Leadership News Hausa:
2025-11-02@17:17:23 GMT

Dangote Ya Koma Matsayi Na 86 A Jadawalin Masu Arziƙin Duniya

Published: 20th, February 2025 GMT

Dangote Ya Koma Matsayi Na 86 A Jadawalin Masu Arziƙin Duniya

Arziƙin hamshakin attajirin nan ɗan jahar Kano Alhaji Aliko Dangote ya ninka na bara inda ya ƙaru zuwa dala biliyan 23.9, wanda hakan yasa ya cigaba da kasancewa mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afrika kuma ya koma matsayi na 86 a jadawalin masu kudin Duniya kamar yadda mujallar Forbes mai ƙididdiga akan masu kuɗin Duniya ta fitar, Forbes ta zaɓi Aliko Dangote a matsayin mutum na 144 mafi arziƙi a duniya a shekarar 2024 da dala biliyan 13.

4.

Forbes ta yi kiyasin cewa dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 23.9, musamman saboda hannun jarin sa na kashi 92.3 na matatar man dangote, Aliko Dangote mai shekaru 67, ya sake zama ɗaya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya, matsayin da bai riƙe ba tun shekarar 2018, a cewar Forbes Real-Time Billionaires List.

Zargin Damfara: Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Ma’aikacin Dangote Kamfanin Harhaɗa Mota Na Dangote  Ya Kera Peugeot 3008 GT A Kaduna

Wannan ya sa ya zarce ɗan Afrika ta Kudu Johann Rupert, wanda ke matsayi na 161 a duniya yana da dukiyar da aka ƙiyasta ta kai dala biliyan 14.4, kuma ya zarce Mike Adenuga, wanda shi ne na biyu mafi arziƙi a Nijeriya kuma yake na 481 a duniya, inda yake da dukiyar da ta kai dala biliyan 6.8.

Dangote ya shiga harkar mai a shekarar da ta gabata ta hanyar gina matatar mai mafi girma a Afirka, bayan shekaru 11, ya zuba jarin dalar Amurka biliyan 23, matatar Dangote ta fara aiki a bara inda matatar da ke kan wani yanki mai girman eka 6,200 a yankin Free Zone na Lekki, za ta sarrafa ganga 650,000 a kowace rana (b/d), wanda zai zama matatar mai ta bakwai mafi girma a duniya kuma mafi girma a Afrika.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: dala biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21 October 30, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • Dan Majalisar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, Ya Koma Jam’iyyar APC
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya