Al’ummar Yemen sun sha alwashin tsayin-daka kan barazanar Trump
Published: 17th, March 2025 GMT
Al’ummar kasar Yemen sun gudanar da wani gagarumin ganganmi a fadin kasar, inda suka lashi takobin tinkarar ta’addancin Amurka ta hanyar kara karfin soji, da hada karfi da karfe, da kuma abokan gaba shakat.
Gangamin ya zo ne bayan da jagoran gwagwarmayar kungiyar Ansarullah Abdul Malik al-Houthi ya bayyana cewa kasar a shirye ta ke duk wata barazanar Amurka.
“Ba mu tsoron kowa, kuma ba mu rusuna wa kowa sai Allah. Za mu fuskanci duk wani tashin hankali. ” inji shi
“A shirye muke mu tunkari dukkan azzaluman duniya ba tare da wata fargaba ko tsoro ba.
Abdul Malik al-Houthi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a ranar Lahadi, kwana guda bayan da Amurka ta kai wasu jerin hare-hare a Sanaa babban birnin kasar Yemen da wasu larduna da dama a fadin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da suka hada da mata da kananan yara.
A yammacin ranar Asabar jiragen yakin Amurka da na Birtaniya sun kai hare-hare 47 a wurare da dama a Sanaa babban birnin kasar, da kuma wasu yankunan lardin Saada da ke arewacin kasar, da lardin al-Bayda da ke tsakiyar kasar, da kuma lardin Dhamar da ke kudu maso yammacin kasar, inda akalla mutane 31 sukayi shahada.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp