Aminiya:
2025-07-31@02:36:57 GMT

Ya isa haka: Tinubu ya umarci shugabannin tsaro su kawo ƙarshen kashe-kashe

Published: 24th, April 2025 GMT

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya  ba da umarnin gaggawa da a yi cikakken sauyi ga dabarun tsaron ƙasa, yana mai umartar shugabannin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don daƙile ƙaruwar tashin hankali da kashe-kashe jihohin Borno, Filato, Binuwai, da Kwara.

Tinubu, wanda ya gana da shugabannin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce dole ne a kawo ƙarshen kashe-kashe a jihohin da abin ya shafa.

“Ya isa haka,” in ji Shugaba Tinubu yayin da ya sake yin tir da kai hari ga ’yan Najeriya ba tare da wani dalili ba.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin tsaron sun yi wa shugaban ƙasa cikakken bayani kan halin da tsaro ke ciki.

Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa gidan rediyo na haɗin gwiwa NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci

Ribadu ya ce Shugaba Tinubu ya ba da umarnin amfani da sabbin dabaru don magance matsalolin rashin tsaro.

Ya ce, shugaban ƙasar “ya ba mu damar zuwa mu sake yi masa bayani. Ya ɗauki lokaci mai tsawo muna masa cikakken kan abin da ke faruwa.

“Ko da ya yi tafiya ƙasar waje yana yawan tuntuba, yana ba da umarni kuma yana bin diddigin abubuwan da ke faruwa. A yau kuma mun sami damar sake yi masa bayani na tsawon awanni.

“Mun saurara, kuma mun karɓi sabbin umarni daga gare shi. Gaskiya, ya nace cewa mu yi aiki tuƙuru don maido da tsaro a ƙasa.

“Mun yi masa bayani kan abin da ya faru kuma muka tabbatar masa da jajircewarmu.

“Mun aiwatar da umarninsa, mun je wuraren da ake fama da rashin tsaro, kamar jihohin Filato da Binuwai da Borno, kuma mun ba shi ra’ayinmu saboda ya ba mu umarni mu je mu gana da hukumomin siyasa a can,” in ji shi.

Ribadu ya ce Tinubu ya jaddada buƙatar ƙara shigar da ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi wajen magance al’amuran rashin tsaro.

“Matsalar rashin tsaro sau da yawa ba ta tsaya ga manyan matakai kawai ba. Ta ƙunshi ƙananan hukumomi. Su ne ke tare da mutane kai tsaye, musamman ma idan wasu ƙalubalen sun shafi matsalolin al’umma.

“Muna buƙatar yin aiki da al’ummomi  da ƙananan hukumomi da kuma gwamnoni. Shugaban Ƙasa ya ba da umarni cewa mu ƙara yin aiki da gwamnoni,” in ji shi.

Ribadu ya ce Shugaban Ƙasa ya “damu sosai” a taron kuma ya ce “abin ya isa haka.”

Ribadu ya ce maharan galibi suna kai hari ne kan ’yan ƙasa marasa galihu ta hanyar dasa bama-bamai da kuma kai hari kan wuraren da ba su da gwamnati.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Tsaro shugabannin tsaro Shugaban Ƙasa Ribadu ya ce rashin tsaro ba da umarni

এছাড়াও পড়ুন:

Zaɓen 2027: Arewa Za Ta Sake Mara Wa Tinubu Baya — Gwamna Inuwa

Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo Za Ta Taimaka Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya — Jega
  • Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa
  • Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari
  • Zaɓen 2027: Arewa Za Ta Sake Mara Wa Tinubu Baya — Gwamna Inuwa
  • Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF
  • Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga
  • Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci
  • Shugaban Kasar Masar Ya Roki Trump Ya Kawo Karshen Yaki A Gaza
  • SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa
  • Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir