Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali
Published: 31st, January 2025 GMT
Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali.
Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar yanayin.
Gwamnatin yankin ya bayyana cewa ajali ya rutsa da su ne a ƙauyen Danga, a cikin wani rami mai ruwa da laka, wanda zaftarewar ƙasar ta binne su a ciki a ranar Laraba.
Ta bayyana a shafinta na Facebook cewa “abin takaicin shi ne babu ko mutum ɗaya da ya tsira a cikin su.”
Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai JigawaJami’in kula da haƙar ma’adanai a yankin, Ousmane Diakite, ya bayyana cewa, “akalla mutum 10 ne abin ya yi alajinsu.”
Wani jami’in gwamnati da ya nemi a bole sunansa ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akwai yiwuwar adadin zai karu, a yayin da hukumomi ake ci gaba aikin ceto.
Magajin wani gari da ke maƙwabtaka da Koulikokro, ya bayyana wa AFP cewa, “babu wanda ya tsira bayan faruwar lamarin.”
Mali na daga cikin ƙasashe mafiya talauci a duniya, duk da cewa tana cikin ƙasashen mafiya arzikin zinare a nahiyar Afirka.
Zaftarewar ƙasa na yawan halaka masu haƙar zinare a ƙasar, a yayin da hukumomi ƙasar ko ƙoƙarin kawo ƙarshen amfani da hanyoyin gargajiya wajen gudanar da harkar.
A watan Janairun 2024 zaftarewar ƙasa ta kashe masu halartar zinare 70 a wurin da na ranar Larabar nan ya faru.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: haƙar zinare masu haƙar zinare
এছাড়াও পড়ুন:
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.
Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.
Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da AmurkaA cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.
“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.
Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.
“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.
Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.
“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.