Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano
Published: 19th, February 2025 GMT
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar.
Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya).
Ya tabbatar da cewa za a fitar da takarda a hukumanci don bayyana waɗanda suka ɗauki nauyin tashin hankali yayin zanga-zangar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bsture Dawaki Tofa ya fitar, zanga-zangar ta yi sanadin rasuwar rayukan mutum 10, yayin da wasu bakwai duka samu munanan raunuka.
Hakazalika ya ce an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11.
“Na gamsu da gaskiya da ƙwarewar mambobin kwamitin. An zaɓe su bisa cancanta, kuma ina da yaƙinin sun yi aikinsu ba tare da son rai ba,” in ji Gwamna Abba.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta tsoma baki a binciken da ya ɗauki watanni shida ana yi ba, domin bai wa kwamitin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
“Gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace dangane da abubuwan da aka gano a cikin rahoton.
“Wannan zai zama izina ga masu tayar da tarzoma da haddasa ɓarna a jihar,” a cewarsa.
Da yake gabatar da rahoton, Mai shari’a Wada, ya bayyana cewa kwamitin ya ziyarci wuraren da abin ya shafa tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tattara bayanai kan tasirin zanga-zangar.
“Alƙawarin da gwamnan ya ɗauka na aiwatar da shawarwarin rahoton yana nuna matakin da za a ɗauka don tabbatar da adalci da daidaito a Jihar Kano,” in ji sanarwar.
Gwamna Abba ya yaba wa kwamitin bisa aikin da suka yi, kuma ya buƙace su da su kasance a shirye idan gwamnati ta sake neman su za su yi wani aiki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwamiti Lalata Dukiya rasuwa Rauni Zanga zangar Yunwa zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan zargi ya ta’allaƙa ne da bayanai marasa tushe, waɗanda ba su san yanayin tsaron Najeriya ba.
“Wasu daga cikin iƙirarin da jami’an Amurka suka yi sun dogara ne da bayanai marasa inganci da tunanin cewa yawancin waɗanda ake kai wa hare-hare Kiristoci ne,” in ji Idris.
“Waɗannan miyagu (’yan ta’adda) ba su ware addini ɗaya ba, suna kai wa Kiristoci da Musulmai hari musamman a Arewacin ƙasar nan.”
Ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai yawan addinai da ke zaune lafiya tare, kuma irin waɗannan rahotanni na ƙarya na iya haddasa rikici da tayar da fitina.
“Keɓe waɗannan hare-hare da sunan wani addini abu ne mai hatsarin gaske. Najeriya ƙasa ce wadda mutane suka yadda da juna inda mutane masu addinai daban-daban ke rayuwa cikin lumana,” in ji ministan.
Idris, ya ce gwamnati na ci gaba da inganta fannin tsaro, ciki har da samar da sabbin kayan aiki da haɗin kai mai ƙarfi tsakanin hukumomin tsaro.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2009, Najeriya ke yaƙi da ta’addanci da ’yan fashin daji, kuma sauye-sauyen da aka yi kwanan nan sauke Hafsoshin Tsaro na nufin inganta tsaro.
Ministan, ya ƙara da cewa gwamnati tana amfani da hanyoyin zaman lafiya ta hanyar noman abinci, samar da ayyukan yi, da shirye-shiryen tallafa wa jama’a don rage talauci da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.