2025-09-17@22:17:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6135

«dala biliyan 40»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta rasu bayan masu zanga-zanga sun cinna wa gidansu da ke unguwar Dallu, Kathmandu wuta. Majiyoyi sun ce masu zanga-zangar sun rufe ta a cikin gidan kafin daga baya suka cinna wa gidan wuta. An harbe ’yan sanda 3 har lahira a Kogi Babban layin wutar lantarki ya sake lalacewa An kai ta Asibitin Kirtipur Burn Hospital amma ta rasu, saboda raunukan da ta samu. Wannan lamari ya faru ne biyo bayan wata zanga-zanga da matasa suka fara a Nepal. Masu zanga-zangar suna neman a sallami jami’an gwamnati saboda zargin cin hanci, nuna son kai, da matsalolin da suka shafi tattalin arziƙi. Aƙalla mutum 22 ne suka rasu tun daga ranar...
    Duk kasar da take son kawo wa al’ummarta ci gaba ta wayewar zamanin da muke ciki wajibi ne ta mayar da hankali a kan gwada basirar ilimin kirkiro da sabbin fasahohi na ci gaba wadda hatta sauran al’ummomi za su amfana, amma ba tayar da husuma da neman zubar da jini ko mai karfi ya danne mara karfi ba. Gudanar da gasa mai tsafta a ko wane fage na ci gaba halas ne, saboda hakan na samar da karin kuzarin ci gaba, amma ba komawa ga zamanin kauyanci na rayuwa tamkar ta namun daji ba! (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
    Bisa amincewar majalisar gudanarwar kasar Sin, gwamnatin kasar za ta kafa yankin kare muhallin halittu na Huangyan Dao. Tuni dai aka fitar da sanarwar amincewa da hakan a shafin yanar gizo na gwamnatin tsakiyar kasar Sin, wato www.gov.cn a Larabar nan, bayan da ma’aikatar kare albarkatun kasa ta gabatar da bukatar hakan. Sanarwar amincewa da wannan bukata, ta ce kafa wannan yanki na Huangyan Dao, muhimmin tabbaci ne ga wanzuwar matakan kare muhallin halittu mabanbanta, bisa daidaito da dorewa. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
    Wasu mahara sun harbe jami’an ’yan sanda uku har lahira da safiyar ranar Laraba a wata madakatar mota da ke garin Egbe, a Ƙaramar Hukumar Yagba Yamma a Jihar Kogi. Kakakin rundunar jihar, SP William Aya, ne ya tabbatar da harin. Babban layin wutar lantarki ya sake faɗuwa Injin niƙa ya yi ajalin matar aure mai ’ya’ya 6 a Gombe Ya ce harin ya faru ne a kan iyakar Jihar Kogi da Jihar Kwara. SP Aya, ya ƙara da cewa, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Miller Dantawaye, ya tura tawaga ta musamman domin bincika yankin domin kama waɗanda suka kai harin. “Ina tabbatar muku cewa ’yan sandanmu uku sun mutu a Egbe yau. Kwamishina ya tura tawaga ta musamman, kuma muna...
    Dukkanin kamfanonin sun roƙi abokan hulɗarsu da su yi haƙuri, inda suka ce injiniyoyi na aiki don gyara wutar. Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ƙoƙarin gyara wutar lantarkin yanzu haka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
    138- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin gama gari a Siffin tsakanin rundunar Amirulmumina Aliyu...
    Wata kotu da ke ƙasar Ghana ta yanke wa ’yan Najeriya uku hukuncin ɗaurin shekaru 96, bayan samun su da laifin satar mota a birnin Kumasi na ƙasar. Kotun dai ta samu Francis Friday da Linus Agwazie da kuma Russell Ekenze ne da laifin a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke neman a kori ’yan Najeriya daga kasar saboda aikata laifuka. Injin niƙa ya yi ajalin matar aure mai ’ya’ya 6 a Gombe Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Mai magana da yawun ’yan sandan yankin Ashanti na ƙasar, Godwin Ahianyo, ne ya bayyana yanke hukuncin a cikin wata sanarwa ranar Talata. Sanarwar ta ce an kama mutanen ne ranar 20 ga watan Yuni bayan an zarge...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya isa kasar tunisiya domin tattaunawa da hukumomin kasar, a ci gaba da ziyarar da yake yi a yammacin Afrika, bayan da ya bar kasar masar inda ya gana da directan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  kuma suka cimma matsaya tsakaninsu, An tsara cewa babban jami’in diplomasiyar na iran zai gana da  ministan harkokin wajen kasar inda za su tattauna game da dangantar dake tsakanin kasashensu, da ma na kasa da kasa, A wani sako da ya aike da shi a shafin sa na X Araqchi ya nuna jin dadinsa sosai da kuma jinjinawa ga gwamnatin kasar masar game da rawar da ta taka a bangaren diplomasiya...
    Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya bayyana cewa ba za a fara aiwatar da shirin cire harajin man fetur na kashi 5 cikin 100 ba nan take. Ministan ya fadi  hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja. Ministan ya kuma ce ba za a fara aiwatar da harajin man fetur a watan Janairun 2026 ba lokacin da za a fara aiwatar da wasu harajin da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a bana. Har yau, babu wani shiri na gaggawa na aiwatar da shirin fara cire harajin kashi 5 na man fetur  da ‘yan kasa suke sha,” in ji Ministan a martanin da ya mayar dangane da cece-ku-ce...
    Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga kunnen doki da takwararta ta Afirika Ta Kudu da ci 1-1 a filin wasa na Toyota dake birnin Bloemfontein dake kasar Afirika Ta Kudu. Kyaftin din Nijeriya Troost Ekong  shi ne ya ci gida a minti na 25 da fara wasan kafin nan dan wasan bayan Nijeriya Calvin Bassey ya farke kwallon dab da za a tafi zuwa hutun rabin lokaci. Wannan sakamakon ya sa Super Eagles din  rasa tikitin kai tsaye da zai kaisu gasar Kofin Duniya, amma kuma suna da wata damar, idan sukayi kokarin karewa a mataki na biyu a rukunin C. Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da...
    Injin nika shinkafa ya yi ajalin wata mata mai shekaru 32, Hauwau Abubakar a kauyen Tumu da ke karamar hukumar Akkon jihar Gombe. Lamarin ya faru a lokacin da marigayiyar mai ’ya’ya shida ta je sayen shinkafa wajen wani mai injin mai suna Muhammad Danjuma mai shekaru 29. Bayanan Rundunar ’Yan Sandan Jihar sun nuna cewa hijabin jikinta ne ya kama bel ɗin injin, sannan ya ja ta jikinsa ya ji mata rauni a wuya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta nan take. Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Daga nan ne aka garzaya da ita zuwa asibitin garin na Tumu, inda likita ya...
    Kakakin Maikatar harkokin wajen kasar iran ismail baqa’I ya sanar cewa an fahimci juna tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya duniya game da shirin ta na nukiliya na zaman lafiya,  wanda hakan ke nuna cewa a kowanne lokacin iran tana shirinta ne domin ayyukan zaman lafiya tare da tuntubar IAEA sabanin parpagandar da  kafafen yada labaran yammacin turai suke yadewa na bayyana shirin na iran a matsayin barazana Iran da IAEA sun cimma yarjejeniyar yadda za su yi muala bisa sabon yanayin da ake ciki, bayan hamartaccen harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyar kasar, kuma an kulla yarjejeniyar ne tsakanin directan na IAEA Rafeel Grosi da kuma ministan harkokin wajen iran abbas araqchi  a...
    A jiya ne HKI ta kai hari a kasar Qatar daya daga cikin kawayen Amurka da ta girke sansanin sojin Amurka mai girma a yammacin Asiya, wanda ke kara tabbatar da cewa lallai alkawarin Amurka na bada tsaro ga kasashen kawayenta bashi da wata kima Harin na isra’ila a Qatar ya afku ne duk da babban sansani Amurka na Al’udeid dake kasar wanda haka ke nuna cewa lallai dukkan kawayen Amurka basu da sauran wata kariya da za su samu  daga duk wata barazana da za su fuskanta daga waje , wannan ya sa kasashen tekun fasha sake tunani game da kariyar da tsaro da Washington za ta basu. Wata babbar jami’a a kungiyar tarayyar turai cinzia bianco ta bayyana...
