2025-11-03@09:48:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2593
«mai kwashe shara»:
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
An bayyana cewa mahalartan EIMC 18 sun fito ne daga hukumomin tsaron Nijeriya da kuma ƙasashen Afrika kamar Chadi, Ghana, Rwanda, Somalia, da Gambiya. A cikin laccarsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa salon Zamfara ta zama abin koyi ga sauran sassan Afrika wajen nazarin yadda ake ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ci gaba....
Lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya gabatar da ƙarar neman a kwace kuɗin, yana sanar da kotun cewa, ICPC ta bi umarnin wucin gadi na kwace dalolin da ta yi a baya. Ya ce, an buga sanarwa ta jama’a inda aka gayyaci duk wani mutum wanda yake ganin akwai dalilin da zai hana ko kuma bai...
Gwamnatin Jihar Gombe, ta fara aikin tantance ma’aikata sama da 7,000 ta hanyar Intanet domin tabbatar da bayanansu da kuma kawar da ma’aikatan bogi. Shugabar Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar (CSC), Hajiya Rabi Shu’aibu Jimeta, wacce ke jagorantar aikin, ta ce wannan shiri na nufin tabbatar da sahihancin bayanan ma’aikata. An kashe mutum 2...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta ceto wata jaririya da ba ta wuce mako daya da haihuwa ba, da aka sayar kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi, tare da cafke mata huɗu da ake zargin su da hannu a cinikin. Kakakin rundunar a jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa...
Mummunan cin zarafi a birnin El Fasher na kasar Sudan ya haifar da tofin Allah tsine da Allah wadai daga al’ummomin ƙasashen duniya da na cikin gida Kisan gilla da laifukan da ake aikatawa kan fararen hula a El Fasher, Arewacin Darfur, sun jawo Allah wadai daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin dan...
Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu. Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.” A watan...
Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu. Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.” A watan...
“’Yan majalisa suna kuma fuskantar barazana daga wasu ‘yan yankunansu da ke samun damar shiga ofisoshinsu ba tare da izini ba.” Ya ƙara da cewa idan aka kasa magance waɗannan matsalolin tsaro, hakan na iya kawo cikas ga gudanar da ayyukan majalisar kamar wakilci, sa ido, tattaunawar kasafin kuɗi da zaman majalisar, wanda zai iya...
Sanusi ya ƙara da cewa da an cire tallafin a shekarar 2012, da talakawa wahala kaɗan za su sha a wancan lokacin. Haka kuma, ya soki shugabannin Nijeriya, yana cewa da yawa daga cikinsu suna mantawa da nauyin da ya rataya a wuyansu bayan sun hau mulki, suna fifita buƙatunsu maimakon jin daɗin jama’a. ShareTweetSendShare...
A zantawarsa da manema labarai, jagoran tafiyar Shelkh Umar Shehu Zaria wanda kuma shi ne, babban limamin Masallacin Mus’ab Ibn Umair, Sun jaddada cewa, su ba su da wani buri na daban face ganin an samu zaman lafiya, hadin kai, da mutunta juna a tsakanin mabiya addinai da jama’ar Kaduna baki daya. “Wadannan malamai...
Sanarwar ta ce, wannan horo mai taken ‘Computer Appreciation Training’ an shirya shi ne ta Hukumar Fasaha da Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), a matsayin babban taron ƙarawa juna sani ga manyan jami’an gwamnati. A jawabinsa yayin buɗe shirin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa wannan horo wata muhimmiyar hanya ce wajen cimma burin gwamnatinsa na...
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, wasu manoma uku da makiyayi daya sun samu kananan raunuka. Ya kara da cewa an tura ‘yansanda da ‘yan banga na yankin don dawo da zaman lafiya. Kakakin rundunar ‘yansandan ya kuma ce, sun kama mutane 17 da ake zargi da...
“Bayan gano alamun karkatar da kudaden tallafin a matakin farko, mun gabatar da matakai don tabbatar da cewa kudin ya isa ga wadanda aka yi niyya,” in ji shi. Wasu daga cikin matakan da aka dauka sun hada da kafa kwamitin mambobi 20 a kowace karamar hukuma, wanda ya kunshi sarakunan gargajiya, shugaban...
Shugaba Tinubu, a cikin wasikarsa, ya ce, an yi nadin ne bisa tanadin Sashe na 18(1) na Dokar Sojojin Kasa, Cap A20, ta Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004. Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da wannan bukatar don gaggawa kan tabbatar da daidaito mai inganci a cikin tsarin tsaron kasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Bugu da kari, an shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun...
Ya ba da shawarar a mayar da wajen ayyukan al’umma kamar filin motsa jiki ko ɗakin taro maimakon a sayar shi. Kiru, ya buƙaci gwamnan jihar da ya ɗauki alhakin kura-kuran da aka tafka a wajen wannan aikin, tare da tabbatar da cewa irin wannan kuskure ba zai sake faruwa ba a nan gaba, musamman...
Mazauna ƙauyukan Bazar da makwabtansu a Karamar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato, sun koka cewa ’yan bindiga sun kakaba musu harajin Naira miliyan 15 tare da barazanar kai sabbin hare-hare idan ba a biya ba. Wadannan ƙauyuka suna yankin Mazabar Sanatan Kudu ta Kudu, inda tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ke wakilta. Wani...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan kasar. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin...
Wakil, ya gargaɗi masu yaɗa labaran ƙarya da su daina, yana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci bisa dokar laifuka ta amfani da kafafen sadarwa. Ya tabbatar da cewa ba a ƙone gidan shugaban jam’iyyar PDP ba, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin. Ya shawarci mazauna yankin da su ci...
An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu. Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa October 27, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025
Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu. Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin. Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro...
Da yake miƙa takardar naɗin, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo, ya taya sabon Sarkin murna, tare da kira gare shi da ya bi dokokin gwamnati da na ƙasa wajen gudanar da mulkinsa. Ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar da naɗin ne bayan ta binciki cancanta, da halayya, da tarihin mulki na sabon Gung...
Duk makarantu a fadin ƙasar Mali da ke Yammacin Afirka za su ci gaba da kasancewa a rufe daga ranar 27 ga Oktoba zuwa 9 ga Nuwamba, sakamakon tsananin ƙarancin man fetur da ya janyo tsaikon harkokin sufuri da na yau da kullum. Ministan Ilimi na ƙasar, Amadou Sy Savane ya sanar a ranar Lahadi...
Wannan tabbacin ya zo ne a daidai lokacin da farashin famfon mai ke canzawa a faɗin ƙasar, wanda tun daga kusan ₦189 a kowace lita a shekarar 2023 zuwa sama da ₦1,000, kafin ya daidaita tsakanin ₦800 da ₦900 a farkon shekarar 2025. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Zaɓi Birgediya Janar Yake A...
Tsohon gwamnan, wanda ya dade yana cikin jam’iyyar PDP kuma fitaccen mai fada a ji a cikin jam’iyyar, yana neman jagorantar jam’iyyar yayin da take shirin yin babban taronta na kasa. Ana sa ran jam’iyyar PDP, wacce ta mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2015, za ta zabi sabon Shugabanta na kasa da sauran shugabannin...
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matukar bakin ciki game da wannan lamarin. Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ya yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasu da kuma dukkan al’ummar Nafada, yana addu’ar Allah ya jikan mamatan. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Duk da saukar farashin abinci a kasuwanni a sassan Najeriya, manoma na kokawa cewa sun shiga damuwa saboda asarar da suka tafka na kuɗaɗen da suka kashe wajen noma gonakinsu, lamarin da suka ce ya rage musu ƙwarin gwiwa su ci gaba da sana’ar. Wasu daga cikin manoman da wakilinmu suka zanta da su sun...
Matatar Dangote ta sanar da shirin ƙara ƙarfin sarrafa man fetur daga ganga 650,000 zuwa miliyan 1.4 a kowace rana, wanda zai sanya ta zama babbar matatar mai mafi girma a duniya. Shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Legas, yana mai cewa faɗaɗawar na nuna ƙwarin gwuiwa ga...
Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Frank Ogunojemite, ne ya sanya rattaba hannunsa a wasiƙar kamar yadda Jaridar PUNCH, ta samu kwafinta. Shugaba ya bayyana cewa, ya kafa hujjar buƙatar soke tsarin, kan ƙalubalen da take fuskanta, na kashe kuɗaɗe masu yawa, musamman wajen safarar mayan Kwantainonin da ake shigoa da su daga ƙasashen da ke a...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal, Abdussamad Dasuki, ya ce ba zai tsaya takara a zaɓen 2027 ba. Dasuki, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin bai wa matasan Najeriya damar shiga harkokin mulki. El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2 Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya...
Ya ƙara da cewa Basira ‘Yar Guda ta bayyana cewa za ta amince da aure ne kawai idan Idris ya mallaki gidansa na kansa, ba wanda yake haya ba. Wannan ne ya sa kotu ta dakatar da yanke hukunci domin bai wa Hisbah damar tabbatar da cewa an bi tsarin aure yadda ya dace da...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta doke babbar abokiya hamayyarta, Barcelona da ci 2 da 1 a filin wasa na Bernabeau. Wasan tsakanin manyan ƙungiyoyin biyu shi ne wasa mafi girma na hamayya a duniya. Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunwa ta diflomasiyya da Amurka domin cimma “mafita kan batun nukiliya cikin mutunta juna. “Iran ta sha sanar da cewa ba ta taba yin watsi da diflomasiyya ba kuma,” in ji Araghchi a wata hira da akayi da shi. “Ba za...
A birnin Paris, an gudanar da wata zanga-zanga a filin jirgin saman Roissy-Charles-de-Gaulle game da shigar da makamai da kayan aikin soja na Faransa zuwa Isra’ila. An shirya zanga-zangar ne bisa kiran wasu kungiyoyi da nufin bayyana rawar da Faransa ke takawa wajen samar wa sojojin Isra’ila makamai da kayan soji, musamman ta babban filin...
Sai dai ya yabawa masu ba da agajin gaggawa, da jami’an tsaro da kuma ‘yan sa-kai da suka yi aiki tuƙuru wajen ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da ba su agaji, yana mai cewa ɗaukin gaggawan da suka kai ya taimaka wajen rage munin ibtila’in. A yayin da take addu’ar Allah ya...
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i. Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000...
Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru...
“Ban taba tunanin zan zama taurariya a duniya ba.” Daga Yobe Zuwa Fagen Duniya An haife ta a Jihar Kano kuma ta tashi a Yobe, labarin Nafisa ba shi da wuya kamar yadda yake da ban sha’awa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya, kuma mijin mahaifiyarta mai suna Alhaji Yusuf Umar Kaigama ya rene ta,...
A gun cikakken zaman taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20 da aka gudanar tun daga ranar 20 zuwa 23 ga wannan wata a nan birnin Beijing, an yi bincike da zartas da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda aka gabatar da jagora da burika...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa a harkar tsaron sararin samaniya, domin hana ’yan ta’adda na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare. Zulum, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a garin Mafa, bayan wani hari da Boko Haram suka kai. Sauke Hafsoshin Tsaro: Za...
A shekarar 2008, Skales ya shiga gasar Zain Tru Search kuma ya lashe yankin ArewaTsakiya na gasar. A lokacin, ya riga ya saki waƙarsa ta farko “Must Shine”, wacce ta samu yawan fitowa a tashoshin Rhythm FM a Lagos, Jos, da Abuja. Ana tuna shi da burinsa na zama babban mawaƙi da sha’awar ilimi, ya...
Mataimakin babban kwamandan rundunar sojin Iran kan hadin gwiwa ya jaddada cewa: Sojojin Iran a shirye suke su fuskanci kowace barazana Mataimakin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Iran kan Hadin Gwiwa, Rear Admiral Habibullah Sayyari, ya ce: An zabi Sojojin Iran daga cikin mafi kyawun matasa a kasar kuma suna shirye su fuskanci kowace barazana. A...
Mazauna unguwar Tudun Wada da ke garin Shendam a Jihar Filato sun zargi wasu jami’an ’yan sanda da ba wa ’yan daba kariya wajen rusa gidajensu. Shaidu sun ce sama da ’yan sanda 100 ɗauke da makamai ne suka isa yankin da misalin karfe 5 na safiyar Laraba, suka ba wa wasu ’yan daba kariya...
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa su na nazarin dokoki guda 69 da kuma buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙudirin ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278 bisa ga tsarin kundin mulkin 1999. Barau, wanda shi ne shugaban Kwamitin Bita na Tsarin Mulki a majalisar dattawa, ya bayyana hakan ne a taron haɗin...
Rashin Biyan Yan-fansho Bisa Lokaci Ta tabbata a lokacin mulkin Kwankwaso, “yan fansho a Kano, kan jira tsawon Watanni zuwa Shekaru ba tare da an biya su hakkokinsu na barin aiki ba. Haka ɗan-jummai Ganduje, yakan dan fara biyan hakkokin “yan fanshon, sai kuma a ga ya watsar. Sai a dauki tsawon lokaci yana ɓaɓatun...
Kungiyar kwallon kafa ta “Futsal” ta matan Iran ta zura kwallaye 14-0 a wasan da ya hada ta da takwararta ta kasar Bahrain mai masaukin baki. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka bude wasannin nahiyar Asiya na kwallon kafar Futsal a kasar Bahrain. A wasan farkon, kungiyar ta Iran ta sami...
Ya bayyana cewa sarakuna suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba, musamman a fannin ilimi, inda ya ce zai tabbatar yara sun koma makaranta. Haka kuma, ya ce zai goyi bayan gwamnati a ɓangaren kiwon lafiya da tsaro, domin inganta rayuwar jama’a. Sabon Sarkin, wanda kuma shi ne shugaban hukumar kula da ilimi a...
Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) za ta jagoranci kwamitin, domin ita ce ke da ikon tattara bayanan ma’adinai na ƙasa baki ɗaya. “NGSA ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kaduna bisa gaskiya da bayyana bayanai, tare da yin kira da a gudanar da binciken tabbatarwa mai zaman kansa,” in ji shi. Ya...