” A wata sanarwa dayta fitar a dandalin X, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin shari’a da harkokin kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya rubuta cewa: “Wannan wani lamari ne mai ban...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa unguwar Al-Zeitoun tare da lalata gidajen Falasdinawa kusan 400 Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean ta bayyana cewa: Kwanaki shida ke nan da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ke luguden wuta a unguwar Zeitoun da ke kudu maso gabashin birnin Gaza, inda suka lalata gidaje kusan 400, ta hanyar jefa musu bama-bamai tare da yi musu luguden wuta da jiragen yaki. Hukumar kula da kare hakkin bil adama ta Euro-Mediterranean ta bayyana a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Safa ya samu a yau Asabar cewa: Wannan na zuwa ne a wani bangare na farmakin da sojojinmamaya suka kai da nufin rusa yankin zirin Gaza, kwatankwacin abin da ya faru a yankunan Rafah,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su shiga yaki a ko dauce, amma yana ganin yiyuwar a sake shiga yaki da HKI nan kusa yana da wuya. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Abbas Argchi yana fadar haka, a daren Ashamis da ta gabata, a lokacinda ya kai ziyarar Karbala don ziyarar 40 na Imam Hussain,(a) Ministan ya bayyana cewa, a halin yanzu, mutanen kasar Iran suna da hadin kai a tsakaninsu da kuma gwamnatin kasar , yace makiya zasu so raba kan mutanen kasar da shuwagabanninsu da kuma sojojin kasar wadanda suke bada rayukansu don kare kasar da kuma kare mutanen kasar. Ministan ya kammala da cewa a yakin...
    Ga hotunan yadda ake gudanar da zaɓen cike gurbi a sassan Najeriya.
    A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya. Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana. Manoma sun fara noma cikin kwanciyar hankali Ƙananan hukumomin Batsari, Jibiya da Ɗanmusa na daga cikin wuraren da aka samu wannan ci gaba. Wasu manoma da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana farin cikinsu da yadda rayuwa ke dawowa dai-dai. Malam Rabe, manomi daga Nasarawa a Ƙaramar Hukumar Jibiya, ya ce: “Mu kam yanzu sai mu ce Alhamdulillahi. Lallai sulhu alheri ne a tsakanin al’umma. Ni rabon da na...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa.   Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin domin jajantawa iyayensa da ‘yan uwansa .   “kwamishinan ya Kara da cewa ‘Mai girma gwamna Uba Sani Yaso yazo da kansa amma bisa wasu abubuwa da suka bijiro hakan ya sanya ya wakilto mu saboda haka gwamna ya kadu matuka da samun labarin rasuwar Abubakar”.   Maiyaki, yace domin ganin an dakile matsalar yawaitar tu’ammali da muyagun kwayoyi, gwamnatin jihar Kaduna ta Kafa wani...
    Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu. Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar, yana mai cewa wannan ya sa jihar ta yi fice a bangaren fasahar zamani. “Fasahar zamani zai bai wa harkokin kassuwanci kanana da matsakaita samun damar intanet mai sauri da mai arha da kayayyakin aiki na zamani da samun hadin gwiwa don koyo da ingantawa, tare da tunawa cewa duniya ta kasance wani fage na bunkasa harkokin kasuwanci a zamanance. “’Yan kasuwa da ke habaka...
    Da safiyar yau Jumma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton tattalin arzikin kasar na watan Yuli, inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare da inganta dunkulewar manyan kasuwanni cikin sassan kasar, ta yadda aka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin tsari, da kara bukatun al’umma, da tabbatar da dorewar samar da aikin yi da daidaiton farashin kaya, da kuma raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, inda aka cimma sabbin nasarori kan neman ci gaba mai inganci. A fannin masana’antu kuma, yawan kayayyakin da aka samar ya karu da sauri, kana, aikin kera na’urori da aikin samar da kayayyaki da fasahohin zamani suna bunkasuwa kamar...
    An sami gawar wani sojan HKI wanda ya taba yaki a Gaza wanda kuma ake zaton shi ya kashe kansa. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar HKI da yaren Hebru mai suna  Yedioth Ahronoth yana fadar cewa an gano gawar sojan dan shekara 28 wanda ba’a bayyana sunansa ba a dajin dajin sweezland kusa da yankin tiberias a yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, idan ya tabbata sojan ya kashe kansa ne to kuwa shi ne 17 da suka kashe kansu tun bayan fara yaki a gaza a shekara ta 2023. Ahronoth ya cewa sojan ya yi aiki da runduna ta 99 a gaza a cikin yan makonnin da suka gabata. Sannan a halin yanzu...
    A yau Juma’a ne kasar Japan ta gudanar da gangamin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin duniya na biyu, sai dai yayin da yake jawabi albarkacin taron, firaministan kasar Shigeru Ishiba, bai tabo batu kan alhakin dake rataye a wuyan kasarsa ba, a matsayinta na wadda ta mamayi wasu kasashen nahiyar Asiya. A hannu guda kuma ya gabatar da addu’a ga wurin ibadar nan na Yasukuni, a matsayin girmmawa ga wurin ibadar da ake kallo a matsayin wurin da aka karrama mutanen da suka tafka danyen aiki yayin yakin duniya na biyu. Kazalika, wasu ministocin kasar sun kaiwa wurin ibadar na Yasukuni ziyarar girmamawa. Jerin wadannan matakai dai na shan suka, da adawa daga sassan kasa da kasa....
    Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya soki lamirin kasar Amurka, dangane da yadda ta wanke Japan daga laifukan da ta tafka, yayin yakin duniya na biyu. Jiang Bin, wanda ya yi sukan a Juma’ar nan, ya kira hakan a matsayin mummunan karan-tsaye ga ainihin abun da ya auku a tarihi, kana tozarta damuwar wadanda mamayar dakarun Japan ta cutar. Jami’in ya yi tsokacin ne a matsayin martani ga sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, inda ta ce, bana shekaru 80 ke nan, bayan da Amurka da Japan suka kawo karshen yaki a yankin tekun Pacific. To sai dai kuma a ta bakin Jiang Bin, yayin yakin duniya na biyu, dakarun Japan ‘yan mamaya sun aikata muggan...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita  ce ranar 20...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita  ce ranar 20...
    A farkon wannan shekarar da ta gabata, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito Ministan Sufurin Ma’aikatar Jiragen Sama Festus Keyamo, a wani taro ya bai wa kungiyoyin na Sufurin Jiragen Sama tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da bi ka’ida wajen sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman kasa. Keyamo ya kuma bai wa shugabannin kungiyoyin tabacin cewa, suma a sanya kan batun na yarjejeniyar ta sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman. Kazalika, ba su tabbacin cewa, zai umarci hadiminsa domin ya ci gaba da sanar da shugabannin kungiyoyin kan abinda ke tafiya game da yarjejeniyar. Sai dai, a jawabin da shuwagabbin kungiyar da kuma na ma’aikatan suka gabatar a wani babban taronsu a shalakwar Tashar Jiragen Sama da ke...
    Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani da karfi kan duk wani wuce gona da iri kanta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Gwagwarmaya ita ce babban jari kuma wata dabara mai kima ga yankin, yana mai jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani mai karfi kan duk wani hari da aka kai mata, kuma babu wata tattaunawa da za ta yi tasiri a karkashin tunanin Amurka na “zaman lafiya da nuna karfi.” Ali Larijani ya jaddada a shirye Iran take a koda yaushe ta mayar da martani mai karfi kan duk wani hari da gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai kan...
    Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin na Iran laifi ne na yaki Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin da ke birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar 23 ga watan Yuni yana matsayin laifin yaki. A cikin wani rahoto da ta buga jiya alhamis, kungiyar ta yi bayanin cewa hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gine-gine da dama a cikin rukunin, sun kuma kashe mutane akalla 80, a cewar sanarwar da Iran din ta fitar, da suka hada da fursunoni da ‘yan uwansu, da...
    An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila a wani dajin da ke arewacin Isra’ila. Sojan ya kashe kansa ne a lokacin da yake aikin soja, wanda ya kawo adadin sojojin da suka kashe kansu tun farkon wannan shekara zuwa 18, kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka bayyana. Gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya bayyana cewa: Rundunar sojin ta bude bincike kan lamarin, tare da bayyana cewa jami’in da ya kashe kansa yana shiyya ta 99 da ke yaki a zirin Gaza. Jaridar Yedioth Ahronoth ya watsa rahoton cewa: Jami’in dan shekaru 28 ya...
