A ci gaba da kokarinsa na kawo sabon tsari domin inganta harkokin noma a jihar Jigawa, Gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa wani babban taro da manyan masu zuba jari na duniya da masu ruwa da tsaki a harkar noma. Taron wanda ya gudana jiya Talata a otal din Hilton da ke Abuja, ya kunshi wakilai daga kamfanonin SINOMACH, China CAMC Engineering Company Ltd, YTO Group Corporation, da Agra Consortium Ltd, da kuma asusun bunkasa noma na gwamnatin tarayya (NADFUND).

Kyautar LEADERSHIP Ta Kara Zaburar Da Mu Kan Sauke Nauyin Al’ummar Jigawa Akanmu – Gwamna Namadi Kasar Sin Na Yaki Da Cin Zalin Da Amurka Ke Yi Ta Hanyar Dora Haraji Ne Bisa Sanin Ya Kamata Taron ya samar wa Gwamnatin Jihar Jigawa wani dandali na baje kolin kayayyakin gona da jihar ta yi fice akansu ga masu saka hannun jari, wanda ya bayyana tsare-tsaren kawo sauyi da nufin mayar da Jihar Jigawa a matsayin babbar cibiyar kasuwancin kayayyakin gona da bunkasa masana’antu a Nijeriya. Jihar na fatan samun hannun jari a bangaren Kamfanin hada takin zamani domin inganta harkar noma, kamfanin harhada Motocin noma na YTO, aiwatar da aikin noman rani a fadin hekta 600 da ke Hadejia, kamfanin Integrated Halal Products Hub, Mayankar dabbobi ta zamani mai karfin yanka dabbobi 2,500 a kullum da dai sauransu. Tunda farko, a nasa jawabin, Gwamna Namadi ya yi maraba da tawagogin manyan kamfanoni da suka zo don halartar taron baje kolin kayan gona na jihar Jigawa a babban birnin tarayya Abuja. Gwamna Namadi ya jaddada amfanin noma na Jigawa, inda ya ce kashi 80 cikin 100 na kadada miliyan 2.47 na jihar gonaki ne na noma, wanda ya hada da ruwa 242 da kuma Kasuwar Dabbobi ta Maigatari, wacce babu sama da ita a Afirka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 

Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Hajj 2025: Kaduna Ta Gaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
  • An Fara Baje Kolin Kayakin Da Ake Kerawa A Iran Tare Da Taron Iran Da Afirka Karo Na Uku
  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Shugaban Kasar Yana Maraba Da Masu Zuba Hannun Jari A Kasarsa Daga Kasashen Waje
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137