2025-05-13@08:59:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 536
«Lafiyar Zuciya»:
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi yana shirin kai ziyara a kasashen Pakistan da Indiya a wannan makon a wani bangare na tuntubar juna tsakanin Tehran da kasashen yankin. Ministan harkokin wajen Iran din zai isa Pakistan a ranar Litinin 5 ga watan Mayu, domin tattaunawa da manyan jami’an kasar. Tattaunawar za ta mayar da...

Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Suka Kai Kan Kasar Siriya
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan kasar Siriya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi Allah-wadai da harin bam da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Siriya a ranar Asabar. A cikin wata...
A yanzu kuma, Amurka na son kawar da dimbin gibin kudaden asusunta, ta hanyar amfani da kare-karen haraji. A baya Amurka ta yi kokarin hakan ba tare da cimma nasara ba, kuma a yanzu ma hakan ne zai sake faruwa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama mutane 95 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri. An kama mutanen ne a wani farmaki da aka kai kan masu aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin asiri a garin Benin City da kewaye a makon da ya gabata. Kwamishinan ’yan sanda, Monday Agbonik, ya bayyana cewa an...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa...
Barcelona ce ta yi nasara a wasan na El Clasico da cin 3-2, sannan ta lashe Copa Del Rey na 32 jimilla ranar Asabar. Daga baya Rudiger ya nemi afuwa, sai dai hukuncin laifin da dan wasan tawagar Jamus ya aikata, za a iya dakatar da shi daga buga wasa hudu zuwa 12, amma sakamakon...
A cewar kakakin shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, “Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta fitar da jadawalin ayyuka na babban zaben shekarar 2027 ba, inda ta kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su yi yakin neman zabe a bainar jama’a, don haka bai dace ba, kuma ya saba wa doka, a ce...
Shugaban INEC ya jaddada muhimman ci gaban da ya samo asali daga sauye-sauyen da suka gabata da suka hada da fadada jaddawalin zabe, gyare-gyare don ba da damar kwanaki 180 tsakanin zaben fid da gwani na jam’iyya da zabe daga kwanaki 60 ya warware jinkirin kayan aiki. Ya ce wannan ya tabbatar da cewa...
Ƙungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta shaida wa masu sukar Shugaba Bola Tinubu cewa zai yi wa’adi biyu ne a kan karagar mulki. Kungiyar ta kuma ce rashin adalci ne a hana Tinubu ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027, ganin cewa jigo a Arewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a baya ya yi cikakken...
Hukumar ta FIRS ta yi gargadin cewa duk bankunan da ke shiga cikin tsarin tattarawa, kudaden da ake aikawa da su, da kuma tsarin sasantawa dole ne su bi wannan umarnin ba tare da bata lokaci ba, su daina amfani da asusun da ba su izini, sannan su tabbatar da cewa ana sarrafa hada-hadar kudaden...
Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin. A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a...
Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Comr. Muhammad Haruna Ibrahim ya bukaci gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta biyan ‘yan kungiyar SSANU, jami’ar Jalingo ta jihar Taraba alawus-alawus da suke bi bashi. Comr. Haruna ya yi wannan bukata ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron majalisar zartarwa na shiyyar karo na...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata....
Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa...

Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Najeriya Wajen Yin Watsi Da Kariyar Cinikayya Da Yin Adawa Da Danniya Da Cin Zarafi
Haka kuma Wang ya halarci taron ministocin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS da na kasashe kawayensu a wannan rana, inda aka tattauna game da yadda za a karfafa ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Wang ya bayyana cewa, mafitar matsalolin da ake fuskanta a duniya ita ce kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori...

Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
Ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai a tashar ruwa ta PTML da Tin Can na da nufin sanin irin kalubalen da jami’an sa ke fuskanta wurin amfani da sabuwar na’urar zamani domin binciken kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Ya kuma kara gargadin jama’a game da karuwar kwararowar magunguna kasar da ba...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta. AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa. Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan...
Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke...
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran. Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar. Ayarin likitocin ƙarƙashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za...
Ƙungiyar ISWAP mai yaƙi da tayar da ƙayar baya a yammacin Afirka, ta ɗauki alhakin harin da ya yi ajalin mutum 26 a Jihar Borno. Ƙungiyar ta iƙirarin ɗaukar alhakin harin ne a wani saƙo da ta wallafa a shafin Telegram kamar yadda BBC ya ruwaito. Aminiya ta ruwaito yadda wani abin fashewa da ake...
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin...
Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma...
Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), kungiyar makarantar tuki ta Nijeriya (DSAN), kungiyar direbobi mata (FDA), kungiyar masu motocin dakon kayayyakin da ake shigo da su ta ruwa (AMATO) da kuma mambobin kungiyar masu binciken tuki ta Nijeriya (IDIN). Da yake jawabi a wajen kaddamar da...
Bari mu dauki dala a matsayin misali, tattalin arzikin Amurka na dogara ne kacokan da girman dalar Amurka. Yayin da kasafin kudinta ke gazawa wajen biyan bukatunta na cikin gida, kuma tana da al’adar dogaro da kasashen waje kan kudaden da take kashewa da ke da alaka da jingina gazawar mulkinta ga sauran kasashen duniya,...
Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan...
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar. “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa....

An Fara Gudanar Da Zaman Taron Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Iran Da Kasashen Nahiyar Afirka
An fara gudanar da zaman taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da kasashen nahiyar Afirka karo na uku A safiyar yau Lahadi ne aka bude zaman taron karo na uku kan harkokin tattalin arziki tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Afirka a birnin Tehran, tare da halartar shugaban kasar Iran da mataimakinsa na...
Wannan wata mahawara ce da aka daɗe ana yi kan wace kungiya ce ta fi gawurta a Birtaniya? Shin wace kungiya ce ta fi lashe kofuna? Wacce ce ta fi tara kudin shiga ko kuma ta fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta? Wace kungiya ce ta fi filin wasa mai girma? Wacce ce ta...
Kungiyar Hamas a Gaza, ta yi allawadai da ma’aikatar sharia ta kasar Amurka wacce ta cire rigar kariya ga ma’aikatan hukumar bada agaji ta falasdinwa wanda MDD take kula da ita. Kungiyar UNRWA ta na bada agaji ga falasdinawa ne tun bayan kafa HKI da kuma korar Falasdinawa a karon farko daga kasarsu a shekara...
Kwanan nan, wakiliyar CMG ta zanta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev wanda ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin zantawar, shugaba Aliyev ya waiwayi dadadden tarihin cudanyar kasashen biyu da ma zumuncin da ke tsakaninsu, kuma ya yi imanin da cewa, kasancewar dukkansu kasashe masu tasowa ne, kasashen biyu za su hada...
Kungiyar kwallon kafa ta PSG – wadda tuni ta lashe gasar League 1 ta Faransa na daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin za su lashe gasar Zakarun Turai ta bana saboda karfin da tawagar take da shi sannan kuma kungiyar a gine take hadi da kwararren mai koyarwa, Luis Enrikue, tsohon kociyan Barcelona da...
Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba. Da yake magana ta wayar...
Manchester United ta kai zagayen kusa da karshe ne bayan doke Olympic Lyon ta Faransa da 5-4, bayan an yi canjaras da 2-2 a wasan farko da aka buga a Faransa. Kenan United ta yi nasara da 7-6 jimilla. Yanzu United za ta fafata wasan gab da na karshe ne da kungiyar Athletic Bilbao a...
Shugaban Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan Isra’ila Netanyahu ba zai ja shi zuwa shiga cikin yaki da Iran ba, kuma a shirye yake ya gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci da shugaban kasar Iran Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya jaddada cewa: Ba za a sanya shi shiga yaki da Iran ba saboda...
Wani mummunan al’amari ya girgiza al’umma a Ƙaramar Hukumar Kwami, Jihar Gombe, inda ake zargin wani magidanci ya jagoranci sacewa da kashe ɗansa mai shekara shida domin yin tsafin kuɗi. Ana zargin cewa mahaifin yaron shi ne jagoran kisan kuma Yana cikin waɗanda suka tsere, a yayin da hukumomi ke ci gaba da farautar sa....
Raguwar kudin a hannun mutane na iya zama wani bangare na kokarin rage matsin lamba kan hauhawar farashin kayayyaki da samun daidaiton tattalin arziki. Baya ga raguwar kudade a hannun mutane, ajiyar a bankin CBN ya karu zuwa naira biliyan 28.52 a watan Maris na 2025, daga naira biliyan 27.57 a watan Fabrairun 2025....
”Wannan lokaci ne na bakin ciki, kuma a cikin irin wadannan lokutan ne kuka san wadanda ke kulawa da ku da gaske.” Ribadu ya bayyana cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tashin hankali da ke fama da shi a kasar nan, kuma tana aiki tukuru don gyara abubuwan da suka lalace. Ya ce,...

Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da...
Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES), sun sanar da shirinsu na ƙaddamar da gidan rediyo na haɗin gwiwa. Ƙasashen guda uku, waɗanda duk a halin yanzu suke ƙarƙashin mulkin soja, sun jaddada cewa sun kafa gidan rediyon ne da nufin daƙile farfagandar ƙasashen waje da kuma isar da...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, za ta karbi bakuncin taron farko na kasa da kasa kan kare hakkin bil adama a Gabas ta Tsakiya. Shugaban Hukumar Al’adu da Sadarwa ta Musulunci Mohammad Mehdi Imanipour ya bayyana cewa, za a gudanar da taron farko na kasa da kasa kan batun kare hakkin bil’adama kan Gabas ta Tsakiya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da ƙananan sana’o’i, waɗanda al’umma ke dogaro da su don biyan buƙatunsu na yau da kullum. Irin waɗannan sana’oi sun haɗa da saƙa, jima, fawa, suyan ƙosai ko masa da dai sauransu. A da can masu waɗannan sana’o’i sun dogara ne...
Hukumar lafiya ta duniya (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar. Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a...
Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan. Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki. Abin da ya sa...
Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da...
Wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ake kira Mahmuda tana ci gaba da kafuwa da ƙara ƙarfi tare da addabar jama’a a wasu garuruwa na ƙananan hukumomin Ilesha Baruba da Kemaanji da Kaiama da Baruten na Jihar Kwara. Bayanai sun ce ’yan ƙungiyar sun sami mafaka ne a gandun dajin Kainji Lake National Park, kuma...
Sai dai daga baya suka fara yawo da makamai suna kama mutane, suna yanke musu hukunci har da kashe wasu. Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa a yanzu mutane ba sa iya zuwa gonakinsu da ke nisan da kilomita biyu saboda tsoron ‘yan ƙungiyar. Ya ce kashi 50 cikin 100 na mutanen garin sun tsere....
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.” A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki,...
A ranar 17 ga watan Afrilun da muke ciki ne wakilai ko ministocin noma na kasashen kungiyar BRICS suka taro a Brazilian a kasar Brazil inda suka rantaba hannu kan shelanta shirin namusamman na bunkasa ayukan noma da kuma harkokin samar da abinci da kuma wadatar da shi ga kasashen duniya farko ga kasashen kungiyar....