2025-06-15@23:01:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3996

«soshiyal midiya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya bai wa alhazan jihar su 3,200 kyautar Riyal 1,000 na Saudiyya (kimanin Naira 450,000) a matsayin barka da sallah. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya kai wa alhazan ziyara a Minna. Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Mutum 9 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa Ya taya su murna bisa kammala aikin Hajji lafiya, inda ya ce wannan kyauta ce domin tallafa musu kafin su dawo gida Najeriya. Gwamna Aliyu, ya yaba da yadda alhazan suka kiyaye doka da oda a ƙasa mai tsarki, inda ya ce sun wakilci Jihar Sakkwato cikin ƙwarewa da girmamawa. Ya kuma gode musu bisa ladabi da haƙuri da...
    Aƙalla mutum tara ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Kyaramma da ke Ƙaramar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan jihar, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, inda motoci biyu ƙirar Golf 3 suka yi taho-mu-gama, kuma mutane da dama sun jikkata. Edgar Lungu: Za a yi zaman makokin kwana 7 a Zambiya  Gobara ta tashi a otal ɗin da ke ɗauke da Alhazan Najeriya 480 a Makkah Ɗaya daga cikin motocin, mai lambar Kaduna MKA 687 AY, ana ɗauke da ita ne daga Abuja zuwa garin Gujungu, kuma direban motar mai suna Adamu Sunusi, mai shekaru 35 daga Ƙaramar Hukumar Hadeja. Rahoton ’yan sanda...
    A masana’antar Nollywood dake Kudancin Nijeriya, manyan masu kudinsu, sarakuna, hukumomi da gwamnatoci na iyakar kokarinsu wajen ganin masana’antar ta cigaba, ta hanyoyi daban daban da suka hada da kayan aiki, wajen daukar fim, fadada ilimi, tallace tallace da sauran tallafi da masana’antar ke bukata, a wasu lokutan ma akan daukesu har kasashen Turai wajen koyon aiki da kuma tallata hajarsu ga manyan dillalan fim a Duniya wanda ta wannan hanyar sai su samu manyan kudade. T Y ya cigaba da cewa idan ana maganar masana’antar Kannywood ba haka abin yake ba, domin kuwa a nan yankin sai mai shirya fim ya nemi gida ko kamfanin da zai shirya fim din sa ya rasa, hakan zai sa ya je ya...
    Jirgin ruwan na “Madeleine” shi ne na 36 a cikin jerin jiragen ruwan ‘yanci da suke son karya takunkumin da aka kakabawa yankin Gaza tun 2007. A cikin wannan jirgin ruwan da akwai ‘yan gwgawarmaya masu rajin kare hakkin bil’adama su 12 da su ka fito daga kasashe daban-daban, yana kuma dauke da kayan agaji na abinci da magani.  Jirgin ruwan ya samo sunansa ne daga wata Bafalasdiniya mai suna; Madeleine Kulaib, wacce ita ce macen farko ta Falasdinu da ta kware a sana’ar kama kifi bayan da mahaifinta ya yi shahada a yayin  yakin da HKI ta shelanta akan Gaza a 2023. Jirgin ruwan na “Madline” ya taso ne daga kasar Italiya, wata daya bayan da jirgin sama maras...
    Idan ana shan ruwan ganyen mangwaro, yana taimakawa wajen rage gudawa da kumburin ciki. 4. Yana Taimakawa ciwon sanyi da tari Yana da sinadaran da ke taimakawa wajen warkar da tari da mura, wanda ke iya zama matsala ga wasu mata masu ciki. 5. Yana inganta lafiyar zuciya Yana rage hawan jini, wanda ke iya zama hadari ga masu ciki, musamman masu ciwon hawan jini (preeclampsia).   Yadda ake amfani da ganyen mangwaro: A tafasa ganyen a ruwa na tsawon minti 10-15, a bar shi ya huce, sannan a sha a hankali. Za a iya hada shi da zuma ko lemon tsami don kara dandano.   Lura: Kar a sha fiye da kima, musamman idan ba a saba ba, domin...
    Jami’in gabatar da kara, Anil Kumar, ya tabbatar da hukuncin kotun, kamar yadda jaridar The Times of India ta ruwaito a ranar Litinin. Rahoton ya bayyana cewa, “A ranar 30 ga Mayu, 2020, ta shigar da karar, tana mai cewa ta samu sako a ranar 12 ga Mayu, 2020, daga wata lambar kasa da kasa da ke ikirarin ta fito daga Landan.” A cewar rahoton, “Mai aikawa ya gabatar da kansa a matsayin ‘Deepak Lee’ kuma ya ba da ID na imel.” “Ba da jimawa ba, wanda ake zargin ya kira ta ya ce ya same ta ne ta wani shafin aurenta, inda suka fara hira ta WhatsApp, sai ya shaida mata cewa ya aika da shaidarta.” Rahoton ya ci...
    Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Asa’d Abu Sharia shi ne baban sakataren kungiyar ‘Dakarun Palastinewa”. Wacce aka kafa a shekara ta 2001 M. Kungiyar kanta ta tabbatar da wannan labarin ta kuma bayyana cewa ya dade yana shugabantar wannan kungiyar sannan a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya shiga cikin yakin da aka fara kan HKI kuma dakarunsa sun kama yahudawa da dama suka shigo da su su gaza. Banda haka shi ne yake jagorantar bangaren soje na kungiyarsa. Sau da dama ya jagoranci Falasdinawa a yaki da yahudawan a Gaza. Sannan kungiyar tana...
    PPRO ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana auren mahaifiyar wanda aka cutar (da sakaya sunanta). “An bayyana cewa ya yi lalata da yarinyar a lokacin da mahaifiyarta ke barci, yana shiga dakinta kuma yana aikata abubuwan da ba su dace ba a lokuta da dama. “Wakil ya ce, “Yarinyar na shan wahala amma duk da haka ta kame bakinta sai da lamarin ya ta’azzara sannan ta fada wa makwabta, wanda hakan ya kai ga daukar matakin kama wanda ake zargi da aikata laifin,” Ya ce a lokacin da ake yi masa tambayoyi an ruwaito wanda ake zargin ya amsa laifinsa. “An kwashe wanda abin ya rutsa da shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa da...
    Ƙasar Zambiya ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai don girmama tsohon shugaban ƙasar, Edgar Lungu, wanda ya rasu a ranar Alhamis, 5 ga watan Yuni, 2025, a ƙasar Afirka ta Kudu. Ya rasu yana da shekaru 68. Gobara ta tashi a otal ɗin da ke ɗauke da Alhazan Najeriya 480 a Makkah 2027: Makomar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na janyo cece-kuce Lungu ya shugabanci Zambiya daga watan Janairun shekarar 2015 har zuwa watan Agustan 2021, lokacin da ya sha kaye a hannun shugaban ƙasa mai ci yanzu, Hakainde Hichilema. Gwamnati ta sanar da cewa daga ranar 8 zuwa 14 ga wata Yuni, duk tutocin ƙasar za su kasance a ƙasa, sannan kuma an dakatar da duk wasu...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta wallafa tsokacinta kan rahoton babban darartan Hukumar IAEA ga kwamitin gwamnonin hukumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da ra’ayoyinta da tsokacinta kan sabon rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnonin hukumar ta IAEA a ranar 24- wannan shekara ta 2025. A cewar cibiyar diflomasiyya da ta yada labarai ta hukumar makamashin nukiliya ta Iran, an fitar da bayanin mai taken “Sa ido da Tabbatarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 (2015)” a ranar 31 ga Mayu, 2025. Bayanin ya fayyace cewa: Rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa...
    Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta amince da samun tauyaya a yawan adadin sojojin mamayar Isra’ila sakamakon halakar wasu daga cikinsu Rundunar sojojin Isra’ila ta yarda cewa: Suna fama da matsanancin karancin sojoji masu yawa, a halin yanzu akwai yawan 10,000, da aka rasa kuma ana neman fiye da rabinsu a fagen gudanar da yaki, a ci gaba da gudanar da ayyukan soji a zirin Gaza. Rundunar sojin ta ce suna fuskantar karancin sojoji fiye da 10,000, ciki har da kusan 6,000 na rukunonin yaki,” wannan rashin sojojin rashi ne maim ai tsanani da ake bukatar samunsu cikin gaggawa, don haka rundunar soji take gudanar da duk matkn da suka dace don toshe wannan gurbin, in ji kakakin rundunar sojin mamayar...
    Ran 4 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan sanarwar hana baiwa daliban ketare dake neman gurbin karatu a jami’ar Harvard bizar shiga kasar da dakatar da shigar daliban ketare dake karatu a jami’ar da ‘yan ketare masu shirin mu’ammalar ilmi a cikin kasar. Sanawar ta ce, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bisa la’akari da batun tsaron kasar. Gwamnatin Amurkta ta matsa lamba kan jami’o’in kasar ciki hadda Harvard ta hanyar katse ayyukansu dake da nasaba da kasashen ketare da hana baiwa dalibai Sinawa bizar shiga kasar ba gaira ba dalili, matakin da ya bullo da ainihin burinta na amfani da sunan wadannan jami’o’i don cimma nasarar matakanta na siyasa. Ba...
    Gobara ta tashi a otal ɗin Imaratus Sanan da ke birnin Makkah a ƙasar Saudiyya, inda sama da alhazan Najeriya 48 suka sauka yayin aikin Hajjin shekarar 2025. Otal ɗin yana unguwar Sharamansur a birnin Makkah. Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa dukkanin alhazan sun tsira kuma babu wanda ya ji rauni. A cewar NAHCON, hukumomin gaggawa na Saudiyya da ma’aikatan otal ɗin sun gaggauta kashe wutar kafin ta bazu. Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya ziyarci otal ɗin tare da wasu jami’an hukumar domin duba halin da ake ciki. Ya bayar da umarnin a kwashe alhazan zuwa wani sabon otal cikin gaggawa,...
    A ‘yan kwanakin da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da masu masana’antu da ‘yan kasuwa na kasa da kasa, inda ya karfafa musu gwiwar kara gudanar da harkokinsu da zuba jari a kasar Sin. Roland Busch, shugaban kwamitin darektoci na kamfanin Siemens yana daya daga cikin baki mahalarta ganawar. A yayin da yake zantawa da wakiliyar CMG, ya bayyana cewa, shugaba Xi da kansa ya halarci ganawar, wanda ya isar da sakon cewa, kasar Sin za ta kara bude kasuwarta, da maraba da kamfanonin kasashen waje da su gudanar da kasuwanci da zuba jari a kasar, lamarin da ya burge kowa da kowa kwarai da gaske.   Roland Busch ya jaddada cewa, kamfaninsa bai taba yin...
    ’Yan Sanda sun kama wani mutum mai suna Mohammed Sani mai shekara 31 da duniya, bisa zargin dukan matarsa Hauwa mai ɗauke da juna biyu, wanda ya zama ajalinta. Lamarin ya faru ne a gidansu da ke unguwar Banin Hashim da ke Minna, a Jihar Neja. Sojojin Isra’ila sun kashe mutum 13 a wajen rabon tallafi a Gaza 2027: Makomar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na janyo cece-kuce Hauwa mai shekara 24 a duniya wadda ke ɗauke da cikin wata tara, an same ta a mace a ɗakinsu kwance cikin jini. Rundunar ’yan sandan ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar 3 ga watan Yuni, 2025. Jami’an ‘yan sanda daga sashen A Division a Minna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      CGTN ta wallafa nazarin ne a dandamalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci. Kuma mutane 5610 ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 12. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani Lauya Okere Kingdom Nnamdi, wanda ya gabatar da takardu don samun rajistar Jam’iyyar Mutanen Kasa (PPP) a ranar 28 ga Maris, 2025, ya ce bayan wata daya sai INEC ta bayyana cewa ba ta bude adireshin fara yin rajistar sabbin jam’iyyun siyasa. Jami’an INEC da suka yi magana kan lamarin, sun musanta zarge-zargen. Sun bayyana cewa duk da cewa an karbi bukatar yin rajista har guda 104, ana ci gaba da gudanar da bincike, sannan kuma tsarin zai fara gudana nan ba da dadewa ba ta hanyar sadarwaar zamani don inganta gaskiya da ingancin aiki. “Hukumar ta amsa wa masu nema. Ba daidai ba ne a zargi INEC da jinkirin amsa bukatun yin sabbin rajistar. Za a bude Shafin...
    Sojojin Rasha sun kai hare-hare mafi muni akan cibiyoyin soja da muhimman cibiyoyi a kasar Ukiraniya da su ka hada da birnin Kiev. Sojojin na Rasha sun yi amfani da kamamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki masu kai harin kunar bakin wake da su ka haddasa tashin gobara. Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kharikiev ya bayyana cewa; A kalla mutane 10 su ka jikkata a bisa kididdigar farko.  Ita kuwa rundunar sojan saman kasar ta Ukiraniya ta sanar da cewa; an yi amfani da makamai masu linzami samfurin “Cruise” wajen kai harin. Su ma sojojin na Rasha sun sanar da cewa, sun kai wa Ukiraniya hare-hare akan sansanonin soja da kuma muhimman cibiyoyin kasar ta hanyar...
    A rana ta biyu tabukuwan  babbar salla, sojojin HKI suna ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyasahi da kuma rusa matsugunansu a yankin Gaza. A yau Asabar kadai gwamman Falasdinawa ne su ka yi shahada a cikin sansanonin da Falasdinawa suke gudun hijira a cikinsu. An sami shahidai 5  da kuma wasu mutane  biyu da su ka jikkata a kusa da cibiyar rana kayan agaji a yammacin Rafah dake kudancin zirin Gaza. A yammacin birnin Khan-Yunus kuwa wasu Faladinawa 12 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 40 su ka jikkata saboda harin da ‘yan sayahoniyar su ka kai wa sansaninsu. A arewacin Khan-Yunus kuwa, sojojin mamayar sun ruguza gidajen Falasdinawa da dama. A kusa da cibiyar kiwon...
    Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta bayyana cewa; Matakin da Amurka ta dauka na kakaba takunkumin  shiga Amurka akan wasu ‘yan kasa da kuma wasu kasashen musulmi yana nuni da yadda Amurkan take adawa da musulmi. Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta ce; Daukin matakin hana wasu mutane yin tafiya saboda  kasar da su ka fito, ko addininsu yana nuni ne da yadda Amekin take jin fifiko da kuma nuna wariya. A karshe ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira ga MDD da sauran cibiyoyin kasa da kasa na shari’a da su dauki mataki karara kuma a fili akan abinda Amurka ta yi, da ya sabawa duk wani ma’auni na ‘yan adamtaka. A ranar...
    Za su fara wasansu na farko da kungiyar Wydad Casablanca ta Morocco a Philadelphia ranar 18 ga watan Yuni, za a bude kasuwar musayar ‘yan wasa har zuwa ranar 10 ga watan Yuni domin karbar kungiyoyin da ke son sayen ‘yan wasa a gasar cin kofin duniya kafin a sake budewa a ranar 16 ga watan Yuni. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A shekarar da ta gabata, kamfanin Dangote ya biya haraji N450 biliyan – wanda ya fi dukkan bankunan Nijeriya suka hada jarin harajin da suka biya. Wannan shiri na gina hanyoyi yana cikin shirye-shiryen gwamnati na ba da rangwamen haraji domin inganta kayayyakin more rayuwa a kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wasu lokuta, matsalolin suna fitowa kai tsaye sakamakon rashin fahimta daga mataki na kasa, wadada a wasu lokutan ba su da wata alaka da sakatariyar jam’iyyun da ke mataki na sama. Ko a cikin jam’iyyar APC da ke mulki, akwai jayayya a cikin rassan jihohinta da ba su warware ba kuma suna barazanar ga damar jam’iyyar a jihohin da abin ya shafa. Wasu masana harkokin siyasa sun bayyana cewa rarrabuwar kawunan ta samu ne sakamakon nuna iko tsakanin wasu mutane a wasu jihohi. Akwai batun wanda ke da iko da tsarin jam’iyyar shi ne shugaban jam’iyyar a jihar. Yayin da wasu ke cewa wannan shi ne tushen da ya haifar da rarrabuwar kawuna da ke faruwa a cikin tsarin...
