2025-06-30@20:12:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2551
«hira»:
A ranar farko ta watan Muharram, an bude juyayin Ashura ta hanyar yin taron kananan yara a matsayin nuna juyayi ga jaririn Imam Hussain ( a.s) Ali Asgar ( a.s) da abokan gaba su ka kashe a Karbala. Iyaye mata dauke da kananan yaransu masu watanni 6 daga haihuwa sun cika wurare mabanbanta na Iran...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana cewa; A cikin kwanaki 12 da su ka gabata duniya ce ta yi yaki da Iran. Hujjatul Islam Wal Muslimin Abu Turabi Fard, ya fara hudubarsa da mika sakon ta’aziyyar shigowar ranakun Ashura, haka nan kuma jinjina ga shahidan jamhuriyar musulunci masu daraja da HKI ta...
Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Danata rasuwa. Alhaji Aminu Danata ya rasu yana da shekaru 94 a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
Wasu daga cikin jami’an sojojin HKI sun yi furuci da cewa, an ba su umarni ne da su rika bude wuta akan Fararen hula Falasdinawa da suke zuwa cibiyoyin karbar kayan agaji, suna jaddada cewa, wadanda su ka kashe din ba su yin wata barazna a gare su. Jaridar “Haarezt” ta ‘yan sahayoniya ta buga...
Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina...
Minsitan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kira yi shugaban kasar Amurka Donald Ttump da ya daina yin maganganun da ba su dace ba akan jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei. Abbas Arakci ya kara da cewa; Ko kadan Tehran ba za ta bari wani mahaluki ya ayyana mata makoma ba,...
Kamfanin Dillancin Labarun “Mehr” ya nakalto cewa; Tun da jijjfin safiyar yau Asabar ne tasoshin jiragen kasa da na safa-safa su ka cika makil da masu son halarta babban filin Juyi na Tehran da can ne zai zama masonin rakiyar shahidan zuwa makwancinsu na karshe. Ana iya ganin dubun dubatar mutane da su ka fito...
A yau Jumma’a 27 ga watan Yunin ne a hukumace aka bude hanyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa da za ta rika aiki a kai a kai, daga Urumqi, yankin jihar Xinjiang ta kasar Sin zuwa Addis Ababa na kasar Habasha. Wannan kuma ita ce hanyar jigilar kayayyaki ta farko daga Xinjiang zuwa Afirka...
A ranar Juma’ar nan ne wasu abubuwa da ake kyautata zaton bom ne ya kashe mutane huɗu tare da raunata wasu 21 a hanyar Katarko zuwa Goniri a Ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe. Kamar yadda rahoton ke nunawa, waɗanda lamarin ya rutsa da su, galibi ’yan ƙabilar Gotala ne, suna kan hanyarsu ta zuwa...
Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da wasu biyar suna jinya bayan da wata babbar mota ƙirar tirela ta ƙwace ta kutsa cikin kasuwar Mile Six da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba. Shaidun gani da ido a wurin sun bayyana cewa, duk ƙoƙarin da direban motar ya yi na hana afkuwar...
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar. Murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take. Sojoji sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Neja ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana rashin...
A wani mataki na ba-zata, shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga muƙaminsa nan take. Ganduje, wanda tsohon gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana dalilan rashin lafiyarsa ne ya sa ya ɗauki matakin murabus, inda ya bayyana cewa yana buƙatar ya maida hankali kan lafiyarsa.
Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa a birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Wadannan shugabannin biyu sun zo kasar Sin ne domin halartar taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos. A yayin ganawarsa...
“Yunwa da talauci ba wai abubuwa ne da suka shafi al’umma ba ne kawai, su ne ke haifar da rashin tsaro, laifuka, tashin hankali, da kuma wargajewar al’umma, wadannan al’amura suna haifar da mugun yanayi, talauci yana haifar da rashin tsaro da rashin tsaro, sannan kuma ya kara zurfafa talauci. “Wadannan yunkurin a bayyane suke...
Alhaji Sabo ya yaba wa shugaban majalisar wakilai kuma Iyan Zazzau, Dakta Abbas Tajuddeen, na yadda a tsarinsa ake koya wa matasa sana’a da zarar sun kammala yana ba matasa kayayyaki da kuma kudade domin dogaro da kai. Ya shawarci gwamnonin arewa da su duba matsalar durkushewar kamfanin yin tamfoli da ke Zariya, wanda a...
Daga ƙarshe dai Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sa hannu kan sababbin dokokin haraji guda hudu da a baya suka jawo cece-kuce da zazzafar muhawara a faɗin Najeriya. An dai sanya hannun ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis, inda shugaban ya ce dokokin za su bunkasa harkokin hada-hadar...
Albarkacin cika shekaru 55 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Italiya, an shirya bikin kaddamar da shirin talibijin mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ya gabatar, a jiya Laraba a birnin Rome, hedkwatar kasar Italiya. Za a fara watsa wannan shiri a kafofin yada labarai na kasar fiye da 30. ...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar. Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin. ’Yan sanda sun kashe ’yan...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar. Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin. ’Yan sanda sun kashe ’yan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta gabatar da cakin kuɗi Naira 13 da dubu ɗari 4 da 28 da ɗari 6 da 59.95 ga ’yan uwan ’yan sanda 10 da suka mutu a bakin aiki. Taron gabatar da kuɗin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, na da nufin bayar da tallafin kuɗi...
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta gabatar da cakin kuɗi Naira 13 da dubu ɗari 4 da 28 da ɗari 6 da 59.95 ga ’yan uwan ’yan sanda 10 da suka mutu a bakin aiki. Taron gabatar da kuɗin wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, na da nufin bayar da tallafin kuɗi...
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin wani fitaccen kasurgumin dan bindiga mai suna Babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Bakatsine ne ya bayyana hakan a wani sharhi da aka wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa,...
Dan wasan mai shekaru 40 ya zura kwallaye 93 sannan ya taimaka wajen zura 19 a wasanni 105 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar ta Saudiyya, amma har yanzu bai samu nasarar lashe kofi a gasar ba, a kakar wasan da aka kammala kwanan nan, Al Nassr ta kare a...
Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da fitar da Naira biliyan 6.563 kuɗin giratuti domin biyan haƙƙoƙin ’yan fansho da suka yi ritaya daga shekarar 2021 zuwa 2023. Wannan sanarwar ta fito ne bayan taron Majalisar Zartarwa karo na 48 wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta. Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian Norgaard...

Sin Ta Sha Alwashin Rarraba Fasahohinta Na Ainihi Da Dabarunta Na Kirkire-Kirkire Tare Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya ce, kasarsa a shirye take ta rarraba fasahohinta na ainihi, da dabarunta na kirkire-kirkire tare da sauran sassan kasa da kasa. Li Qiang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa na bude taron shekara-shekara, na sabbin jagorori karo na 16, wato dandalin tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos...
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wakilan ƙasarsa za su gana da na Iran domin ci gaba da tattaunawa kan makaman nukiliyarta a mako mai zuwa. “Za mu tattauna da Iran a mako mai zuwa, ƙila mu ƙulla yarjejeniya ko kuma akasin haka, ba na ce ba,” in ji shi yayin jawabinsa a taron ƙasashe...

Shawarar Gudanar Da Harkokin AI Na Duniya Na Jagorantar Ci Gaban Wayewar Kan Dan Adam Ta Hanyar Amfani Da Fasahar Zamani
A yanzu haka, fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI na sauya zaman rayuwar dan Adam. Ga misalin, motoci mara matuki na saukaka tafiye-tafiye na dan Adam, samfurin binciken yanayi na iya hasashen hanyar guguwa a cikin dakika 10 kawai… Amma, fasaha ta zama kamar “takobi mai kaifi biyu”, wadda a lokaci daya take kuma...
Wasu jihohin da suka hada da Benuwe, Filato, da Borno, a ‘yan kwanakin nan sun samu tabarbarewar tsaro, lamarin da ya sa sojoji da sauran jami’an tsaro suka kara zage damtse wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da kalubalen tsaron ke kara ta’azzara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Rigimar shugabanci a jam’iyyar adawa ta PDP, ta lafa yayin da Sanata Samuel Anyanwu ya samu umarnin komawa bakin aikinsa a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata...
Kasar Iran ta zargi Isra’ila da kai mata hari a safiyar Talata bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta a tsakanin kasashen biyu. “Gwamnatin Yahudawa ta ƙaddamar mana da hari har guda uku a ƙasar Iran har zuwa ƙarfe 9:00 na safiyar Talata,” kamar yadda gidan talabijin ɗin kasar Iran ya ambato...
A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba. Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana matukar damuwar da Sin ke da ita dangane yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, tare da bayyana fatan ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran nan bada jimawa ba. Guo Jiakun ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau...
Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Isra’ila da Iran, bayan zargin ƙasashen biyu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla. Lamarin na zuwa ne bayan ɓullar rahoton kai wa juna hari daga dukkan ƙasashen biyu, duk da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ’yan sa’o’in da suka gabata. Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Legas ta yi wa wasun ‘yan China shida ɗaurin shekara ɗaya bayan ta same su da laifin ta’addanci da zamba ta intanet. Sanarwar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Nijeriya ta’annati (EFCC) ta fitar ta ce kotun da ke unguwar Ikoyi ta Jihar...
