Gwamnatin Kano Da NBC Sun Shirya Taron Bita Domin Tsaftace Harkar Siyasa
Published: 24th, April 2025 GMT
Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar kula da gidajen Radiyo da Talabijin ta kasa NBC sun shirya taron yini biyu ga masu fafutukar siyasa da masu sharhi kan harkokin yada labarai.
Taron na da nufin tsaftace harkar siyasa da inganta fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasa a jihar.
An zabo mahalarta taron ne daga jam’iyyun siyasa daban-daban da gidajen rediyo a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
A nasa jawabin, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa, a karshen taron, mahalarta taron za su fahimci ladubban da suka shafi harkokin siyasa.
Ya yi Allah wadai da karuwar kararrakin batanci da sunan siyasa, yana mai cewa masu fafutuka na siyasa, masu sharhi kan harkokin yada labarai da masu gabatar da shirye-shiryen siyasa na bukatar ilimin kan kyawawan ayyuka bisa al’adu da addini.
Kwamared Waiya ya nanata kudirin gwamnatin jihar na hada hannu da masu ruwa da tsaki domin ciyar da Kano gaba da kuma baiwa ‘yan kasa damar cin moriyar dimokradiyya.
“Ba mu zo nan don shawo kan kowa ya canza sheka zuwa wata jam’iyya ba amma don tsaftace tsarin”
Shima da yake nasa jawabin, kodinetan NBC na jihar Malam Adamu Salisu ya bayyana cewa taron bitar ya yi daidai da aikin hukumar, don haka akwai bukatar hada hannu da masu ruwa da tsaki domin cimma manufofin da ake bukata.
Ya yabawa ma’aikatar yada labarai kan wannan shiri, sannan ya bukaci masu ruwa da tsaki da su bada gudunmawar ta hanyar samar da zaman lafiya.
Ya yi nuni da cewa taron ya yi daidai da aikin hukumar NBC.
Ko’odinetan jihar ya bayyana cewa masu fafutuka, masu sharhi kan harkokin yada labarai, da masu gabatar da shirye-shirye na da muhimmiyar rawa da za su taka a fagen siyasar Kano.
Da yake gabatar da kasida kan inganta magana mai kyau da kuma nisantar kalaman batanci a kafafen yada labarai ta mahangar Musulunci, babban limamin masallacin Al-furqan, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya bayyana wasu abubuwa guda uku na yada bayanai bisa koyarwar addinin Musulunci, wadanda suka hada da gaskiya, daidaito da kuma sanin yakamata.
Shugaban masu fafutukar siyasar jihar Kano, wanda aka fi sani da Gauta Club, Alhaji Hamius Danwawu Fagge, ya bayyana horon a matsayin wanda ya dace.
Ya yi alkawarin cewa mahalarta taron za su yi amfani da ilimin da aka samu wajen ci gaban Kano da Najeriya baki daya.
KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Taro yada labarai
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
Daga Usman Muhammad Zaria
Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.
Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.
Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin noma daban daban.
A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.
Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.
Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.
Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.
Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.
Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.
Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.
Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.
A garin Chuwasu dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.
Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.
Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.
Yace da farko suna da shakku akan amfani da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.
Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.
Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.
A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.
A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.
Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.
Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.