    Ya ce: “A Inugu, mun sami damar cika duk abin da muka yi wa mutanen mu alƙawari a lokacin kamfen, godiya ga jarumtar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi, wadda ta samar mana da albarkatun da ake buƙata don aiwatar da manyan ayyuka.”   Ya kuma bayyana ayyukan da ake yi a halin yanzu a jihar, waɗanda suka haɗa da gina ajujuwa 7,000, samar gadajen asibiti 3,300, da samar da gonakin gwamnati hekta 2,000 a cikin gundumomi 260 na jihar.   Gwamna Mbah ya yi alƙawarin ci gaba da mara wa manufofin Gwamnatin Tarayya baya, yana mai cewa suna da amfani ga al’ummar jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Babban Sufeton ’Yan Sanda na Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce galibin jama’a ba sa yaba wa kokarin jami’ansu na hana aikata laifi a cikin al’umma, duk da yana daya daga cikin manyan ayyukansu. Kayode, wanda Mataimakin Babban Sufeto mai kula da sashen sayo kayayyaki na rundunar, A.A. Hamza ya wakilta, ya fadi hakan ne a Abuja ranar Alhamis, yayin taron kaddamar da wani littafi mai suna “Fraud unmasked”, wanda Dr Preal Ogbulu ya wallafa. Kotun kasar Kanada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a Najeriya A cewarsa, “Duk laifin da aka dakile aikatawa, dole akwai namijin kokarin da aka yi a kan hakan. Kundin tsarin mulki da...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauyen jagoranci a Hukumar Talabijin ta ƙasa (NTA), inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro a matsayin sabon Darakta-Janar. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Karimah Bello a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Tallace-Tallace, Stella Din a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Labarai, da Sophia Essahmed a matsayin Manajing Darakta ta Kamfanin NTA Enterprises Limited. Pedro, ɗan asalin jihar Lagos, ƙwararren mai ba da shawara ne a harkar kafofin watsa labarai, mai gogewa sama da shekaru 30 a fannoni da suka haɗa da talabijin, haƙƙoƙin watsa wasanni, da dabarun tallace-tallace a Afrika, da Birtaniya da Gabas ta Tsakiya. Kwararre ne a fannin nishaɗi da mallakar fasaha, tare da digirin na biyu a Gudanar da Zuba...
    Akwai wasu tsaffin ‘yan siyasa daga yankin Arewacin Najeriya,wadanda ke ci da gumin ‘yan Arewa. Wadannan tsaffin ‘yan siyasa, yanzu alkadarinsu ya riga ya karye, ba su da wani abu da ya rage illa su rungumi siyasar kabilanci da bangaranci. Ba tsaffin ‘yan siyasa kawai ba ne. Gungu-gungu ne. Wasun su, tsaffin ‘yan boko ne. Wasu ‘yan Kasuwa. Wasu ma ba wata sana’a ko wani aiki da suka taba yi a rayuwarsu da ya wuce ci da gumin Arewa . Wani abu da ya hade su shi ne, mafi yawansu sun samu damar da za su taimaki Arewa ko mutanen Arewa, amma suka ki. Misali, a cikin irin wadannan mutane, babu maras sa kunya,irin wadanda suka rike mukamai a gwamnatin...
    Gwamna Malam Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana harkar kiwon dabbobi a matsayin babbar harkar tattalin arziki ta biyu a jihar baya ga noma. Ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamishina na farko na ma’aikatar ci gaban kiwon dabbobi da aka kafa kwanan nan, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, a zauren majalisar zartarwa na gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, baya ga noma, kiwon dabbobi shi ne babban abin da mutanen jihar Jigawa suka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kara da cewa kafa wannan ma’aikata na cikin shirin gwamnati na bude manyan damarmaki da ke cikin wannan bangare. “Mun dauki mataki na musamman domin ingantawa da bunkasa bangaren kiwon dabbobi. Mun yi hadin gwiwa da...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari ga daukacin al’ummar Falasdinu ne Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari kan dukkanin al’ummar Falastinu ne, yana mai jaddada cewa: Makiyan ‘yan sahayoniyya sun aikata kowane irin laifi da kowane nau’i na wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu a zirin Gaza. A jawabin da ya gabatar kai tsaye kan sabbin ci gaban da ake samu a hare-haren wuce gona da iri kan zirin Gaza da kuma ci gaban yanki da na duniya, Sayyed al-Houthi ya yi nuni da cewa, yawan hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai cikin...
    Kungiyoyin kasa da kasa guda 100 sun koka kan yadda gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi watsi da bukatu har 60 kan ba da damar shigar da agaji zuwa Gaza Sama da kungiyoyi masu zaman kansu 100 ne suka bayyana a wata wasika ta hadin gwiwa da aka buga jiya alhamis cewa, ana kara amfani da sabbin dokokin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta tsara kan ayyukan kungiyoyin agaji na kasashen waje wajen kin amincewa da bukatarsu ta shigar da kayayyaki zuwa zirin Gaza. Wasikar ta ce: “Hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila sun yi watsi da bukatar da kungiyoyi masu zaman kansu da dama suka gabatar na kawo kayayyakin ceton rai, lamarin da ya bar miliyoyin daloli na agajin jin kai da suka...
    Laifukan da ake gudanarwa a gabar tekun Siriya: Cin zarafin ya kai ga laifukan yaki! Rahotonni sun bayyana cewa; Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Siriya ya fitar ya ce: Rikicin kabilanci da ya faru a gabar tekun Siriya ya kunshi cin zarafi da ya kai ga laifukan yaki. Rahoton ya kara da cewa; Rikicin addini ya shafi mabiya darikar Alawiyya ne, inda aka kashe fiye da mutane 1,400 Alawiyyawa a rikicin addini da suka hada da daukacin iyalai da mata da yara da kuma tsofaffi a gabar tekun Siriya. Bugu da kari, an samu rahotannin kone-kone, sace-sace da kuma wulakanta gawarwakin da wasu ‘yan bindiga suka aikata. Rahoton ya bukaci gwamnatin rikon kwarya ta Siriya da ta fadada kokarin...
    Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta sanar da cewa: Mutane 40 ne suka mutu a Sudan sakamakon barkewar cutar kwalara mafi muni cikin shekaru Kungiyar likitocin ba da agaji ta “Doctors Without Borders” ta sanar da mutuwar mutane 40 sakamakon kamuwa da cutar kwalara a Sudan cikin mako guda kacal, tare da tabbatar da cewa a halin yanzu kasar na fama da barkewar cutar mafi muni cikin shekaru da dama, sakamakon yakin da ake yi. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar ta bayyana cewa, kungiyarta ta yi jinyar mutane fiye da 2,300 masu fama da cutar kwalara a yankin Darfur kadai a cibiyoyin da ma’aikatar lafiya ta kasar ke kula da su, inda ta yi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A wasu jihohin Arewacin Najeriya, masu karɓar fansho suna cikin mawuyacin hali sakamakon ƙarancin kuɗin da ake biyansu duk wata. Wasu daga cikinsu sun bayyana yadda suke karbar naira dubu 5 a kowane wata a matsayin kudin fansho bayan kwashe shekaru suna aiki. NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin halin da ’yan fansho ke ciki a wasu jihohin Arewacin Najeriya. Domin sauke shirin, latsa nan
      Alkaluman sun nuna cewa, cikin wa’adin, yawan sakwannin da aka yi jigilarsu a cikin birni daya sun kai biliyan 9.26, adadin da ya karu da kaso 6.5 bisa dari a mizanin shekara, yayin da wadanda aka yi jigilarsu daga birni guda zuwa wani na daban, suka kai biliyan 100.43, karuwar da ta kai ta kaso 19.9 bisa dari cikin wa’adin na watanni bakwai. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.   “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, wasu sai sun amso cin hancin kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, kuma dole sai sun bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”  ...
    A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.   “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, wasu sai sun amso cin hancin kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, kuma dole sai sun bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”  ...
    Bugu da kari, idan an lura da yawan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin lantarki, yawan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin a shekarar 2024 ya kai kusan 42000, wanda ya karu da kusan kashi 9 bisa dari a shekarar 2023.   A farkon rabin wannan shekara, masana’antar lantarki ta kasar ta ci gaba da kiyaye ingantaccen yanayin ci gaba. Kudaden shiga da manyan kamfanonin masana’antar samar da kayayyakin lantarki suka samu ya kai yuan triliyan 8.04, wadanda suka karu da kashi 9.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyeed Abdulmalik Badruddeen Huthi , a jawabinsa na mako-mako da ya saba gabatarwa, dangane da Falasdinu da kuma sabbin al-amura da suka faru ko suke faruwa a yankin da kuma duniya gaba daya ya tabo al-amura da dama. Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye shiryenta da harshen larabci a nan Tehran ta bayyana cewa, shugaban Ansarullah, ya yi gargadi kan cewa, ida HKI tana son dabbaka shirinta na Isra’ila babba, a cikin wannan halin da kasashen larabawa suke rarrabe, hakan zai zama musiba babba. Labarin ya kara da cewa sojojin kasar Yemen sun aiwatar da ayyukan soje a kan HKI a dama a cikin makon da ya gabata, daga cikin cilla makamai...
    Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin ta ce nan ba da jimawa ba, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar, za su gudanar da zagaye na 3 na ayyuka a wajen cibiyar. ‘Yan sama jannatin 3 da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da irin wannan aiki har sau biyu, a watannin Mayu da Yuni. Baya ga haka, sun kammala ayyukan nazarin muhalli da kula da tantance da kayayyakin aiki a cikin cibiyar da jigilar kayayyaki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.   “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, sai an biya kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, sai ka bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”   Dan majalisar ya kuma yi...
      Ya kara da cewa, kasar Sin tana kira ga kasa da kasa su ci gaba da tallafa wa ayyukan UNRWA, yana mai cewa a shirye Sin take ta yi abun da zai kawo karshen rikicin da samar da mafita mai adalci da dorewa bisa manufar kafa kasashe biyu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar ‘yan bindiga,” in ji shi. Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya ɗauki matakaki a kan waɗanda suka aikata wannan kisan gilla, sannan ya roƙi jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin kawo ƙarshen duk wata ɓarna a Zamfara. Sarkin Kauran Namoda, Dokta Sunusi Ahmad Rashad, wanda ya raka gwamnan, ya yaba masa bisa saurin ɗaukar mataki bayan faruwar lamarin. “Wannan ziyara tana da...
    Dukkanin mutanen biyu na Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan an kammala bincike. Kwamishinan ’Yansandan jihar, Emmanuel Olugbemiga Adesina, ya gargaɗi masu aikata laifi su daina ko su bar jihar. Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da aiki don tabbatar da masu laifi sun fuskanci hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi tsokaci kan furucin Netanyahu game da kafa ‘Babban Kasar Isra’ila’ Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana a safiyar yau alhamis cewa: Kafafen yada labaran yammacin duniya a al’ada na zargin duk wanda ya ambaci ra’ayin ‘yan sahayoniyya na kafa “Babban kasar Isra’ila” da kiyayya ga wata al’umma. Bayanin Araqchi, wanda aka yi da sanyin safiyar Alhamis a shafinsa na yanar gizo na dandalin sada zumunta na X, yana mai mayar da martani ga kalaman fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu game da batun kafa “Babban kasar Isra’ila.” A cikin shafinsa na yanar gizo, Araqchi ya yi tambaya cewa: “Shin suna daukan furucin Netanyahu kansa a matsayin mai adawa da wata...
    Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi Allah wadai da kalaman fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ake nema ruwa a jallo a kotun kasa da kasa ya yi dangane da abin da ake kira “Kafa kasar babban Isra’ila”. Wadannan kalamai tana nuna karara aniyar gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasashe masu cin gashin kansu da suka hada da Masar, da Jordan, da Lebanon da kuma Syria, tare da la’akari da su a matsayin babban misali na keta dokokin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa. A cikin wani rubutu da...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran A martaninsa ga fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Kasar Iran a yayin da yake gabatar da wasu takardu kan matsalar karancin ruwa da kuma matsalar fari a yankunan da aka mamaye na Falasdinu, ya bayyana cewa; ‘Yan Nazi na karni na 21, wadanda suka kai hari kan babbar tashar ruwa da ke arewacin birnin Tehran a dandalin Tajrish da makami mai linzami, a yanzu haka suna kokarin yaudarar al’ummar Iran da kofin ruwa da aka yi masa magani. Amma al’ummar Iran a tsawon tarihi, sun dauki ko da mafi gogaggen...
    Babban sakataren kungiya Hizbullahi ta kasar Lebanon ya karbi bakwancin Ali Larijani ya kuma godewa Iran bisa goyon bayan da take baiwa kasar Lebanon da ‘yan gwagwarmaya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Qassem ya gana da Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran da tawagarsa a gaban jakadan Iran a Lebanon Mojtaba Amani. A yayin taron, Sheik Qassem ya jaddada godiyarsa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa ci gaba da goyon bayan da take baiwa kasar Lebanon da kuma ‘yan gwagwarmaya da yakin da suke yi da makiya yahudawan sahayoniyyar Isra’ila da kuma goyon bayan da take baiwa hadin kai da ‘yancin kai na Lebanon da kuma ci gaba...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani matashi mai shekara 18 bisa zargin aikata fashi da makami a jihar. An kama shi ne a garin Kwadon bayan samun sahihin bayani daga jama’a. NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama matashin ne ranar 9 ga watan Agusta, 2025 da misalin ƙarfe 2:30 na rana. Hakazalika, ya ce an samu ƙunshi ganyen da ake zargin tabar wiwi ne. Bincike ya nuna cewa matashin na cikin mutanen da ’yan sanda ke nema game da aikata fashi da makami, waɗanda ake shari’arsu a babbar kotun jihar. A cewar DSP Abdullahi,...
    Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin hanzarta shari’o’i da kuma rage cunkoson gidan yarin. A lokacin ziyarar, ya lura da cewa yawancin fursunonin na zaune a ƙasa babu katifa. Don inganta rayuwarsu, ya umarci a samar musu da katifu 500. Gwamna Sule ya yaba wa jami’an gidan yari da sauran jami’an tsaro saboda sake kama wasu daga cikin waɗanda suka tsere. Ya kuma roƙi jama’a da su kasance cikin shiri su kuma sanar da hukumomin tsaro idan sun ga wani mai kama da wanda ake nema. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya. Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su. Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Galibi dai ’yan ci-ranin da suka fito daga ƙasashen Afirka na ƙoƙarin tsallakawa nahiyar Turai ne domin samun ingantacciyar rayuwa. Ko a ranar Laraba dai ma’aikatan ceto sun ce sun ceto mutum 60 da ransu, wadanda suka hada da maza 56 da kuma mata hudu, sannan aka...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani tsohon malami kuma manomi, Andrew Imuekheme, a Jihar Edo. Lamarin ya faru ne a ranar Talata a garin Ikabigbo, da ke Masarautar Uzairue, a Ƙaramar Hukumar Etsako ta Yamma. Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Rahotanni sun ce Malam Andrew na kan hanyarsa daga gona lokacin da maharan suka tare shi, tare da ɗauke shi zuwa daji. Wata mata da ta tsere daga hannun maharan ta koma cikin gari tare da sanar wa mafarauta, waɗanda suka fara bincike nan take. Tuni jami’an tsaro suka umarci manoma da ke da gonaki a kusa da yankin da su koma gidajensu...
    Wani mazaunin Safana, Iliyasu Sani, ya ce sulhun ya kawo sauƙi ga rayuwar jama’a, domin yanzu suna iya zuwa kasuwa da yin noma ba tare da fargaba ba. Masani a fannin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce talauci da rashin tsaro ne suka sa jama’a neman mafita da kansu. Ya kuma bayyana cewa idan duk ɓangarorin suka tsaya kan alƙawarin da aka yi, wannan sulhu na iya zama mataki na farko na samun zaman lafiya na dindindin a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu tare da tabbatar wa al’ummar yankin ƙudurinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.   A nasa jawabin, gwamnan ya yi kakkausar suka ga hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa a baya-bayan nan, yana mai cewa da gangan maƙiya ke nufin waɗannan munanan ayyuka don yaɗa tsoro a tsakanin al’umma.   “Na ziyarci garin Banga ne domin jajanta wa jama’a game da harin da ‘yan bindiga suka kai a kwanakin baya.   “Lokacin da abin takaicin ya faru, na kasance ba na kusa, amma daga samun labarin, na umarci mataimakin gwamna da ya jagoranci wata babbar tawaga domin ziyarar jaje.   “A jiya ne na dawo...
    Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai.   Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban tattalin arzikin kasa a baya, amma a yanzu, za su karfafa kwarin gwiwar masu zuba jari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran wato (AEOI) Muhammad Eslami ya bayyana cewa babu jada bayana a shirin nukliyar kasar iran, duk tare da takurawar kasashen yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Eslami yana fadar haka a wani taro nay an jarida a nan Tehran a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa kasashen yamma masu babakere kan al-amura a duniya suna son haramtawa mutanen kasar Iran ilmin zamani da kuma ci gaba a fasahar Nukliya. Amma gwamnatin kasar Iran ta dage kan cewa yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar ba zai hana ta ci gaba da shirinta na makamashin nukliya ba. A wani bangare a maganarsa, shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran...
    Hukuma mai kula da sauka da tashin jiragen sama a birnin Paris ya dakatar da wani ma’aikacinsa, wanda yake aikin a bangaren kula da sauka da tashin jiragen sama, saboda ya shelantawa wani jirin HKI wanda ke kokarin sauka a tashar jiragen kan cewa “yanci-yenci Falasdinu”. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar kafafen yana labarai na kasar Faransa na cewa, ma’aikacin ya fadi wadannan kalmomi ne ga matukin HKI wanda ya tashi a tashar ‘Charles de Gaulle’ da ke birnin Paris. Labarin ya kara da cewa matukin jirgin ne ya bada wannan rahoton ga hukumomin kasar Faransa don daukar matakin da ya dace. Ba’a bayyana sunan ma’aikacin ba, amma a jiya talata ce hakan ya auku,...
    Miistan harkokin wajen kasar Masar ya sake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi ta wayar tarho. Kamfanin dillancin labarana Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar na cewa jami’am gwamnatin kasashen biyu da kuma Grossi sun tattauna al-amura da suka shafi sake komawa kan taburin tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya ne bayan yakin kwanaki 12 wadanda HKI da Amurka suka kaiwa kasar Iran. Badar Abdullatf ministan harkokin wajen kasar Masar yana kokarin sake maida dangantakar hukumar AIEA da kuma Iran bayan tayi tsami a watan yunin da ya gabata, inda Iran tana zargin Grossi da hada kai da Amurka...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa ƙudiri zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin neman amincewarta a ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13. Gwamnan, ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wa gwamnati wajen kusantar al’umma, da ayyukan raya ƙasa. Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki Sabbin ƙananan hukumomin da ake shirin ƙirƙira za su fito daga ƙananan hukumomin da ake da a jihar. A cewar gwamnan sabbin ƙananan hukumomin za su mayar da hankali kan samar da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, gina muhalli da sauran muhimman ayyukan jama’a musamman a yankunan karkara. Za su kuma yi aiki tare da masarautu da shugabannin al’umma wajen tabbatar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ɗakin taro na Majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja. Kafin a fara taron, Shugaban Ƙasa ya rantsar da Farfesa Dakas James Dakas da Dakta Uchenna Eugene a matsayin Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki ta Ƙasa da Kwamishina. Majalisar ta kuma dakatar da taron na minti ɗaya domin girmama marigayi Cif Audu Ogbe, wanda ya kasance memba a majalisar a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari, haka kuma a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Cif Ogbe ya rasu a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, yana da shekaru 78.   Daga Bello Wakili  
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Lokaci ya yi da za a amince da takunkumin da bai dace ba a matsayin laifi ga bil’adama Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce lokaci ya yi da za a amince da takunkumin bai daya da Amurka da kawayenta suka kakaba wa Iran a matsayin wani laifi na cin zarafin bil adama. A cikin shafinsa na dandalin X, Araqchi ya bayyana cewa: “Gwamnatocin yammacin duniya a koyaushe suna da’awar cewa takunkumin zaman lafiya ne maimakon yakin zubar da jinni,                 amma gaskiyar tana bayyana wani labari na daban.” Ya yi nuni da wani bincike na baya-bayan nan da aka buga a cikin jaridar The Lancet, wanda ya nuna cewa takunkumin bai-daya-musamman wanda...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar. A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya yaba wa shugabannin NBA bisa hadin kai da kwarewarsu wajen gudanar da aiki. “Na shafe watanni da dama ina bin diddigi da sha’awar yadda kuka kafa, tare da gudanar da ayyukan kungiyar  reshen jihar,  cikin haɗin kai da ƙarfafawa, inda ya zama wata gagarumar kafa wacce ke kare muradun aikin lauya da mambobin ƙungiyar a Jigawa  ma da wajen ta.” In ji shi. “Na...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Masana Iran da suka yi shahada a lokacin yaki babu laifin da suka aikata ban da hidima ga al’ummarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka kan shirun da masu da’awar kare hakkin bil’adama da zaman lafiya da tsaro suka yi dangane da laifukan gwamnatin ‘yan sahayoniyya, yana mai cewa: Masana kimiyyar Iran da suka yi shahada ba su aikata komai ba face hidimar al’ummar Iran a fadin duniya, amma gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe su. Masoud Pezeshkian ya halarci bikin karrama masana kimiyya da suka yi shahada a tsangayar koyar da fasahar nukiliya ta jami’ar Shahid Beheshti a safiyar ranar Talata, inda ya jinjinawa hotunan malaman kimiyya da suka yi shahada...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Lokaci ya yi da za a amince da takunkumin da bai dace ba a matsayin laifi ga bil’adama Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce lokaci ya yi da za a amince da takunkumin bai daya da Amurka da kawayenta suka kakaba wa Iran a matsayin wani laifi na cin zarafin bil adama. A cikin shafinsa na dandalin X, Araqchi ya bayyana cewa: “Gwamnatocin yammacin duniya a koyaushe suna da’awar cewa takunkumin zaman lafiya ne maimakon yakin zubar da jinni,                 amma gaskiyar tana bayyana wani labari na daban.” Ya yi nuni da wani bincike na baya-bayan nan da aka buga a cikin jaridar The Lancet, wanda ya nuna cewa takunkumin bai-daya-musamman wanda...
    Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Iran za ta kasance tare da al’ummar Lebanon a koyaushe Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya tabbatar da cewa: Alakar al’adu tsakanin Iran da Lebanon ta taimaka wajen karfafa alaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu. A cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Beirut a yau Laraba, Larijani ya yi nuni da cewa, Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Lebanon. Larijani ya kara da cewa: Iran da Labanon suna da dadaddiyar wayewa, kuma a ko da yaushe akwai alaka ta kut-da-kut a tsakanin al’ummomin kasashen biyu. Ya kara da cewa, wannan alaka ta al’adu ta haifar da alaka ta musamman tsakanin al’ummomin...
    Wani sabon rikici ya barke a jihar Sokoto inda ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Marnouna da ke karamar hukumar Wurno, inda suka kashe akalla mutum daya tare da yin awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da ake sallar isha.   Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Sokoto, Alhaji Isah Sadik Achida, wanda ya fito daga yankin ya tabbatar da faruwar harin inda ya jaddada cewa maharan sun kuma kashe shugaban kungiyar masu sayar da babura na yankin a yayin farmakin.   Achida ya ci gaba da cewa, kwana biyu kacal kafin harin masallacin, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyuka biyu da ke makwabtaka da su, Gidan Taru da Kwargaba, inda...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kundin tsarin mulki na hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) da asusun samar da ayukka na kasa da kasa (USPF), dukkanin su a karkashin ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani.   A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai ya fitar, ya ce an nada Idris Olorunnimbe a matsayin shugaban hukumar NCC, yayin da Dr. Aminu Waida ya ci gaba da zama mataimakin shugaban zartarwa/Babban jami’in gudanarwa, mukamin da aka nada shi a watan Oktoban 2023 kuma majalisar dattawa ta tabbatar da shi a watan Nuwamba na wannan shekarar.   A baya Olorunnimbe ya yi aiki a hukumar kula da ayyukan yi na jihar...
    Gwamnatin Iraki ta bayyana cewa: Yarjejeniyar da Iran ta kulla da Iraki zata yi gagarumar amfani a fagen tsaron yankin Ofishin jakadancin Iraki a Amurka ya tabbatar da cewa: Iraki kasa ce mai cin gashin kanta kuma tana da hakkin kulla yarjejeniyoyin da kuma yarjejeniyar fahimtar juna. An yi nuni da cewa, yarjejeniyar tsaro da aka rattabawa hannu a baya-bayan nan tsakanin Iran da Iraki ta zo ne a cikin tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da tsaro da kuma kula da kan iyakokin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa: Ofishin jakadancin ya bayyana a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar Iraki INA ya watsa cewa: “A matsayin martani ga kalaman da kakakin...
    Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kama Abubakar Abba, jagoran kungiyar Mahmuda, daya daga cikin manyan kungiyoyin ta’addanci da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi a Najeriya.   An ce an kama shi ne a Wawa da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja inda aka kai shi Abuja domin ci gaba da bincike.   Gwamna Umar Bago ya bayyana matakin a matsayin nuni da irin jajircewar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi na tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan Nijeriya.   Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin babban sakataren yada labaran sa, Bologi Ibrahim, ya ce, “Eh gaskiya ne, zan iya tabbatar da cewa hukumar...
    Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce, “Idan ba a zarge ni wajen binciken gwamnoni da ministocin jam’iyyar da ke mulki ba, bai kamata a zarge ni idan na binciki ’yan hamayya ba.” Duk da haka, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun nuna shakku, tare da tambayar dalilin da ya sa EFCC ba ta ɗauki mataki kan manyan ’yan siyasa na jam’iyyar APC kamar tsohon Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ba. Wasu sun zargi EFCC da yin aiki ƙarƙashin ikon gwamnatin da ke mulki, yayin da wasu suka yi tsokaci ta hanyar buƙtar shugaban EFCC ya bayyana bayanan asusun bankinsa na yanzu. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya. Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki. Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP). Haka...