Eze ya gode wa waɗanda suka kafa ADA saboda ƙoƙarinsu na ceton Nijeriya daga hannun shugabannin da ba sa bin tsarin dimokuraɗiyya. Ya ce sun nuna ƙwazo da ƙaunar ƙasa. Ya ce, “Kun nuna bajinta da kishin ƙasa ta hanyar ƙoƙarin ƙwato mulki daga hannun shugabannin da suka haddasa rikice-rikice, garkuwa da mutane, talauci, yunwa...
Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya zargi Iran da Isra’ila da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta. Da yake jawabi kafin tafiyar Babban Taron Ƙungiyar NATO, da zai gudana a birnin Hague, Trump, ya bayyana takaicinsa bisa yadda kasashen biyu game da saɓa yarjejeniyar, sa’o’i kaɗan bayan sun amince da ita. Tun da farko sai da ya...

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, shugaban kasar Xi Jinping, zai halarci bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin jinin harin sojojin Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, da safiyar ranar 3 ga watan Satumban bana, tare da gabatar da jawabi. Kazalika a ranar, kasar Sin...
Iran ta kama mutane shida kan zargin kasancewa ’yan leken asiri ga Isra’ila. Rahotannin kafofin watsa labarai na ƙasar Iran sun nuna cewa mutanen shida suna leken asiri ne ga hukumar leken asiri ta Isra’ila, Mossad, kuma an kama su ne a lardin Hamadan da ke yammacin kasar. Ali Akbar Karimpour, wani jami’in Rundunar Juyin...
Gwamnatin ƙasar Isra’ila ta ce ta amince da tsagaita wuta a yaƙin da aka kwana 12 ana gwabzawa tsakaninsu da Iran. Isra’ila ta ce ta amince da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ce bayan abin da ya kira cimma burinta na ƙaddamar da yaƙin a Iran tun a farko. Ta bayyana a cikin wata...
Haka kuma wasu ƙungiyoyi a Turai sun nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan. Majiyoyi sun bayyana cewa Brentford na son a ce darajar Mbeumo ta kai irin kuɗin da United ta biya wajen ɗauko Cunha kafin su yarda su sayar da shi. Mbeumo ya zura ƙwallaye 20 a kakar wasan da ta gabata, kuma ya taimaka...
Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran...
Sai dai babu wani tabbaci daga gwamnatin Iran ko Isra’ila kan cewa sun yarda su dakatar da yaƙin. Trump ya kira rikicin da ake ciki da suna “yaƙin kwana 12,” yana mai cewa wannan rikici da za a iya yin shekaru ana fafatawa da shi bai bazu ba, kuma ba zai bazu ba. Mene ne...
Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran...
Gwamnatin Qatar ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojin saman Amurka da ke yankin al-Udeid na kasar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed al-Ansari, ya wallafa a shafinsa na X cewa: “Mun ɗauki wannan a matsayin keta haddin Qatar da sararin samaniyarta da dokokin duniya da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin...
Wani hari da Sojojin Amurka da Isra’ila suka kai kan wuraren Nukiliyar Iran ya kara tsoratar da kasuwar mai, wanda ke nuna cewa farashin na iya haura sama da $80 a kowace gangar mai. Masana sun yi hasashen cewa farashin fetur na iya haura sama da N1,000 a litar cikin ‘yan makonnin nan idan ba...
Rahotanni na cewa ƙasar Iran ta fara abin da ta kira martani mafi girma da nasara kan hare-haren Amurka. Kamfanin Dillancin Labaran Iran na Tasnim, ya ce dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar da Iraƙi A halin yanzu ne aka samu labaran...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu wata hujja ko dalilin kai wa Iran hari. Putin ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Agarachi a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha Fararen hula sun yi...
Wani babban jami’in Rasha, Dmitry Medvedev ya yi iƙirarin cewa akwai wasu ƙasashe da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya domin kare kanta daga abokan gaba. A ranar Lahadi, Dmitry Medvedev wanda tsohon Firaministan Rasha ya yi iƙirarin cewa wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya kai-tsaye bayan hare-haren Amurka kan...
Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Rasha, da Sin da Pakistan, sun gabatar da wani daftarin kudurin kwamitin sulhun MDD, kan halin da ake ciki a Iran. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya shaidawa nuni taron manema labarai da aka saba yi a yau Litinin cewa, harin da Amurka ta...