    “Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim.   Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda amfani da injin sare bishiya ba tare da izini ba, da kuma tarar ₦250,000 kan kowace bishiya da aka sare ba bisa ka’ida ba.   “Haka kuma za a umurci waɗanda suka aikata laifin da su sake dasa bishiyar sannan kuma za a ƙwace injin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza A matsayin martani ga kuri’ar raba gardama kan halaccin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza da ake zalunta, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya ba da izini na addini na fitar da wani kaso na kudaden Khumusi don haka. A cikin cikakken labarin, a baya-bayan nan ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba da izini na addini na ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Falastinu da ake zalunta a Gaza. Ga rubutun tambaya da amsar, kamar yadda gidan yanar gizon KHAMENEI.IR ya...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Hanya daya tilo ta kalubalantar ‘yan sahayoniyya ita ce ta hanyar hadin kai tsakanin kasashen musulmi Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, yayin da yake tsokaci kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar, ya bayyana cewa, hanya daya tilo da za a bi wajen kalubalantar mummunar dabi’ar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ita ce ta hanyar hada kai da hadin gwiwa tsakanin kasashen musulmi. Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a shafin sada zumunta na X a yammacin ranar Talata cewa: “Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata wani mugun aiki kan Iran da ba za a iya tunani ba, a halin yanzu kuma ta kai hari ga al’ummar Qatar...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan kasar Qatar laifi ne da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kakkausar murya ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan kasar Qatar, tana mai jaddada cewa, harin da aka kai kan tawagar kungiyar Hamas da ke tattaunawa da kuma janyo shahadan Falasdinawa da ‘yan Qatar, babban laifi ne da kuma keta dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta jaddada cikakken goyon bayanta ga Doha wajen tunkarar wannan ta’addanci. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta fitar cewa, wannan harin ta’addanci na nuni da cewa, cin zarafi...
    Martanin farko da gwamnatin Siriya ta fitar game da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a Homs, Latakia da Palmyra Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta yi kakkausar suka tare da Allah wadai kan hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu wurare a yankunan Homs, Latakia da Palmyra, lamarin da ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Siriya da kuma ‘yan kasashen ketare ta tabbatar da cewa: Wadannan hare-haren suna nuni ne a fili karara na keta hurumin Jamhuriyar Larabawa ta Siriya, barazana kai tsaye ga tsaronta da zaman lafiyar yankin, kuma wani bangare ne na ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila ke ci...
    Wani mamakon ruwan sama da aka tafka a birnin Zariyan jihar Kaduna, ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku yayin da kuma ake ci gaba da neman gawar mutum daya. Bayanai sun nuna cewa biyu daga cikin wadanda suka rasa ransu dalibai ne, Fatima Sani Danmarke mai shekara 18, da ke karatu a makarantar share fagen shiga jami’a da ke Funtua a jihar Katsina da Yusuf Surajo da shi kuma yake karatu a Zariya, sai kuma yarinyar da Fatima ke goye da ita. DSS ta warware tankiyar da ke tsakanin NUPENG da Dangote ’Yan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 11 a Zamfara Wani da lamarin ya faru a gabansa, Mallam Mustapha Badamasi Danbakano, ya ce, “Bayan ruwa ya ɗan...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, rashin imanin da Amurka ke da shi ne ya sa yin shawarwari da wannan kasa ba shi da amfani. Wannan labarin daga Pars Today ya yi nazari kan matsayin Imam Khamenei dangane da mugun imanin Amurka da manufofinsa. Menene ra’ayin Imam Khamenei kan mugun imanin Amurka da manufofinsa? Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a wata ganawa da yayi da dakarun Basij na Iran ya yi ishara da cewa Amurka ba ta cika alkawuran da ta dauka yana mai cewa: “A cikin JCPOA, sun ce, ‘Idan kun rage ayyukan masana’antar nukiliya ku, za mu yi waɗannan abubuwa: ɗage takunkumi, ɗaukar wasu ayyuka, yin wannan da wancan.’ Shin sun yi...
    “Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun rubuta a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me yasa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: Mun tashi don ci gaba da bege. Rasa bege na nufin watsi da mutanen Gaza da kuma mika su ga gwamnatin zalunci. “Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun lura a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me ya sa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: A cikin watanni 23 da suka gabata, mun shaida yadda gwamnatin wariyar launin fata ta...
    Sabanin yadda wasu kasashe ke tayar da takaddamar cinikayya da kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da tsarin samar da kayayyaki a duniya, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen ganin duniya ta samu ci gaba, musammam kasashe masu tasowa, ta hanyar bude kofa da yin komai cikin adalci.   A duk inda aka ambaci “Babba”, to a ko da yaushe, shi ne mai nuna sanin ya kamata da tallafawa da jagorantar na kasa, domin su zamo masu dogaro da kan su da bin daidaitacciyar hanya. Wannan kuma ya yi daidai da dabaru da manufofin kasar Sin, inda take mayar da hankali kan yadda za a gudu tare a tsira tare tsakaninta da kasashe masu tasowa.   A sakonsa...
    An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya.   Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun jari a duniya, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen sauya labarin Zamfara daga ƙalubale zuwa wani babban matsayi mai cike da damarmaki.   “Gwamnatina ta himmatu wajen samar da ingantaccen yanayi da ɗorewar yanayin zuba jari. Ina nan a yau a matsayin abokin tarayya, a shirye nake na ba ku cikakken haɗin kai don buɗe hanyoyin jin daɗin gare mu duka....
    Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da wasu da ba a san ko su wane ba suka yi garkuwa da shi. Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Talatar nan a Ibadan, babban birnin jihar. DSS ta warware tankiyar da ke tsakanin NUPENG da Dangote ’Yan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 11 a Zamfara Ya ce an ceto ɗan Masar ɗin ne a ranar Talata da safe — kwana ɗaya kacal bayan sace shi — ba tare da an biya kuɗin fansa ba. Osifeso ya ce an sace mutumin ne a yankin Alomaja, kusa da garin Idi-Ayunre, wani yanki...
      Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da Canada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ana sa ran darajar kayayyakin da masana’antun kasar Sin ke sarrafawa za ta karu da fiye da yuan tiriliyan 8, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.13 a karkashin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 na shekarar 2021 zuwa 2025, inda hakan zai ba da gudummawar fiye da kashi 30 bisa dari na ci gaban masana’antun duniya, kamar yadda wani jami’i ya bayyana a yau Talata. Ministan masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani Li Lecheng wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya kuma ce, kasar Sin ta ci gaba da rike matsayinta na zama babbar cibiyar masana’antu a duniya tsawon shekaru 15 a jere. A cikin shekaru 5 da suka gabata, kasar Sin ta ci gaba da bunkasa...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin sun shigo cikin al’umma sanye da hijabai sun yi garkuwa da mutane 11 ciki har da masallata guda uku a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadin da ta gabata a garin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru, kamar yadda rahotanni daga shafin Zagazola Makama suka tabbatar. An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi Makama wanda kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya ne ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne sanye da hijabai da rigunan mata da suka yi basaja da su, inda suka yi awon gaba da...
    Rundunar ’yan sanda ta Jihar Gombe ta samu nasarori a yaƙi da masu aikata laifuka, inda ta kama wata mata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar. An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi ’Yan bindiga da masu ɗaukar musu bayanai ba su da bambanci — Gwamnan Sakkwato Ya ce jami’an sashen kwantar da tarzoma na Anti-Violence Squad sun kama matar mai suna Rakiya Ahmed mai shekaru 53 a unguwar Barunde, inda aka same ta da ƙunshi takwas na ganyen wiwi. A cewarsa, an cafke matar ce bayan samun sahihan bayanan sirri daga jama’a, kuma...
    Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin Qatar a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar Hamasa a yau Talata. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotterre ya yi tir da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai birnin Doha na kasar Qatar ya kuma bayyana cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Haka ma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad Gaith ya yi tir da hare-haren da HKI ta kai gine-gine a Doka. Sannan kasashen Iran Saudia da Hadaddiyar daular Larabawa duk sun yi allawadai da hare-here. Gwamnatin kasar Turkiyya ta yi allawadai da...
    Yayin da ake gab da yin bikin ranar malamai ta kasar Sin karo na 41 nan ba da jimawa ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da martanin wasika ga wakilan malamai na musamman a duk fadin kasar, inda ya bayyana fatansa tare da mika gaisuwar ranar ga malamai da ma’aikata a bangaren ilmi a fadin kasar. A cikin wasikar, Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru 20 da fara aiwatar da shirin “malamai na musamman”, da yawa daga cikin malamai na musamman sun dukufa wajen ba da ilmi a yankunan karkara, tare da nuna kishi da jajircewa. Ya kuma bayyana fatan cewa za su ci gaba da tabbatar da aniyarsu kan koyarwa tare da bayar da sabbin gudumawa...
    A ƙoƙarinta na daƙile matsalar cin zarafin yara, rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta samu nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe a makon jiya.  Wakilinmu ya ruwaito cewa, wata yarinya ’yar kimanin shekaru 10 da ke Unguwar Bedi a ƙaramar hukumar Zuru, ta faɗa mummunan tarkon ne a lokacin da mahaifiyarta ta aike ta karɓo saƙo. ’Yan bindiga da masu ɗaukar musu bayanai ba su da bambanci — Gwamnan Sakkwato TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki kan ƙara harajin man fetur Bayanai sun ce wani mai suna Amos Jondo Maliki, wanda ke maƙwabtaka da su, ya kai ta ɗakinsa inda ya samu damar saduwa da ita. Haka zalika, wata...
    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Wurno da Rabah a ranar Litinin da ta gabata, domin jajanta wa al’umma bisa hare-haren da ’yan bindiga ke kai musu. TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki kan ƙara harajin man fetur Dalilin da muka yi watsi da buƙatar dawowar Sanata Natasha — Majalisar Dattawa Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen daƙile matsalar ’yan bindiga a faɗin jihar, inda ya buƙaci mazauna ƙauyuka su riƙa tona asirin duk wanda suka sani yana...
