2025-09-17@21:55:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3730

«hira»:

    Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana gudanar da ayyukan gyara da ginawa da kuma inganta hanyoyin mota domin cimma kudirin ta na bunkasa bangaren aikin noma. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin sanya kwalta akan hanyar Dandi da Farin Daba zuwa Gada a karamar hukumar Kazaure. Ya ce gwamnatin jihar ta...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Kudancin Caucasus cikin lura Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i, ya yi nuni da yadda Iran ke daukan abubuwan da ke faruwa a yankin arewa maso yammacin kasar da muhimmanci, yana mai jaddada cewa: “Suna...
    Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba zasu yarda wasu kasashe su shiga tsakanin Iran da Iraki ba Yayin da yake magana game da rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakanin Iran da Iraki, babban sakataren majalisar koli na tsaron kasar Iran Ali Larijani  ya yi nuni da cewa: Bai kamata a...
    Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wata barazana da makarkashiyar ‘yan sahayoniyya da Amurka Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwa a ranar 16 ga watan Agusta na tunawa da dawowar fursunonin da aka ‘yantar zuwa mahaifar ta daular...
    Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da neman kasashen da za su karbi ‘yan gudun hijiran Falasdinawan Gaza! Jaridar Wall Street Journal ta buga wani rahoto da ke cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da gudanar da tattaunawar da ta bayyana na zaman natsuwa domin...
    Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ki amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta sanar da kin amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma da ke gabashin kasar, duba da matakin da ya saba wa ka’idojin diflomasiyya, duba da yadda Kongo ke ganin ci...
    Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan tsawon watannin da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba. Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni su kawo musu ɗauki cikin gaggawa. Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zuru Adam A. Zango...
    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ta bayyana alhininta game da rasuwar Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, Mai Martaba Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (mai ritaya) Gomo II, wanda ya rasu yana da shekaru 81. Shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce marigayin jagora ne mai kishin ƙasa, dattijo nagari kuma basarake mai daraja wanda...
    Sarkin Zuru, Alhaji Mohammed Sani Sami Gomo II, ya rasu a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, a wani asibiti da ke birnin London bayan gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 82. A cewar majiyoyin danginsa, ana sa ran za a kawo gawarsa daga London zuwa Najeriya nan da gobe (Litinin), domin gudanar...
    Sojojin haramtaciyar kasar Isara’ila (HKI) sun kai hare-hare kan wuraren jama’a a kasar Yemen. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto daga tashar talabijin ta Almasirah na Ansarullah na fadar haka. Ta kuma kara da cewa makami mai linzami na sojojin ruwa na yahudawan sun fada kan tashar bada wutan lantar na Hazeem...
     Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa shuwagabannin kasashen turai kan cewa ya amince da shawara shugaba Putin na musayar kasa don samar da zaman lafiya. Majiyoyi biyu wadanda basa son a bayyana sunayensu kuma kusa da Trump a taron na Alaska ya bayyanawa jaridar ‘The guardian’ ta kasar Burtania a jiya Asabar kan cewa,...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya aika da jajensa ga mutane da Firai ministan kasar Pakisatan kan ambaliyar ruwa da ta faru a kasar bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 300 da kuma bacewar wasu. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban y...
    Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, ritaya Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami, ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Garba Umar-Dutsinmari, ne ya tabbatar da rasuwar mai martaba a cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi ranar Lahadi. Ya bayyana cewa Sarkin ya rasu ne...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk. Ya kara...
    Mutum sama da 600 sun rasa matsuguni sanadiyyar wata mummunar ambaliya da ta afku a garin Potiskum da ke Jihar Yobe. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta bayyana cewa kimanin mutane 612 ne ta samarwa matsuguni bayan ambaliyar ruwa ta mamaye sama da gidaje 102 a garin Potiskum. Wannan ambaliya ta afku...
    Firaministar kasarDenmark Mette Frederiksen, wadda a halin yanzu kasarta ke rike da shugabancin kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana a wata sanarwa ga manema labarai a jiya Asabar cewa, kasarta na shirin kakabawa Isra’ila takunkumi, sakamakon yakin da take yi a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan. A wata hira da ya yi da Jyllands-Posten, Frederiksen...
    Jakadan Iran a Saudiyya Alireza Enayati ya tabbatar da ci gaba da tuntubar juna tsakanin babban hafsan hafsoshin sojin Iran da ministan tsaron Saudiyya. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na IRNA Alireza Enayati ya yi nuni da cewa, Saudiyya na kallon alakar ta da Iran a matsayin alaka mai matukar muhimamnci, kamar yadda...
    Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Zirin Gaza ta sanar a yau cewa akalla mutane 70 suka yi shahada da suka hada da 8 da aka gano gawarwakinsu, yayin da wasu 385 suka jikkata a cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata, sakamakon hare-haren da Isra’ila a sassa daban-daban na yankin. Ma’aikatar ta yi nuni...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci. Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da...
    Kasashe 31 na duniya sun yi Allah wadai da kalaman fira ministan Isra’ila na shirin mamaye yankunan kasashe don kafa ‘Babbar kasar Isra’ila Kalaman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbare kasar Isra’ila” ta janyo suka daga Larabawa da Musulunci. Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen...
    Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa ya mayar da martani ga son zuciya da wani jami’in kasa da kasa ke yi game da mamayar ‘yan sahayoniyya Mataimakin ministan harkokin waje kan harkokin shari’a da kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya yi tsokaci game da kalaman mataimakiyar shugaban kotun kasa da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Suna godiya ga  Iraki saboda karimcin da ta yi wa masu ziyarar Arba’een na Imam Husain {a.s} Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yaba da kokarin gwamnati da al’ummar Iraki wajen karbar bakwancin masu ziyarar juyayin Arba’een na Imam Husaini {a.s}. A yayin da yake...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa unguwar Al-Zeitoun tare da lalata gidajen Falasdinawa kusan 400 Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean ta bayyana cewa: Kwanaki shida ke nan da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ke luguden wuta a unguwar Zeitoun da ke kudu maso gabashin birnin Gaza, inda suka lalata gidaje kusan 400, ta hanyar jefa...
    A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya. Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana. Manoma sun fara noma cikin...
    An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka bayyana taron a matsayin mai matukar amfani. Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi, yayin da manzon musamman na Rasha Kirill Dmitriev ya bayyana cewa yanayin...
    Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da...
    “Tsarin mulkin ADC ta bayyana cewa duk wanda ke neman zama shugaban jam’iyyar, dole ne ya kasance mamba nagari na jam’iyya. Wannan shi ne muhimman bukata ta asali wadda ba za a iya yin watsi da ita ko kauce mata ta kowace hanya ba. “A cewar tsarin mulkin ADC, hanyar da ta dace don cike...
    Gwamnatin kasar China ta bayyana cewa ba zata taba amincewa a sake dorawa JMI takunkuman tattatalin arziki wadanda MDD ta dauke mata su a watan octoban da ya gabata ba. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Lin yana fadar haka ya kuma kara da cewa kasashen...
    Mutum 12 sun rasu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Samawa, da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano. Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:40 na daren ranar Juma’a a kan titin Zariya zuw Kano. Ambaliya: Magidanta da dama sun rasa muhallinsu a...
    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin.   Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar...
    “Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar...
    An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila a wani dajin da ke arewacin Isra’ila. Sojan ya kashe kansa ne a lokacin da yake aikin soja, wanda ya kawo adadin sojojin da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Manufar ita ce a ninka adadin likitoci, ma’aikatan jinya, masu hada magunguna, kwararrun dakunan gwaje-gwaje da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya. Wannan ko shakka babu zai kara habaka harkokin kiwon lafiya a kasar,” in ji shi. Tsohon gwamnan Jihar Katsinan ya bayyana cewa, a bana, TETFund ta samu tallafinta mafi girma na Naira Tiriliyan...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja domin ziyarar aiki zuwa ƙasashen Japan da Brazil. Ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar Juma’a, inda zai tsaya a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Matsalar tsaro...
    Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin...
    A farkon wannan shekarar da ta gabata, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito Ministan Sufurin Ma’aikatar Jiragen Sama Festus Keyamo, a wani taro ya bai wa kungiyoyin na Sufurin Jiragen Sama tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da bi ka’ida wajen sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman kasa. Keyamo ya kuma bai wa shugabannin kungiyoyin...
    Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani da karfi kan duk wani wuce gona da iri kanta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Gwagwarmaya ita ce babban jari kuma wata dabara mai kima ga yankin, yana mai jaddada...
    Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin na Iran laifi ne na yaki Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce: Harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan gidan yarin Evin da ke birnin Tehran fadar mulkin...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun kai wani mummunan farmakin kan birnin Gaza tare da janyo ruftawar gidaje a Khan Yunis Falasdinawa da dama sun yi shahada tare da jikkata a yau Juma’a a wani kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza a rana ta hudu a jere, yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila take...
    An gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila da ya kashe kansa bayan yaki a Gaza Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da gano gawar wani jami’in sojin gwamnatin mamayar Isra’ila a wani dajin da ke arewacin Isra’ila. Sojan ya kashe kansa ne a lokacin da yake aikin soja, wanda ya kawo adadin sojojin da...
    Wata kotun tarayya a kasar Kanada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Suna buƙatar kawar da makaman nukiliya da kuma kawo ƙarshen maganganun rashin jin daɗi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan kawar da makaman nukiliya da kuma amincewa da laifukan tarihi a hukumance kamar harin bam din da...
    Kungiyoyin kasa da kasa guda 100 sun koka kan yadda gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi watsi da bukatu har 60 kan ba da damar shigar da agaji zuwa Gaza Sama da kungiyoyi masu zaman kansu 100 ne suka bayyana a wata wasika ta hadin gwiwa da aka buga jiya alhamis cewa, ana kara amfani da...
    Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da miƙa wa mataimakinsa, Malam Faruk Jobe, ragamar mulkin jihar, inda shi kuma zai tafi hutun mako uku domin duba lafiyarsa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara...
    A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan...
    A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan...
    Shugaban ƙasar Lithuania, Gitanas Nauseda, ya zabi ’yar majalisa Inga Ruginiene ta jam’iyyar Social Democrat, a matsayin firaminista, bayan Gintautas Paluckas ya yi murabus sakamakon binciken rashawa da ake gudanarwa a kansa. Sai dai Ruginiene ta taba fuskantar suka kasancewar tana da alaka da ’yan uwa a Rasha, wadanda ta ziyarta a shekarun 2015 da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.”   Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na...