Aminiya:
2025-07-30@23:19:03 GMT

Mutum 10 sun rasu, an lalata dukiyar N11bn yayin zanga-zangar yunwa a Kano — Rahoto

Published: 19th, February 2025 GMT

Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka.

Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar.

Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram

Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya).

Ya tabbatar da cewa za a fitar da takarda a hukumanci don bayyana waɗanda suka ɗauki nauyin tashin hankali yayin zanga-zangar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bsture Dawaki Tofa ya fitar, zanga-zangar ta yi sanadin rasuwar rayukan mutum 10, yayin da wasu bakwai duka samu munanan raunuka.

Hakazalika ya ce an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11.

“Na gamsu da gaskiya da ƙwarewar mambobin kwamitin. An zaɓe su bisa cancanta, kuma ina da yaƙinin sun yi aikinsu ba tare da son rai ba,” in ji Gwamna Abba.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta tsoma baki a binciken da ya ɗauki watanni shida ana yi ba, domin bai wa kwamitin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

“Gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace dangane da abubuwan da aka gano a cikin rahoton.

“Wannan zai zama izina ga masu tayar da tarzoma da haddasa ɓarna a jihar,” a cewarsa.

Da yake gabatar da rahoton, Mai shari’a Wada, ya bayyana cewa kwamitin ya ziyarci wuraren da abin ya shafa tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tattara bayanai kan tasirin zanga-zangar.

“Alƙawarin da gwamnan ya ɗauka na aiwatar da shawarwarin rahoton yana nuna matakin da za a ɗauka don tabbatar da adalci da daidaito a Jihar Kano,” in ji sanarwar.

Gwamna Abba ya yaba wa kwamitin bisa aikin da suka yi, kuma ya buƙace su da su kasance a shirye idan gwamnati ta sake neman su za su yi wani aiki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwamiti Lalata Dukiya rasuwa Rauni Zanga zangar Yunwa zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana
  • Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
  • Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa
  • Mutum miliyan 1.2 na fama da ciwon hanta a Kano
  • Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya