Cutar sanƙarau ta yi ajalin mutum 3 a Gombe
Published: 28th, March 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum uku daga cikin 33 da suka kamu da cutar sanƙarau a jihar.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ne, ya bayyana hakan yayin ƙarin haske game da ɓullar cutar a jihar.
Majalisa ta janye ƙudirin tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a KebbiYayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu rahoton mutum 53 da ake zargi sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi hudu: Kaltungo, Yamaltu Deba, Billiri, da Gombe.
A cewarsa, an tabbatar da mutuwar mutum uku daga ƙananan hukumomin Kaltungo, Yamaltu Deba, da Billiri.
A Shongom kuwa, daga cikin mutum huɗu da ake zargi sun kamu da cutar, an tabbatar da uku na ɗauke da ita.
Sai kuma ƙananan hukumomin Dukku da Nafada, inda aka samu mutum ɗaya kowanne, amma ba a tabbatar da sun kamu ba.
Kwamishinan, ya ce gwamnatin Gombe, ta samar da magunguna kyauta domin kula da masu cutar a cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a ƙananan hukumomi 11 na jihar.
Ya bayyana cewa alamomin cutar sun haɗa da zazzabi, ciwon wuya, da ciwon kai mai tsanani.
Ya kuma shawarci jama’a da su kiyaye tsafta, guje wa zama a ɗakuna marasa iska, da kuma nisantar masu alamomin cutar domin hana yaɗuwarta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sanƙarau tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar.
Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna.
Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a BornoDa yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na ilimi, noma, kiwon lafiya, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa.
“Babu wani sashe a jihar da aka bari a baya a cikin ayyukan ci gaban da Gwamna Mai Mala Buni ke aiwatarwa,” in ji Adamu.
A nasa martanin, Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Barde Gubana, ya wakilta, ya karɓi karramawar a matsayin “hanyar mayar da martani mai ƙarfi” da ke tabbatar da tasirin gwamnatinsa a matakin farko.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin kai Yobe matsayin jiha da za ta iya gogayya da takwarorinta a fagen ci gaban ƙasa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ’yan siyasa daga ciki da wajen jihar, da kuma sarakunan gargajiya.