2025-09-17@21:56:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2944
«Fassara»:

Pezeshkian: Dole Kasashen Musulmi Da Na Larabawa Su Fito Fili Su Yi Allah Wadai Da Harin Isra’ila Kan Qatar
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kasashen musulmi da na Larabawa su yi Allah wadai da yin tir da harin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Qatar Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga ‘yan uwanta na kasar Qatar, yana...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan kasar Qatar laifi ne da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kakkausar murya ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan kasar Qatar, tana mai jaddada cewa, harin da...
Sabanin yadda wasu kasashe ke tayar da takaddamar cinikayya da kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da tsarin samar da kayayyaki a duniya, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen ganin duniya ta samu ci gaba, musammam kasashe masu tasowa, ta hanyar bude kofa da yin komai cikin adalci. A duk inda aka...
An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya. Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun...
Cikin shekarar 2024, an kafa sabbin kamfanonin 59,000 masu jarin waje a kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 9.9 bisa dari kan na 2023. Wani rahoto da ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta fitar a wajen bikin baje kolin cinikayya da zuba jari karo na 25 dake gudana a birnin Xiamen ya...
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu nasarar warware tankiyar da ke tsakanin Matatar Dangote da Ƙungiyar Ma’aikatan Dakon Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG). Wannan na zuwa ne bayan wani zama da aka gudanar a babban ofishin DSS da ke Abuja, inda rahotanni ke cewa shugabannin NUPENG sun umurci mambobinsu da su...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin sun shigo cikin al’umma sanye da hijabai sun yi garkuwa da mutane 11 ciki har da masallata guda uku a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadin da ta gabata a garin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru, kamar yadda rahotanni daga shafin Zagazola Makama suka...
Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin Qatar a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar Hamasa a yau Talata. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotterre ya yi tir da...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi watsi da abinda yazo cikin bayanin bayan taro na kungiyar kasashen Larabawa na cewa tsiran Abu Musa da Tumb babba da karami mallakin UAE ne. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran na fada a cikin bayanin da...
Ya yi nuni da cewa, dokar za ta bukaci umarnin fara aiki daga ministan kudi kamun a fara. Edun ya ce, dole ne gwamnati ta zauna tare da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kafin aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Yayin da ake gab da yin bikin ranar malamai ta kasar Sin karo na 41 nan ba da jimawa ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da martanin wasika ga wakilan malamai na musamman a duk fadin kasar, inda ya bayyana fatansa tare da mika gaisuwar ranar ga malamai da ma’aikata a bangaren ilmi...
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki dangane da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ɗauka na ƙara harajin kaso 5 cikin 100 a farashin duk litar man fetur. A yayin da ƙungiyar ta yi watsi da matakin, ta kuma kwatanta aiwatar da hakan a matsayin ganganci da mugunta...
Iyalan wani jami’in sibil difens mai suna DSP Adama Adekunle Emmanuel, mai shekaru 45, sun ce suna zargin abokin aikinsa ne ya harbe shi har lahira a ranar Lahadi a wani otel da ke Abuja. Matar marigayin ta ce alamu sun nuna an kashe mijinta ne, saboda an samu raunukan harbin bindiga a kafaɗunsa. Gini...
Idan Afirka Ta Kudu ta yi nasara yau, za ta tabbatar da zuwa gasar Kofin Duniya da za a buga a Arewacin Amurka a 2026, kuma karo na farko tun bayan 2010 lokacin da ta ɗauki nauyin gasar. Nijeriya kuwa, wadda ta halarci gasar sau shida a baya, tana ƙoƙarin dawo da martabarta. Nasarar da...
El-Rufa’i ya jaddada cewa manufarsa ita ce ganin an tabbatar da gaskiya da bin doka a ƴansandan Nijeriya, domin tabbatar da jami’an suna aiki da gaskiya da biyayya ga ƙa’ida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Majalisar dokokin Faransa ta kada kuri’ar yankan kauna wadda ta kawo karshen gwamnatin Firaministan kasar Francois Bayrou. Yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri’ar yanke masa kauna da kashi biyu cikin uku a jiya Litini. Bayrou dai ya shafe watanni 9 kacal akan wannan kujera a matsayin Firaminista na shida karƙashin shugabancin Emmanuel Macron da...

Gwamnatin Tarayya, NUPENG Da Ɗangote Sun Fara Tattaunawa Don Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Ma’aikatan Mai
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC). Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu...
Yarima Harry wanda ya koma rayuwa a Jihar California ta Amurka, ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, a fadar Windsor da ke yammacin birnin Landan a ranar Litinin. Shekaru uku ke nan daidai da rasuwar Sarauniya Elizabeth II wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga Satumba, 2022, kuma aka binne ta...
An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan da ya yi murabus, inda tsohon Ministan Harkokin Waje ya bayyana takarar neman kujerar mai tasiri a kasar wadda take sahun gaba na kasashe masu arziki a duniya. Tsohon Ministan Harkokin Wajen kasar Japan, Toshimitsu Motegi ya zama mutum na farko da ya nemi ’yan majalisar dokoki...
Kwamitin ya kuma jaddada buƙatar wayar da kan jama’a da kamfen ɗin mutunta kai, da haɗa ɗabi’a mai kyau a cikin kundin karatu, da ɗaukar iyaye da ke taimaka wa ‘ya’yansu wajen magudi a matsayin masu laifi. Kwamitin ya gargadi cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za a ci gaba da lalata...
Tawagar kasar Iran ta maza da mata a wasan wushu a bangaren sanda da taolu ta samu gagarumar nasara inda ta samu lambobin yabo guda guda 10, zinariya 6 Azurfa guda 2 sai kuma tagulla guda 2, a wasan zakarun na washu karo na 17 da aka gudanar a kasar brazil, Gasar Wushu ta duniya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen dakatar da ta’addanci kan al’ummar Falasdinu Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Lahadin da ta gabata cewa, tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka...
Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke ƙara tsada yayin komawan ’ya’yansu makaranta a sabuwar shekarar karatu. Makarantu na ƙara ɓullo da sabbin hanyoyin karɓar kuɗi daga hannun yara da sunan koyarwa. NAJERIYA A YAU: Yadda ake gudanar da bukukuwar Sallar Gani yayin Mauludi DAGA...
Saboda tsabar gudunsu da kuma zilliya inda suke da sauri ninki biyar na gudun sauti makamai ne da ka iya sauya yadda ake fafata yaki a yanzu. Hakan ta sa yanzu kasashe ke rige-rigen samar da su. Rasha, China, Amurka: rigegeniyar nuna iko Bikin faretin na Beijing ya jawo rade-radi game da barazanar da China...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da sabon harin da Boko Haram suka kai a Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama; ciki har da sojoji. Atiku, ya bayyana halin da ’yan Najeriya ke shiga sakamakon hare-haren ta’addanci. Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna ...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Darajamal da ke Ƙaramar Hukumar Bama, domin jajanta wa iyalan mutanen da Boko Haram suka kashe. Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun hallaka aƙalla mutum 63, yayin da dakarun soja suka kashe 30 daga cikinsu. Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake...
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnati, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta sake duba mafi ƙarancin albashi, domin Naira Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ta isa wajen tafiyar da al’amuran yau da kullum. A cewarsu tashin farashin kayan abinci, sufuri, haya, da wutar lantarki ya ƙara jefa su cikin wahalar da rayuwa....
Sojojin runduna ta 6 da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, sun gano wata mafakar ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai da dama a ƙauyen Ikyaior da ke ƙaramar hukumar Wukari, a kan iyakar Taraba da Benuwai. Bayanan sirri da sojojin suka samu ne suka taimaka musu wajen kai farmakin da ya kai ga gano...
Ƙungiyar masu dakon Man Fetur da Gas (NUPENG) ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin kasa baki daya daga ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025, domin nuna adawa da abin da ta kira tsauraran matakan kin amincewa da kungiyar da Kamfanin matatar Dangote ke yi. NUPENG ta zargi kamfanin da daukar direbobin da...
Babban sakataren hukumar samar da hadin kai takanin mazhabobin musulunci hujjatul islam shahriyori ya sanar cewa a gobe litinin 8 ga watan satumba ne zaa bude taron makon hadin kai na 39 a nan birnin Tehran inda zai samu halartar malamai sama a 80 da baki 210 da kuma masu rajin kare hakkin bil adama...
A jawabin ‘yan jaridu wanda darekta na bangaren manema labarai da al’amuran da suka shafi jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya Folasade Boriowo, abin ya bayyana; “A sashen Firamare , ‘yan aji 1- 3 za su byi darussa 9–10, su kuma wadanda suke aji 4–6 zasu yi darussa 10–12.Sai bagaren karamar Sakandare, abin ya fara...
Zulum, wanda ya yi matukar takaici da harin, ya gana da shugabannin al’umma tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Shugaban yace jihar Kaduna itace akan gaba daga cikin jihohi 36 da Birnin tarayya Abuja wajen tara kudin fatun layya Wanda ta tara Naira miliyan 23 sai jihar Kebbi wacce tazo ta biyu da Naira milliyan 21 sai kuma jihar Sakkwato wacce tazo ta uku. Yace kudadan da aka tara za’ayi amfani dasu wajen...
“Abin da Jibrin ya faɗa ba wai adawa da jam’iyya ba ne. Kowane ɗan siyasa yana da ‘yancin sauya jam’iyya. Ko Shugaba Bola Tinubu ya taɓa sauya jam’iyya kafin ya zama shugaban ƙasa,” in ji Doguwa. Ya kuma gargaɗi Dungurawa da ya daina korar ‘ya’yan jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba, inda ya ce za su...
Yawancin waɗanda aka kashe sun fito ne daga sansanin ’yan gudun hijira da ke Makarantar Sakandare ta Kimiyya ta Gwamnati. Wata majiyar ta ce: “Aƙalla mutanen gari 56 da sojoji biyar aka kashe. An ƙone gidaje fiye da 20 da kuma motoci 10. Har yanzu ana neman wasu da suka ɓace.” Har yanzu, babu wata...
Ana zargin mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Darul Jamal da ke Karamar Hukumar Bama, a Jihar Borno, inda suka kashe gomman mutane da sojoji. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Juma’a. ’Yan bindiga sun kashe mutum 7 a Katsina Yadda makarantu ke tatsar kuɗaɗe daga iyayen ɗalibai Mutane...
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa da dama sun bayyana bacin ransu kan barazanar da ministan yakin Isra’ila ya yi na bude “kofofin jahannama” a zirin Gaza. Wannan martanin ya zo ne a ranar Juma’a bayan da Isra’ila Katz ya ayyana cewa gwamnatin sahyoniyawan na gab da maida yankin jahannama a gabar tekun. Katz, ya bayyana cewa sojojin...
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe mutane bakwai, yayin wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen. Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta...
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga bakwai sun mutu a wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen. Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar...
An ce saurayin ya yi wa Ammaye wasa da cewa yana son aurenta domin “cika Sunnah”. Sai dai kuma an ce Ammaye ta yi wata magana da aka dauka a matsayin Batanci. Wannan ne ya fusata matasan yankin. Lamarin aka kai shi fadar Dagacin Kasuwar Garba, inda aka yi mata tambayoyi, kuma a cewar rahoto...
Jam’iyyar NNPP ta Jihar Kano, ta kori Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji. Jam’iyyar ta zarge shi da yi mata zagon ƙasa da kuma gaza biyan kuɗaɗen da ake binsa. ’Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC 8, sun sace ɗan China a Edo APC ta yi barazanar hukunta “Yaran Badaru” a...
Ya kara da cewa, saboda haka; akwai bukatar a kara yawan hektar noman kwakwar manjar zuwa hekta akalla 500,000, domin cike gibin bukatar da ake da ita a kasar nan tare kuma da kara bunkasa nomanta a Nijeriya baki-daya. Shugaban ya ci gaba da cewa, har yanzu a Nijeriya ana ci gaba da fuskantar samun...
Ya kuma sanar da ci gaba da bai wa shugabancin Dakta Dantsoho goyon baya, musaman domin kara samar da sauye-sauyen da za su kara bunkasa hada-hadar zirga-zirga, da kuma a bangaren kara bunkasa kasuwancin tatalin azrki na Teku. A nan kuma Kamfanin Rukunonin SIFAD, ya taya Dakta Dantsoho murnar zama Mataimakin Shugaban na kungiyar ta...
Kungiyar ‘Movement for North East Organization Forum’ ta yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya yi hattara na yin katsalandan game da yakin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi daji. Shugaban Kungiyar, Alhaji Abdulrahman Buba Kwacham, wanda kuma shi ne Sarkin Fulanin masarautar Mubi a Jihar Adamawa, shi...
Ya yaba da jajircewar Gidauniyar Abdullahi Maikudi, yana mai kira ga sauran masu kudi da kungiyoyi su yi koyi da wannan aiki na alheri. Ya kara da cewa a matsayinsa na dan arewa, ba zai daina fafutukar ganin matasa sun samu damar da za ta inganta rayuwarsu ba. A yayin taron, daliban da aka dauki...
Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar. A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta...

Kwamitocin Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinu Sun Bayyana Barazanar Katz A Matsayin Kira Ga Kisan Kare Dangi
Kwamitocin kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya sun bayyana barazanar Katz da cewa; Kira ne ga aiwatar da kisan kare dangi da kuma shafe wata al’umma Kwamitin kungiyoyin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa ya tabbatar da cewa: Kalaman ministan tsaron Isra’ila Katz game da “bude kofofin jahannama” kan birnin Gaza ya zama kira ga jama’a na Aiwatar da kisan kiyashi,...