Kasar Iran Ta Yi Maraba Da Gyara Batun Cewa; An Dakatar Da Jigilar Jiragenta Zuwa Kasar Lebanon
Published: 14th, February 2025 GMT
Jakadan Iran a Lebanon ya bayyana cewa: Suna maraba da matakin jigilar jiragen saman Lebanon zuwa Iran da sharadin rashin soke jigilar jiragen Iran zuwa Lebanon
Jakadan kasar Iran a kasar Lebanon Mujtaba Amani ya bayyana cewa: Bangaren Iran yana maraba da samar da jigilar jiragen saman kamfanonin jiragen saman kasar Lebanon zuwa kasar Iran, ba tare da batun soke jigilar jiragen saman Iran zuwa kasar Lebanon ba.
Gidan talabijin din kasar Iran a yau Juma’a ya sanar da cewa: An yi watsi da furucin wasu kamfanonin jiragen sama guda biyu da suka ce, gwamnatin Lebanon ta hana tafiyar jiragen saman Iran guda biyu zuwa kasar Lebanon da suke tashi a ranakun Alhamis da Juma’a, don haka ofishin jakadancin Iran a Lebanon ya bi sawun abin da ke faruwa, inda aka gyara matsalar ta hanyar tabbatar da izinin ci gaba da jigilar jiragen, tare da sanar da matafiya daga Iran zuwa Lebanon gudanar da tafiye-tafiyensu daga Iran zuwa Lebanon.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a kasar Lebanon jigilar jiragen jiragen saman
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza.
A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na tsoma baki a shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da dukkan kasashen duniya tana yin kakkausar suka kan kisan gillar da ake yi a Gaza tare da goyon bayan duk wani tsari da zai kai ga dakatar da aikata laifuka da kuma rage radadin wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki.
Baqa’i ya jaddada cewa; Masu yin shawarwarin Hamas sun fahimci bukatar neman cimma muradun al’ummar Gaza da ake zalunta ta hanyar da ta dace, kuma ba sa bukatar shiga tsakani na bangarori na uku dangane da hakan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya yi la’akari da katsalandan din Iran a cikin shawarwarin da suka dace da cewa ba shi da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa irin wadannan zarge-zarge wani nau’i ne na neman tauyaye hakki da gujewa hakkin da ya rataya a wuyar mutum da kokarin Amurka na gujewa duk wani mugun aiki da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aikita kan al’ummar Falasdinu, da suka hada da kisan fararen hula 60,000 da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara da kuma killace Zirin Gaza tsawon watanni. Da hana shigar agajin jin kai da kuma kashe fararen hula da ke fama da yunwa da kishirwa a tarkon kisa a wuraren da ake kira cibiyoyin rarraba kayan agaji da wata cibiyar Amurka ta kafa.