Aminiya:
2025-09-17@21:51:07 GMT

Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano

Published: 26th, February 2025 GMT

Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta.

Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi.

Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino

Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu.

“Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu.

“Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai dai su riƙa yawo kamar awaki. Don haka, muka yi bincike muka zaƙulo irin waɗannan yara don mu taimaka musu,” in ji shi.

Taron rabon kayayyakin ya samu halartar mai unguwar Kofar Mata, Alhaji Muhammad Jibril, wanda ya yi kira da a riƙa taimakon marayu da mabuƙata domin hana lalacewar tarbiyyar yara a yankin.

Ya ce rashin irin wannan taimako ne ke janyo koma-baya a yankin Arewa, inda ya bayar da misali da Kudancin Najeriya inda ake ɗaukar nauyin marayu har su girma su zama mutane nagari a rayuwa.

“Idan har ba a taimaka wa marayu da mabuƙata ba, za su tashi babu tarbiyya.

“Idan yaro ba shi da gata, babu wanda zai gyara masa hanya. Amma idan ana tallafa masa, zai girma da sanin darajar rayuwa,” in ji shi.

Ya buƙaci iyaye da al’umma su ci gaba da kula da tarbiyyar yara tare da basu kulawa da taimako domin su zama mutane nagari da za su amfanar da al’umma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kayayyakin Makaranta Kofar Mata Ƙungiya Marayu

এছাড়াও পড়ুন:

KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta
  • KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
  • Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata