Saudiyya ta Gayyaci Kasashen Larabawa Kan Batun Kan Batun Gaza
Published: 20th, February 2025 GMT
Saudiyya ta kira shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Masar da Jordan a wani taron domin tattauna batun Gaza.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne ya gayyaci shugabannin a taron na gobe Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar SPA ya ruwaito.
Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin aiki a kan wani shiri na bayan yakin Gaza da kuma sake gina Zirin a wani mataki na tunkarar shawarar shugaban Amurka Donald Trump na sake gina yankin da mayar da shi wurin shakatawa na gabar tekun kasa da kasa bayan korar mutanen Gaza zuwa wasu wurare.
Saudiyya ta ce taron na ranar Juma’a zai kasance ba na hukuma ba kuma za a yi shi ne cikin “tsarin dangantakar ‘yan’uwantaka da ke hada shugabannin,” in ji kamfanin SPA.
A cewar labarin, dangane da matakin da kasashen Larabawa suka dauka na hadin gwiwa da kuma shawarwarin da aka fitar dangane da shi, zai kasance cikin ajandar taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a Masar,” in ji SPA, yayin da yake magana kan shirin taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a ranar 4 ga watan Maris mai zuwa domin tattauna rikicin Isra’ila da Falasdinu.
Shi dai shugaban Amurka D.Trump ya yi kira ga kasashen Masar da Jordan su karbi Falasdinawa da ba su wajen zama bayan fitar da su daga Gaza, shawarar da kasashen suka yi fatali da ita.
Kasashen duniya da dama sun soki matakin na Trump, suna masu danganta shi da raba Falasdinawa da kasarsu ta gado.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen Larabawa
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu
A cikin kwanakin bayan nan ana samun karuwar sojojin HKI da suke kashe kawunansu saboda tabuwar kwakwalensu sanadiyyar yakin Gaza.
Kafafen watsa labarun HKI sun kunshi rahotanni da suke bayani akan yadda sojojin mamayar da su ka yi yaki a Gaza, suke samun tabuwar hankali, da hakan yake sa su kashe kawukansu bayan sun baro Gaza.
Wasu rahotannin sun ambaci cewa, sojojin na HKI suna rayuwa ne a cikin tsaro da ranaza saboda munanan ayyukan da su ka aikata marasa kyau.