    Wasu sahihin rahotannin daga cikin gwamnatin sun shaida cewa Gwamna Eno ba zai iya sauya sheka zuwa APC ba tare da amincewar Emmanuel ba, domin yin hakan na iya jawo masa asarar goyon bayan mambobin majalisun kasa da na jihar, ciki har da sauran muhimman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. An kuma tattaro cewa wani bangare na shirin fadar shugaban kasa shi ne, dukkan jihohin Kudu Maso Gabas su kasance na APC. Gwamnonin kamar Hope Uzodimma su ne kan gaban wajen yin matsinlamba ga Gwamnan Peter Mbah na Jihar Inugu, Aled Oti na Jihar Abiya da Chukwuma Soludo na Jihar Anambra don su sauya sheka zuwa APC. Duk da haka, rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Inugu bai bayar da...
    Yanzu mun yi hakan a kananan Hukumomi takwas,zuwa Lahadi mai zuwa,zamu je ta tare. Zamu ci gaba da yin hakan har zuwa watan Nuwamba wanda hakan zai sa mu kammala da kananan Hukumomi 27. Zuwa yanzu ana ganin amfanin abinda aka yi,a duk kananan Hukumomi da muka ziyarta. Ina ganin mun yi rawar gani kan muradai 12,amma kamar yadda na ce al’ummar Jigawa sune wadanda ya dace su yi bayani kan irin ayyukan alkhairi da ci gaban da muka yi a matsayinmu na gwamnati.   Da aka yi ma shi maganar ya ware kashi 30 cikin 100 saboda bangaren ilimi,cewa ya yi ai Jigawa Jiha ce da take da manoma. Domin kuwa kusan kashi 85 zuwa 90 na yawan al’ummar...
    Shugaban kasar Amurka ya ci gaba da fadin kalamai na zagi ga tsohon mai taimaka masa a harkokin gwamnati bayan sun babe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana cewa hamshaken  attajirin ya haukace. Labarin ya nakalto Fadar white house na karyata zancen cewa mutanen biyu zasu dinke barakan da ta faru a tsakaninsu wanda yasa shugaban ya kore shi. Wani mai Magana da yawun fadar white House yana cewa shugaban bai da wani shin a Magana da Musk a yau. Ya ce Trump ba ya kaunar sake ganinsa, duk da cewa Musk ya bayyana anniyarsa ta gyaran barakar da ta barke a tsakaninsa da maigidansa shugaba Trump. A safiyar jiya Jumma’a Trump ya fadawa radiyon...
    Abu Ubaida kakakn dakarun Ezzuddeen Al-Qassam reshen soje na kungiyar Hamasa ya bayyana cewa dakarunsa zasu ci gaba da Yakar sojojin yahudawa har zuwa korarsu daga yankin zirin Gaza. Abu Ubaida ya kara nda cewa, dakarun Hamas suna a madaka ga sojojin HKI babu jada baya babu janyewa daga matsayinsu. Kafin haka dai a jiya Jumma’a dakarun na Hamas tare da hadin guiwa da na Saraya Qudus sun aiwatar da wani shiri ko tarko kan sojojin yahudawan wanda ya sami nasara halaka sojojin yahudawa da dam. Majiyar yahudawan sun tabbatar da aukuwar hare-haren na Khan Yunus dake kudancin Gaza, wanda kuma ya halaka yahufawa da dama., Abu ubaida ya kammala da cewa aikin soje da suka yi a Khan Yunus...
    Kafafen yada labarai na HKI sun tabbatar da mutuwar wasu da dama daga cikin sojojin su a wani tarkon da dakarun Hamas suka yi masau a garin Khan Yunus na Gaza, wasu sun ji nrauni, sannan har yanzun akwai wadanda ba’a fito dasu daga karkashin burbushin gine-gine ba. Kamfanin dillancin labatan IP na kasar Iran. Majiyar yahudawan ta kara da cewa karfin da kungiyar Hamas ta tokwarorinsu suke da shin a halaka sojojin HKI kamar haka ya Sanya shakku a kan yiyuwar samun nasara a kansu. Kamfanin dillancin labaran Hadashot Bazman na yahudawan ya tabbatar da cewa an kashe yahudawa 5 sannan wasu 12 sun ji Rauni a yayinda har yanzun ba’a san halin da wasu daga cikin sojojin suke ciki...
    A yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, a duk irin kalubalen da za a iya samu daga waje, masana’antun kasar Sin za su ci gaba da zama ababen nema a duniya, kuma kasuwannin kasar za su kasance a ko yaushe masu jan hankali wajen zuba jarin waje. An ba da rahoton cewa, a yanayin tangardar da tattalin arzikin kasa da kasa ke fuskanta, huldar kasuwanci da tattalin arzikin kasar Sin da sauran kasashen duniya na nan daram ko gezau. A cikin watanni biyar na farkon wannan shekara, kasar Sin ta bude hanyoyin sufurin jiragen sama na dakon kaya na kasa da kasa guda 101, kuma an kara yawan zirga-zirgar jiragen sama na...
    Akalla mutane hudu ne, ciki har da wani matashi dan shekara 13, an ce an harbe su tare da fille kawunansu a ranar Alhamis a yankin Gangaran Kwata da ke karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato. Mazauna yankin sun ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe biyu na tsakar daren ya haifar da tashin hankali a yankin na Mangu. Sojoji sun dakile hare-haren ‘Yan Boko Haram biyu a Borno Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Abdullahi Maicibi, shugaban addini a yankin Kwata, ya tabbatarwa da wakilin Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce an dauki gawarwakin wadanda aka kashe zuwa babban masallacin Mangu da ke garin Mangu domin yin sallar jana’iza. Shagari Madaki, another resident, said...
    “Gidauniyarmu ta farko da aka kafa a shekarar 1952, ta tallafa wa masu fasaha daban-daban na Afirka, ta hanyar ba su damar shiga kasuwannin duniya. Gidauniyar Egbuagu, wadda aka kaddamar a yau; za ta mayar da hankali ne wajen kula da ayyukan shari’a, domin taimaka wa ‘yan Nijeriyan da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba,” in ji shi. “Babban bangaren da za mu bai wa fifiko shi ne, na matasan fursunoni, masu basirar kirkire-kirkire. Muna so mu taimaka musu su yi amfani da kwarewarsu, domin samun damar rike kawunansu ko da kuwa a gidajen yarin ne. Kazalika, bincikenmu zai mayar da hankali kan shekaru da kuma yanayin daurin da aka yi musu.” Dangane da batun hadin gwiwa kuwa,...
    Idan za a tuna dai kamfanonin samar da wutar lantarki a kwanakin baya sun gargadi gwamnatin tarayya kan ci gaba da rike musu basuka wanda yanzu ke neman kai wa naira tiriliyan 4. A kwanakin baya ne kwamitin majalisar datawa mai kula da wutar lantarki ya nuna damuwarsa kan matsalar karancin wutar lantarki da ta dabaibaye bangaren wutar lantarki, inda ya koka da yadda karancin kudin wutar lantarki a masana’antar, ya nuna cewa gwamnati na rike da kudaden kamfanonin da ke samar da wutar lantarki kusan naira biliyan 200 a duk wata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Adadin ‘yan jarida wadanda suka yi shahada a Gaza ya karu zuwa 226 tun bayan fara kisan kare dangi kan yankin Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar a yau Juma’a cewa: Adadin ‘yan jaridun da suka yi shahada ya karu zuwa 226, bayan sanar da shahadar dan jarida Ahmed Qaljah. Ofishin ya bayyana cewa: Yawan ‘yan jaridan da suka yi shahada ya karu zuwa 226 tun farkon yakin kisan kare dangi kan zirin Gaza, bayan sanar da shahadar daya daga cikin ‘yan jaridan Falasdinawa: Ahmed Qaljah, wanda ya yi aiki a matsayin mai daukar hoto na gidan talabijin na Al-Arabiya. Ofishin ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai hare-haren wuce...
    A zangon farkon 2025, jihohi bakwai din dukkaninsu na neman naira biliyan 46.80 daga asusun gwamnatin tarayya domin cike gibin kudin shiga da biyan basukan da suke yi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da ke samun goyon bayan sojojin sama Air Component sun kashe wasu manyan kwamandojin Kungiyar ISWAP guda uku. Rundunar ta kashe kwamandojin ne a harin ta’addanci da ba a yi nasara ba a kan Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam a Jihar Borno. Sallah: Gwamna Inuwa ya yi kiran sadaukarwa da haɗin kai Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Wata majiya mai tushe daga jami’an rundunar ta OPHK ta tabbatar a ranar Alhamis din nan cewa, kwamandojin da aka bayyana sunayensu: Amir Abu Ali Weldone da Amir Ibunu da Amir Abu Waldume, na daga cikin wadanda aka kashe a harin da aka kwashe sa’o’i hudu ana yi a sansanin ‘yan...
    Kwamishinan Harkoki na Musamman a Jihar Akwa Ibom, Mista Ini Ememobong, ya yi murabus daga muƙaminsa biyo bayan sauya sheƙar Gwamna Umo Eno daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC. Sallah: Gwamna Inuwa ya yi kiran sadaukarwa da haɗin kai Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC Gwamna Eno ya faɗa wa kwamishinoninsa cewa duk wanda ba ya son bin sa zuwa APC ya ajiye aikinsa. Ememobong, ya ce yana girmama ra’ayin gwamnan, amma ba zai iya binsa APC ba. “Ba zan iya yin wannan tafiya ba,” in ji Ememobong. “Na yarda da siyasar aƙida. Na gode wa gwamna bisa ƙauna da...
    Wani rahoton tsaro da hukumar Kididdiga (NBS) ta fitar a watan Disamban 2024, ta ce, yawan kudin fansa da jama’an Nijeriya suka biya ya zarce naira tiriliyan 2.23 ga masu garkuwa da mutane daga Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024. A cewar rahoton na CESPS, kusan kashi 65 cikin 100 na magidanta da suka fuskanci matsalar sace-sacen jama’a sun biya matsakaitan kudin fansa na naira miliyan 2.67, wanda ya kai naira tiriliyan 2.23. An fitar da rahoton ne kwana guda bayan rahoton hukumar kare kakkin Dan’adam na Nijeriya na shekarar 2024, ya nuna cewa akalla mutane 526 ne aka kashe a wasu munanan hare-hare tare da yin garkuwa da wasu 949 a wasu sassan kasar. Duk da masana sun sha nusar...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aika da sakon taya murnar Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi, yana kira gare su da su rungumi darajoji na sadaukarwa, biyayya da hakuri irin wanda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna. A wata sanarwa da Daraktan Yada labarai na gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Gwamnan ya yi kira da a yi addu’o’in zaman lafiya da haɗin kan Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya. Ya jaddada muhimmancin nuna soyayya, tausayi da zama mai ƙyau da maƙwabta a rayuwar yau da kullum. “Yayin da muke murnar Babbar Sallah, mu yi tunani kan abin da take nufi biyayya, sadaukarwa da ƙwarin gwiwa,” in ji Gwamna Yahaya, yana mai ƙarfafawa al’umma da su ci gaba da...
    Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC. Ya bayyana hakan ne a hukumance a ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar da ke Uyo, babban birnin jihar. Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda Wannan mataki ya biyo bayan wasu kwanaki da ya shafe yana nuna sha’awarsa na sauya sheƙa. A wani taron jama’a da aka gudanar a Ikot Abasi, ya ce: “Lokaci ya yi da za mu motsa” domin a haɗa kai da Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta. Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan...
    Domin shawo kan wannan matsalar, ministan ya zayyana kokarin da ake yi a karkashin dabarun bunkasa kiwon dabbobi na kasa, wanda ya mayar da hankali kan ginshikai guda 10 da suka hada da bunkasa kimar dabbobi, inganta kiwo, kiwon lafiyar dabbobi, samar da kudi, sauya salon kiwo da karfafawa matasa da mata gwiwa kan dogaro da kai. Maiha ya yi tunin cewa zuwa yanzu ma’aikatar ta samu cimma wasu nasarori da suka hada da yin rajistar nau’in kiwo guda takwas, “na farko a cikin shekaru 48” da kuma samar da wani shiri na kasa kan albarkatun halittun dabbobi tare da hadin gwiwar FAO. “Dabbobinmu na cikin gida suna samar da lita 1-2 na madara a kullun, idan aka kwatanta da...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnatin jihar Zamfara tana taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana ta Babbar Sallar.   “Babbar Sallah tana bai wa Musulmi damar girmama sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya yi na ɗansa domin biyayya ga umarnin Allah.   “Tana tunatar da mu muhimmancin imani, rashin son kai, da sadaukarwar da muke da ita ga al’umma da bil’adama, ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani a kan kimar sadaukarwa da biyayya ga Allah Maɗaukakin Sarki.   “Dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da duk wani nau’i na munanan ɗabi’u da kuma laifuka da suka shafi al’ummarmu.   “Haƙƙinmu ne na gamayya mu yi aiki don tabbatar da tsaron al’ummarmu,...
    Miliyoyin musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya suka gudanar da sallar Layyah, wanda yake daga cikin manya-manya bukukuwa a cikin addinin musulunci. Tashar talabijin na Press tv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan sallar wanda maniyya da kuma sauran musulni suke yi ya hada da yanka dabba gwagwadon hali, da kuma raba namansa a tsakanin mabukata musulmi. Don tunawa da annabi Ibrahim a lokacinda ya yi kokarin yanka dansa annabi Isma’ila duk da cewa shi kadai ne yake da shi. Kuma yana sonsa, da yayi haka sai All..T ya fance shi da rago, don haka a mai makon dansa ya yanka rago, Ana son duk musulmi baligi wanda ya ke da lafiya da ikon zuwa...
    Kotun kasa da kasa ta ICC ta yi tir da gwamnatin kasar Amurka wacce ta kakabawa al-kalan kotun guda hudu saboda hannu da suke da shi wajen fidda sammacin kama fray ministan HKI Benyamin Natanyahu. Kotun ta kara da cewa tana goyon bayan alkalanta kuma zata ci gaba da aikinta na tabbatar da adalci a duniya duk tare da abinda suke faskanta. Kotun ta bayyana cewa tana aikinta ne bisa goyon bayan kasashen duniya 125 wadanda suka fito daga dukkan kusruwowin duniya. Takunkuman dai ya shafi wadannan alkalai su 4 kuma mata. Kuma sun hana ko wanne daga cikinsu, shiga kasar Amurka kuma idan suna da kadarori ko kudade gwamnatin Amurka ta kwace su. A cikin watan Nuwamban shekara ta...
    Gwamnatin kasar Saudiya ta yi amfani da fasahar kirkirarren tunani ko (AI) don sauwakawa kanta da kuma mahajjata a hajjin wannan shekara ta 2025, kama daga kula da cinkoson mutane, kiyaye lafiyar mahajjata da haka kuma ta kyautata ayyukan mahajjata a cikin nutsuwa da rashin damuwa. Jaridar ArabNews ta kasar Saudiya ta bayyana cewa tare da wannan fasahar ta kula da zafin dukkan wuraren da mahajjata zuwa zuwa da kuma hana cinkoson mutane a kewayen Kaaba da sauran wurare.. Jami’I mai kula da bangaren kirkirerren fasaha wato AI na aikin Ajjin bana ya shaidawa Jaridar ArabNews kan cewa sun kirkiro abubuwa da dama don sawwaka aikin hajji ga mahajjata da kuma khidimomin da kasar saudiyya take yiwa mahajjata, Ya ce...
    Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mohammed Lawal Uwais ya rasu yana da shekaru 89 a duniya. Mmarigayin, wanda ya kasance Alkalin Alkalan na tsawon shekaru 11 daga 1995 zuwa 2006 ya rasu ne a Abuja ranar Juma’a. Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda Wani mutum ya mutu a cikin rijiya a Kano Wata majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar da rasuwar sannan ta ce shirye-shirye sun kankama na yi wa mamacin jana’iza. An dai haifi marigayin ne a ranar 12 ga watan Yunin 1936 a Zariyan jihar Kaduna. A zamanin da yake shugabancin Alkalan, ya kawo sauye-sauyen shari’a da dama musamman a bangaren fadada harkokin siyasa, inda hakan ya zama silar...
    “Idan za ku yi adalci a gare mu, a cikin makonni biyu da suka gabata, za ku ga cewa sojojin suna samun nasara wajen karya lagon ‘yan ta’adda, inda suka kashe su tare da tarwatsa sassaninsu,” in ji ministan. A karshen makon da ya gabata, wadanda ake zargi ‘yan ta’adda na Boko Haram sun dasa na’urorin fashewa a Unguwar Guzamala na Jihar Borno, inda suka kashe mutane tara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ce an samu yawan mace-macen ne saboda rashin bin umarnin gargadin ambaliyar ruwa daga mutane a jihar. Ya bukaci jihohi su dauki matakai don hana mummunar ambaliyar ruwa da ka iya lalata rayuka da kadarori, ministan ya ce, “Ma’aikatar Tarayya ta Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli tana mika ta’aziyya ga gwamnatin da al’ummar Jihar Neja, musamman ga al’ummomin da lamarin ya shafa a Mokwa, wadanda suka fuskanci asara, mutuwa da canjin wuri sakamakon wannan bala’i na ambaliyar ruwa. “Ina jaddada cewa ambaliyan da aka samu ba ta kasance saboda sakin ruwa daga dam din Kainji ko Jebba ba ne, domin duka dam din suna cikin tsaro. “Mun yaba da kokarin gaggawa na gwamnatin Jihar Neja da hukumomin yankin, da...
    Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki wajen kai hare-hare a kan birnin Kiev da kuma wasu gundumomi 9 na kasar. Rundunar sojan saman kasar Ukiraniya ta ce; Kasar tasu ta fuskanci munanan hare-hare da makamai masu linzami a cikin gundumomin gabashi, yammaci da kuma babban birnin kasar Kiev. Rundunar soja da take tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kiev ta sanar da cewa; Daga cikin wuraren da aka kai wa hare-haren da akwai tashar jirgin kasa, hakan nan kuma muhimman cibiyoyi da gidajen fararen hula. Magajin birnin Vitali Klitschko ya sanar da cewa; Mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu mutane 20 su ka jikkata sanadiyyar harin na Rasha. Haka nan kuma...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahotannin daga kasar Lebanon sun ce jiragen HKI sun kai hare-hare sau 17 a cikin unguwar Dhahiya a birnin Beirut. Kafafen watsa labarun HKI sun ce; harin shi ne mafi girma da HKI ta kai a Lebanon tun bayan tsayar da yaki, kuma tuni sojojin na HKI sun kafa na’urorin kakkabo makamai a arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya saboda harin da za a iya kai ma ta daga Lebanon. Kananan jiragen yaki marasa matuki masu yawa sun rika yin shawagi kasa-kasa a saman birnin Beirut, tare da yin kira ga mazauna yankin da su fice daga gidajensu. HKI ta riya cewa, wurin da ta kai wa harin, masana’anta ce ta kera jiragen sama marasa matuki, lamarin da majiyar Lebanon ta...
    Kafafen watsa labarun kasar ta Zambia da kuma jam’iyyarsa ta “PFT” sun sanar da cewa; Tsohon shugaban kasar ya fadi ne a lokacin da yake motsa jiki a gidansa dake birnin Lusaka. Bayan da aka kai shi asibitin soja na “Maina Soko” likitoci sun tabbatar da cewa ya rasu. Gwamnatin kasar ta Zambia ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar, tare kuma da shelanta ranakun alhini na kasa. Shi dai Lunga ya jagorancin kasar ta Zambia ne daga 2015 zuwa 2021 da ake yabonsa da gina muhimman cibiyoyi a kasar, sai dai kuma hakan ya bar kasar da dimbin bashi. Ya zuwa yanzu dai ba a sanar da lokacin da za a yi jana’izar tsohon shugaban kasar ba.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin.   Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a yanzu matasa sukayi watsi da su wadanda kuma na da muhimmanci yayin bukukuwan sallah a da can baya wanda kuma suke ganin ba a yin su a yanzu. Ko wadanne irin al’adu kenan na bukuwan sallah da dattawa ke ganin anyi watsi dasu. NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah...
    Abdullahi ya ce, an dauko wanda ya fadan a sume amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.   Ya kara da cewa, an mika gawar marigayin ga Hakimin Kawon Arewa, Alhaji Hamisu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yau ce ranar muhalli ta duniya. An yi sharhi a baya cewa, a cikin ’yan shekarun nan, kasar Sin ta jagoranci ayyukan samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a duniya, da samun gagaruman nasarori a fannin raya makamashin da ake sabuntawa da sauran fannoni, da taimaka wa sauran kasashe masu tasowa wajen aiwatar da ayyukan sauyin makamashi. Yayin da yake amsa tambayoyi a wurin taron manema labaru da ya gudana a yau, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance mai fafutukar neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a ko da yaushe, kana mai taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi ta wannan fuskar...
    A cewarsa, jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa da ke cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun rufe babbar hanyar, sun fara yin fashi ga matafiya a ranar 4 ga watan Yunin 2025.   Nan take aka tura tawaga a ƙarƙashin jagorancin babban jami’in ɗansanda (DPO) da ke kula da caji ofis ɗin Toro, tare da haɗin guiwar sauran jami’an tsaro inda suka nufi wurin da nufin daƙile fashin.   Da isarsu wurin, suka fara musayar wuta inda jami’an tsaron suka samu nasarar fatattakarsu wanda hakan ya janyo da dama daga cikin ‘yan fashin suka gamu da raunuka na harbin bindiga sannan an harbe daya ya mutu nan take.   LEADERSHIP ta rawaito cewa, an miƙa gawar Shagari ga...
    “Al’ummar kasa da kasa da yawa sun sauya ra’ayinsu mai kyau game da Amurka zuwa mummunan ra’ayi, yayin da yawan masu nuna kauna ga kasar Sin ya karu.” Wani bincike da kamfanin bincike na Morning Consult na Amurka ya fitar kwanan nan ya nuna cewa, har zuwa karshen watan Mayu, yawan al’ummar duniya dake nuna kauna ga Amurka ya ragu zuwa -1.5, yayin da adadin ya karu zuwa 8.8 ga kasar Sin. Ko da yake sakamakon ya fito ne daga hukumar bincike guda daya kawai, amma yana da ma’ana sosai wajen yin kashedi, idan aka yi la’akari da cewa binciken ya shafi kasashe da yankuna fiye da arba’in, inda akasarinsu su ne muhimman abokan huldar Amurka a fannin tattalin arziki...
    A wani hari ta kasa da na sama, rundunar sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wasu manyan hare-haren ta’addanci guda biyu a ranar Alhamis a Jihar Borno. Dakarun sun kashe da dama daga cikin maharan tare da kwato tarin makamai da alburusai. Wani mutum ya mutu a cikin rijiya a Kano Mahajjata kusan miliyan biyu na hawan Arfa a Saudiyya Rahoton da hukumar tsaron sojan Najeriya suka fitar na nuna cewar, dakarun sojan rundunar ta OPHK an kaddamar da hare-haren ne a wasu wurare daban-daban na sojoji a Buratai da ke karamar hukumar Biu da kuma Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam. An bayyana cikakkun bayanan hare-haren a cikin wata sanarwa da Mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na...
    Hakika abin da suke yi shi ne kokarin cika alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta sanya, na taimakon yankunan karkara na kasashen Afirka wajen samun hakikanin ci gaba, inda za a kyautata muhallin rayuwar mutane, da fitar da su daga kangin talauci, maimakon samar da karuwar adadin tattalin arziki kawai. Kana a bayan manufar ta kasar Sin akwai wani tunani mai muhimmanci da kasar ta rike, wato na “Gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”. A ganin kasar Sin, dukkan al’ummun kasashe daban daban suna zama a duniya daya, don haka suna da makomar bai daya. Saboda haka ya kamata a lura da bukatun sauran kasashe, da tabbatar da ci gaban mabambantan kasashe na bai daya, yayin da...
    Wani matashi dan shekara 33 mai suna Muhammad ​​Sagir ya rasa ransa bayan ya fada rijiya a unguwar Kawon Alhaji Sani da ke karamar hukumar Nasarawa a Jihar Kano. A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, mataimakin jami’in kashe gobara (ACFO) Saminu Yusif Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:42 na rana a ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025. Tsohon Ministan Ilimi, Farfesa Jibril Aminu, ya rasu Ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga wani mai suna Sabi’u Muhammed, inda ya sanar da su lamarin. “Nan da nan aka tattara tawagar ceto daga hedkwatar hukumar zuwa wurin.” “Da isowar jami’an, ma’aikatan sun gano wani mutum guda...
    Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiyan ya zanta ta wayar tarko tare da shugaban kasar Masar abdulfatta Assisi, inda suka taya juna murnar tahowar sallar Babba. Shugaban ya bayyana cewa kasar Iran tana da tsari ta makobta farko, don haka ne take, kara kyautata dangantaka da kasashe makobta da kuma musamman kasar ta Masar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a wata wayar tarho ta daban shugaban ya zanta da Yarima mai jiran gadon sarautan saudiya kuma Firay ministan kasar Muhammad bin Salman inda ya taya shi murnar zagayowar ranar Sallah babba sannan suka yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu. Duk tare da bambancin ra’ayin da kasashen biyu suke da shi dangane da yadda za’a warware...
    Mai bawa jagoran Juyin juya halin musulunci shawara kan al-amuran siyasa Ali Shamkhani ya sake tabbatar da cewa kasar Iran ba zata dakatar da aikin tace makamacin Uranium kamar yadda gwamnatin Amurka take so ba. Sannan ya kara da cewa kasar tana kokarin sake gabatar da wata shawara daban ga kasar Amurka. Ali shamkhani ya fadawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon a wata hira da ta hadasu a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu suna rubutun wata shawagara ga gwamnatin Amurka dangane da hakan. Shamkhani ya kara da cewa wasikar da Amurka aikawa Tehran bata ambaci batun daukewa kasar takunkuman tattalin arziki ko kadan ba. Ya kuma soki kasar ta Amurka a wasikar da...
    Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai kawo ziyarar aiki Tehran nan ba da dadewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran. Labarin ya kara da cewa kasashen biyu sun kulla yarjeniyoyi masu yawa a tsakanin daga ciki har da masu dogon zango. Kazem Jalali ya bayyana a yau Alhamis kan cewa kasar Rashe ce kasa tilo wacce ta zuwa jarin dalar Amurka biliyon $8 a bangaren  gas da man fetur. Kuma ya zuwa yanzu ta kashe dala $ 5bl daga cikinsu. Banda haka zata kashe kudade don kammala layin dogo wacce ake kira hanyar Arewa zuwa Kudu. Banda haka Rasha zata fara tura danyen man fetur daga Rasha zuwa Iran don...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qolibof ya bayyana cewa kungiyar BRICS wata dama ce ta kaucewa danniya da babakeren da Amurka take kudaden sauran kasashen duniya. Qolibof yana bayyana haka ne a lokacin ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar Brazil Dowi Alku-Lomubre a gefen taron shuwagabannin majalisun dokokin kungiyar BRICS wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Brazia na kasar Brazil. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin Iran yana fadar cewa kasashen Iran da Brazil suna da fahinta iri guda dangane da yenci da kuma zama yentacciyar kasa. Don haka tare da wannan ana iya gina dangantaka ta bunkasar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu tare da wannan fahintar. Qolibof ya kara...
    Farfesa Jibril Amin Likita kuma tsohon malamin Jami’a, ya rasu a jiya  Laraba yana dan shekara 85 a duniya. Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto majiyar iyalar mamacin na tabbatar da haka. Ta kuma bayyana cewa kwamishin gidaje a jihar Adama Hon Abdullahi Prambe ya tabbatar da labarin. Sannan ya kara da cewa an yi masa sallar Jana’iza a babban masallacin kasa a Abuja a yau Alhamis. Sannan za’a maida shi garinsa Song na jihar Adamawa inda za’a rufe shi. A rayuwarsa dai Farfesa AAmin likitan zuciya ne, sannan malami da shugaba Jami’ar Maiduri na Jahar bornin a wani lokaci, ya kuma karantar. Har’ila yau Farfesa Amin ya rike kujerar Ministan ilmi da manfetur, sannan jakadan Najeriya A Amurka...
    Daraktan hukumar kashe gobara a jihar, Alhaji Sani Anas ya bukaci jama’a da su sanya ido sosai, musamman ganin yadda bukukuwan Sallar layya ke gabatowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan ya bayyana gabatarwar da C-WINS ta yi a matsayin mai motsa zuciya kuma mai cike da ƙarin haske. Ya ce: “A yau na koyi abubuwa da dama. Yawancin ’yan Nijeriya, kamar ni kai na, sun san cutar masassarar cizon sauro amma ba su san da ƙyandar jamus da mummunan tasirin ta ba. “Gaskiya batun cewa za a iya haihuwar yara makafi, kurame ko kuma masu nakasar zuciya sakamakon kamuwa da ƙyanda daga uwa a lokacin ɗaukar ciki babbar masifa ce da ya kamata mu haɗa kai mu daƙile ta.” Ya ƙara da cewa ma’aikatar za ta haɗa hannu da sauran hukumomin da suka dace wajen tsara saƙonnin faɗakarwa da shirye-shiryen ilimantar da al’umma. Ya kuma shawarci tawagar da su...
    A wani cigaba makamancin haka, dakarun Mallam Fatori suma sun daƙile wani yunƙurin hari daga ‘yan ta’adda da suka zo ta wurare daban-daban. Ya ce bayan sa’o’i na musayar wuta, dakarun sun bi ‘yan ta’addan da suka tsere, inda suka hallaka da dama, wasu kuma suka gudu da raunukan harbin bindiga. An kuma kwato muggan makamai da dama kamar bindigogi AK-47, da bindigar kakkaɓo jirgi (RPG), da sauran kayayyakin yaƙi. Yanzu haka Sojojin na ci gaba da sintiri a yankin, tare da goyon bayan jiragen sama da na leƙen asiri. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Tsohon malamin makaranta, dan siyasa kuma ambasada, Farfesa Jibril Aminu ya rasu yana da shekara 85. Wata majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar da rasuwar, kuma Kwamishinan Gidaje da Raya Birane na jihar Adamawa, Hon Abdullahi Prambe ma ya tabbatar da haka. Ya ce, “Ba za a taba mantawa da gudunmawar shi ba musamman a bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma shugabanci.” Wata majiya da ke da kusanci da mamacin ta ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a Masallacin Kasa da ke Abuja. Sai dai kawo yanzu, iyalai da ’yan uwan mamaci bas u fid da cikakken bayani kan yadda za a yi jana’izar mamacin ba ko kuma musabbabin rasuwarsa. An haifi Farfesa Jibril...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Babu makawa Amurka abokiyar laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa ne a Gaza A safiyar yau Alhamis ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da kira ga mahajjatan dakin Allah. Yana mai jaddada cewa; Aikin Hajji ba kamar sauran tafiye-tafiye ne da ake nufi kasuwanci, yawon bude ido, ko wasu abubuwa daban-daban ba, wadanda wani lokaci sukan hada da ibada ko ayyukan alheri. Motsa jiki ne na ƙaura daga rayuwar da ta saba zuwa rayuwar da ake so. Rayuwar da ake so ita ce rayuwar tauhidi, wacce ta kunshi muhimman abubuwa masu muhimmanci na dindindin kamar: dawafi akai-akai a kusa da kusurwoyin gaskiya, da jajircewa a tsakanin...
    Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan fitowar wani littafi mai taken Original Sin da ya zargi wani na kusa da Biden da ɓoye yadda jikinsa ya gaza yayin yaƙin neman zaɓen 2024, wanda daga ƙarshe ya janye. Wannan ya ƙara sanya tambayoyi kan ko an san da cutar sankarar da ya kamu da ita tun da wuri, musamman ganin yadda aka ce ta bazu zuwa ƙasusuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Miliyoyin alhazai ciki har da ’yan Najeriya ne suka taru a Dutsen Arfa domin tsayuwa a yayin Aikin Hajjin bana duk da tsananin zafin ranar da ake fama da shi a kasar Saudiyya. Ministan Aikin Hajji na kasar dai ya shawarci mahajjatan da su kasance a cikin tantinansu tun daga tsakain karfe 10 na safe zuwa karfe 4:00 na yamma, saboda tsananin zafin rana. Ko a ranar Lahadi sai da Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasar (NCM) ta yi gargadin cewa zafin zai iya kai wa ma’auni 47, inda ta shawarce su da su dauki matakan kariya. Musulman Kudancin Kaduna sun yi taron addu’ar zaman lafiya Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano To...
    Al’ummar Musulmin yankin Kudancin Kaduna, sun shirya taron addu’a na musamman a sakatariyar karamar hukumar Sanga da ke Gwantu, Jihar Kaduna, kan neman zaman lafiya. A yayin taron dai Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya jaddada kudirin rundunar sojin Najeriya na dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin kasar tare da yin kira ga ’yan kasa da su mara wa kokarin hadin kai da ci gaban kasa baya. Janar Musa wanda Rear Admiral Ibrahim Aliyu Shettima ya wakilta, ya ce zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaba da bunkasar kasa. Ya bukaci ’yan Najeriya baki daya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba, da su bayar da gudummawarsu wajen gina kasa. Barazanar Yajin Aiki:...
    Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata. A makon da ya gabata, rundunar ta kashe aƙalla ‘yan ta’adda 20 a wani samame da aka kai Garin Mani, da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara. Wannan farmaki ya biyo bayan luguden wuta da aka riƙa yi wa ‘yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka. Shugaban sojin ya ce motsa jiki abu ne da ya zama dole ga dukkanin ma’aikata, kuma babu wanda zai samu ƙarin girma ba tare da...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya. Ya ce PDP tana da ƙarfi kuma za ta iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027. Barazanar Yajin Aiki: Abuja da wasu jihohi 3 za su faɗa cikin duhu A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Saraki, wanda ke jagorantar Kwamitin Sulhu na PDP, ya faɗi haka ne a wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Ilorin. Ya amince cewa wasu sun bar jam’iyyar, amma mutane da dama suna ci gaba da shigowa jam’iyyar. “PDP ce kawai jam’iyyar adawa ta haƙiƙa,” in ji shi. “Eh, muna fuskantar ƙalubale, amma muna...
    Sannan Annabi (SAW) ya ce “Babu wata rana mafificiya a wajen Allah kamar Ranar Arfa”, haka nan kuma ragowar kwanakin da ke cikin 10 na farkon watan nan, Ranar Arfa ta ninninka su falala. Don a wannan ranar ce Annabi (SAW) ya ce Ubangiji yana sauka zuwa saman duniya (Kamar yadda ya dace da Shi (SWT). Ire-iren waɗannan Hadisan ne ake ce musu “Mutashabihai”. Ana kawo bayanansu ne ta yadda za a yi mana kwatance amma ba kamar yadda ma’anar lamarin yake a hulɗar da ke tsakaninmu ba. Wajibi ne yin imani da Hadisan don rashin yin imani da su ridda ne, amma ba kuma a riƙa fassarawa da yadda ƙananan ƙwaƙwalenmu ke ɗaukawa ba. Duk wanda ya ce zai...
    Aliyu, ya bayyana cewa Jibrin manomi ne daga ƙauyen Gargai da ke ƙaramar hukumar Bebeji a Kano. Ya kuma ce yana fama da cutar gyambon ciki da hawan jini. Likitoci sun bayyana cewa rasuwarsa ta faru ne sakamakon bugun zuciya da gazawar zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu. Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024. A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ƙorafe-ƙorafen nasu sun haɗa da rashin biyan kuɗin fansho na tsawon watanni 16, rashin ƙarin girma, rashin kula da lafiyar ma’aikata. Sun kuma ce an ƙi biyansu ladan aiki na shekarar 2024 duk da cewa sun taimaka wajen samar da kuɗin...
      Mazauna unguwar da asibitin kula da ido ta kasa yake wato Mahuta da ke jihar Kaduna sun amince da Gwamna Uba Sani ya zarce karo na biyu, biyo bayan warware takaddamar filaye da aka dade ana yi wanda ya yi sanadiyar rushe gidaje da dama a gwamnatin da ta gabata. Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Kaduna ta hannun hukumar kula da bayanan kasa ta jihar Kaduna (KADGIS) ta bayar da shedar mallakar filayen sama da 300 ga al’ummar da rusau da aka yi a zamanin tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya shafa. Da yake jawabi a madadin mazauna yankin, Kanar Haruna Idris Zaria mai ritaya, ya yabawa Gwamna Sani bisa abin da ya bayyana a matsayin tsarin sa...
    Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake tabbatar da cewa Iran ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba kan ‘yancinta na tace Uranium, yana mai cewa ci gaban da kasar ta samu a fannin makamashin nukiliya ya samo asali ne sakamakon sadaukarwa da kuma saka hannun jari na kasa. A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya ce, ba batun inganta makamashin Uranium a duk wata yarjejeniyar nukiliya da za a yi nan gaba. “Iran ta saka kudi da yawa domin kai wag a wannan mataki, sannan kuma ba zai sa mu yi watsi da sadaukarwar da ‘yan kishin kasa sukayi don tabbatar da burinmu. Araghchi ya bayyana tace...
    Amurka ta sake hana kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kiran tsagaita bude wuta da kuma kai agajin jin kai a Gaza. Wannan hawa kujerar na-ki shi ne irinsa na farko na sabuwar gwamnatin Trump kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan ci gaba da yakin da takeyi a gaza dama hana shigar da kayan agaji. Daftarin kudurin da aka gabatar wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba ya bukaci “a gaggauta tsagaita wuta na dindindin” da kuma sakin wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba. Kudirin da kasashe 10 wadanda ba mambobin kwamitin na dindindin ba suka gabatar, ya samu sahalewa...
    Yau Alhamis 9 ga watan Zul Hijja, ita ce ranar da miliyoyin Musulmi da ke aikin Hajji a kasar Saudiyya ke hawan Arfa, wato daya daga cikin shika- shikan aikin Hajji. Maniyyata kusan miliyan biyu daga fadin duniya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin, wanda ya kunshi dawafi da zaman Mina da tsayuwar ta Arfa da kuma jifar shaidan. A washegarin ranar ne kuma sauran Musulmai a duk fadin duniya su ke shagulgulan Sallar layya. Hukumar lura da aikin hajji ta Saudiyya ta ce yanayin zafi zai kai maki 45 a kwanakin da ake tsaka da aikin na hajji.
    Shugaba Donald Trump na Amurka ya haramtawa kasashen duniya 12 shiga Amurka a wani mataki da ya ce na kare kasar ne daga “yan ta’adda na kasashen waje. Wata takarda da fadar White House ta fitar a ranar Laraba ta ce haramcin, wanda zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Yuni, ya shafi kasashen Afghanistan, Burma, Chadi, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan, da kuma Yemen. Baya ga hakan akwai wasu kasashe bakwai su ma da aka gindawa wasu sharudda da suka hada da Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkmenistan da kuma Venezuela. A cewar Amurka matakin bai shafi mutanen da balaguron su zuwa kasar ke da amfani ga muradun kasar ba.” Haka ma...
    Wasu daga cikin mazauna yankin Mokwa da ambaliyar ruwa ta lalata wa gidaje a Jihar Neja, yanzu na zaune a sansanin ’yan gudun hijira. Ambaliyar, wadda ta kashe sama da mutum 100, ta jawo asarar dukiya da lalacewar gidaje da dama a yankin. Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ambaliyar Mokwa: An gano gawar yara 7, jama’a na neman agaji Aminiya ta kai ziyara sansanin a ranar Talata, inda ta ɗauki wasu hotuna da ke nuna halin da waɗanda abin ya shafa ke ciki da yadda suke rayuwa a sabon wajen da suka koma.   Ga hotunan a ƙasa:
    Attajirin nan na duniya dan asalin kasar Amurka, Bill Gates, ya ce a shekara 25 da gidauniyarsa ta yi da kafuwa, ya kashe Dalar Amurka biliyan 100, kwatankwacin Naira tiriliyan 161 wajen inganta kiwon lafiya a nahiyar Afirka. Attajirin ya bayyana hakan ne a Legas yayin wani taro da gidauniyarsa ta Gates Foundation ta shirya mai taken Goalkeepers, ranar Laraba. Ya ce gidauniyar ta fara aiki ne a shekara ta 2000, kuma babban makasudinta shi ne ganin an rage samun mace-macen kananan yara a fadin duniya, musamman a Afirka. Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma Bill Gates ya ce, “Ganin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata al’ada da ta zama gama gari a tsakanin matasa, ita ce yankewa da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan bukukuwan Sallah. A da, ana da wurare na musamman da ake yin irin wannan abu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa Sai dai masana sun ce wannan abu na iya haifar da matsaloli ga lafiya da kuma gurɓata muhalli. Wannan shi ne abin da shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kai, yayin da ake Bikin Ranar Muhalli ta Duniya kwana ɗaya kafin Babbar Sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
    Kasar Sin ta ci gaba da yin tsayin daka kan matsayinta na guje wa yin katsalandan musamman a Afirka. Ba kamar kasashen yammacin duniya da suka tsunduma cikin harkokin soji da makamai ba, kasar ta mai da hankali kan hadin gwiwar tattalin arziki, kamar zuba jari mai yawa a kasashen Afirka da dama ba tare da gindaya sharuddan siyasa ba. Wannan tsarin ya taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali a yankin. Kazalika, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sulhunta rikici a yankin Asiya, inda ta samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici da juna maimakon samar da mafita ta hanyar karfin soja. Sulhunta tsakanin Saudiya da Iran a shekarar 2023, tare da daidaita harkokin diflomasiyya...
    Har ila yau, ya bayyana cewa, bangaren tekun kudancin kasar Sin gaba daya yana cikin kwanciyar hankali kuma babu wata matsala game da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da na sama da dukkan kasashe ke morewa bisa doka. Ya ce, a ko da yaushe, kasar Sin na dagewa kan amfani da tattaunawa da tuntubar juna wajen warware sabani da magance abubuwan da aka sha bamban a kai game da teku yadda ya kamata a tsakanin kasashen da abin ya shafa kai-tsaye, bisa mutunta hakikanin tarihi na gaskiya. Haka nan, ya kamata kasashen da ba na yankin ba su mutunta kokarin da kasashen yankin suke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, maimakon haddasa fitina...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An gano gawar yara bakwai a yankin Mokwa, da ke Jihar Neja, bayan ambaliyar ruwa da ta afka wa garin mako guda da ya wuce. Yawan adadin waɗanda suka rasu kawo yanzu ya kai mutum 160, amma wasu jami’ai sun ce za a iya gano gawar sama da mutum 200. Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano Sallah: Mun shirya samar da tsaro a Yobe — ’Yan Sanda Ambaliyar ta kuma tafi da motar haya mai kujeru 18 ɗauke da fasinjoji. Kawo yanzu, bayan kwana shida da faruwar ambaliyar, ba a ga motar ko wani daga cikin fasinjojin ba. Wani mazaunin garin, Baba Abu, ya ce: “Direban bai nemi ƙetare ruwan ba. Ya...
    Yanzu haka an shiga shekaru 10 na zagaye na 2 na karni na 21, kuma duniya na fuskantar kwaskwarima, da sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a tarihi, wanda ya zarce tunanin da ake yi. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana kwaskwarimar da ake fuskanta a matsayin “Babban sauyi da ba a taba ganin irinsa ba cikin karni daya”, wanda ya hada da kyautatuwar karfi tsakanin mabambantan kasashe da ya zarce zaton da aka yi a baya, matakin ya tabbatar da alkiblar da Sin za ta bi, har ma ya kunshi sauye-sauyen al’adu da wayewar kan Bil Adama. Yau za mu ganin ma’anar maganar Xi Jinping kan wannan batu dake jawo hankalinmu. Daga kanmu, magana ta...
    Gwamnatin kasar Amurka wacce ta bude cibiyoyin rarraba kayakin Agaji a Gaza, ta ce zata rufe cibiyoyin zuwa ranar Alhamis mai zuwa don sake tsara ayyukan Rabomn.  Majiyar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda sojojin yahudawan suna kashe falasdinawa wadanda suke fama da yunwa a lokacinda suka iso cibiyoyin raba abincin ko kuma suka hau kan hanyar zuwa karban abincin. Labarin ya kara da cewa a jiya Talata kadai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa mayunwata 27 a kokarinsu na karban abinci. Sannan a yau Laraba ya zuwa lokacin bada wannan labarin sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 32 a hare-haren da suka kai kan yankuna daban-daban a Gaza. Majiyar ta kara da cewa Palasdinawa 95 ne...
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Nain Qasim da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi sun gana a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran siyasa da yankin kudancin Asiya tare da kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto aragchi yana cewa dangantaka tsakanin Iran da kungiyar Hizbullah dangane ce wacce ta shafi yankin kudancin Asiya gaba daya. A nashi bangaren shugaban kungiyar Hizbullah sheikh Naem Kassem ya godewa JMI ta irin tallafin da take bayarwa ga kungiyoyi da kasashen kawancen masu gwagwarmaya a yankin wadanda suka hada da Falasdinawa da Lebanon da sauransu. Aragchi ya kara da cewa Iran a shirye take ta taimakawa kasar Lebanon a...
    Jami’an Yansanda masu kula da ayyukan ta’addanci da kuma hana aukuwarsu a nan Iran sun sami nasarar kama wasu yan kungiyar ISIS 13 a duk fadin kasar daga ciki har da shugabansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Saeed Montazer al-Mahdi kakakin rundunar FARAJA mai kula da fada da yan ta’adda yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa yan ta’addan su 13 daga cikin har da shugabansu, sun kuduri anniyar kai hare-hare a cikin Jama’a su kuma kashe mutane a wasu tarurrukan da aka gudanar a kasar nan. Labarin ya kara da cewa an kama yan ta’addan na ISIS a biranen Tehran, Qum, Esfahan da kuma Albus. Kuma an kama tare da su kayakin...
    An kama su da manyan makamai ciki har da bindiga ƙirar GPMG, bindigu ƙirar AK-47 da sauransu. Mutanen sun amsa laifin da ake zargin su, inda suka ce an biyasu Naira 500,000 domin su kai makaman daga Jihar Binuwsi zuwa Kwara. Rundunar ‘yansandan ta ce da ba a kama su ba, makaman na iya shiga hannun ‘yan ta’adda. Ana ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu a wannan harkar safarar makamai. Kwamishinan ‘yansandan, ya ce Nasarawa ba mafaka ba ce ga masu laifi, kuma za su ci gaba da yaƙi da masu safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba. Ya kuma roƙi jama’a da su riƙa sanar da duk wani abin da suka gani mai kama...
    A nasa bangare kuma, David Perdue ya ce, shugaba Donald Trump yana matukar girmama shugaba Xi Jinping, kuma yana da muhimmanci a ci gaba da karfafa mu’amala dake tsakanin shugabannin biyu. A matsayin jakadan kasar Amurka a kasar Sin, yana fatan yin mu’amala da bangaren Sin yadda ya kamata, bisa ka’idar girmama juna, da sauraron ra’ayoyin juna. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Za mu warkar da raunukan rarrabuwar kawuna da yaki da kuma kafa makomar zaman lafiya da wadata,” in ji shi. “Komai runtsi, zaman lafiya ya fi yaki.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta jaddada haramcin gudanar da hawan Durbar na shagulgulan Babbar Sallah. Wannan sanarwar na cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano. Sanarwar ta bayyana cewa an sanya wannan doka ne bisa rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu na shirin amfani da hawan Durbar domin tayar da hankali da barazana ga tsaro da doka a jihar. Rundunar ta taba sanya irin wannan haramci a lokacin bukukuwan Sallah ƙarama da suka gabata, kuma an yanke shawarar ci gaba da dokar har zuwa Sallah Babba. Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta ɗauki...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas. Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar. Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Fubara, ya samu saɓani da ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan hauwansa mulki. Saɓani kan ikon mallakar kuɗin jihar da naɗin muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar. A watan Maris 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya. Ya naɗa...
    Jami’an hukumar tsaro ta DSS da na rundunar sojojin Najeriya sun ce sun hallaka ’yan bindiga akalla 45 a kusa da garin Kuchi da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja. An dai sami nasarar ce sakamakon wani harin da dakarun suka kai cikin sirri a ci gaba da yakin da suke yi da ’yan bindiga a yankin. Majiyoyi daga cikin jami’an tsaro sun bayyana cewa jami’an DSS sun bi sahun wasu ’yan bindiga ne inda suka dakile yunkurinsu na kai munanan hare-hare, wanda kasurgumin dan bindigar nan, Dogo Gide da yaransa suka shirya kai wa. Kasa ta danne almajirai 11 sun mutu a Kaduna Uba ya harbe ɗansa har lahira saboda zaton biri ne Majiyar ta ce bayanan sirrin...