    Kana wasu alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a cikin watanni 7 na farkon wannan shekara, darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashe mafi karancin ci gaba a nahiyar Afirka, wadanda Sin ta riga ta yafe musu dukkan haraji, ta kai dalar Amurka biliyan 39.66, adadin da ya karu da kaso 10.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin a bara. Ta hanyar karfafa hadin gwiwar cinikayya da abokan hulda kamar Sin, da inganta cinikayya a cikin nahiya, ana sa ran ganin Afirka za ta samu nasarar rage tasirin manufar harajin Amurka. A halin yanzu, kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin da kasashen Afirka, suna kokarin daukaka ra’ayin cudanyar sassa...
    Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki dangane da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ɗauka na ƙara harajin kaso 5 cikin 100 a farashin duk litar man fetur. A yayin da ƙungiyar ta yi watsi da matakin, ta kuma kwatanta aiwatar da hakan a matsayin ganganci da mugunta ga tattalin arzikin ƙasar. Dalilin da muka yi watsi da buƙatar dawowar Sanata Natasha — Majalisar Dattawa NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya A bayan nan ne dai Gwamnatin Tarayyar ta sanar da ɗaukar wannan mataki da zai fara aiki a farkon watan Janairun 2026, domin samun kuɗaɗen shiga da za a yi amfani da su wajen gina...
    Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, tare da tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan kowa ba tare da nuna bambanci ba. A cewarsa, hare-haren da ake kai wa jam’iyyun adawa barazana ce ga makomar dimokuraɗiyya a Nijeriya, don haka dole a yi magana a kai kafin abin ya zama al’ada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kafar yada labaran Syria ta ce Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a wasu sassa na tsakiya da kuma yammacin kasar. Rahotanni sun ce an kai hare haren ne a kusa da Homs da Palmyra da kuma birnin Latakia da ke gabar ruwa. Ana ganin Isra’ilan ta kai hare-haren kan sansanonin Soji ne. Ba a bayar da rahoto akan mutanen da hare haren ya shafa ba, haka ita ma Isra’ilan ba ta ce komai a kan harin ba.  Isra’ila dai na kai hare-hare ta sama tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Bashar al- Assad a watan Disambar bara. ana ta bangaren gamnatin kasar siriya ta tir da kai harin tare da bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da...
    Idan Afirka Ta Kudu ta yi nasara yau, za ta tabbatar da zuwa gasar Kofin Duniya da za a buga a Arewacin Amurka a 2026, kuma karo na farko tun bayan 2010 lokacin da ta ɗauki nauyin gasar. Nijeriya kuwa, wadda ta halarci gasar sau shida a baya, tana ƙoƙarin dawo da martabarta. Nasarar da ta samu a kan Rwanda a wasan da ya gabata ta farfaɗo da ƙwarin guiwar masoyanta, duk da cewa a wasanni bakwai da ta buga na neman gurbin shiga 2026, sau biyu kacal ta ci. Wasan na yau shi ne karo na 17 da ƙasashen biyu za su haɗu. Nijeriya ta fi samun nasara sau takwas, inda aka tashi canjaras sau bakwai, sai Afirka Ta...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi alla-wadai da wani harin da ’yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, da ke karamar hukumar Bama a Jihar Borno. Mohamed Malick Fall, Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan jinkai na Majalisar a Nijeriya, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin, wanda ya faru a yammacin ranar Jumma’a, 5 ga watan Satumba. “Ina matukar bakin ciki da rahoton kisan da aka yi wa sojoji da fararen hula da dama a ranar Juma’a a kauyen Dara Jamal,” in ji Fall. Rahotannin farko sun nuna cewa an kashe fararen hula fiye da 50, inda ake zargin an yi garkuwa da wadanda ba a san adadinsu ba. Kazalika, bayanai sun nuna mutane da dama sun gudu daga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya sun shiga taraddadin abin da ka iya biyo bayana kudurin Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NPENG) na tsunduma yajin aiki.   Hakan dai ya biyo bayan tashi da aka yi daga zaman da Gwamnatin Tarayya ta kira don sasanta kungiyar, mai samun goyon bayan sauran kungiyoyin kwadago, da rukunin kamfanonin Dangote, ba tare da cimma wata matsaya ba. NAJERIYA A YAU: Yadda Ilimi Ke Ƙara Tsada Yayin Komawar Yara Makaranta DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Ministan Kwadago Muhammadu Dingyadi ne dai ya kira taron, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin NUPENG da NLC da TUC da na Dangote...
    El-Rufa’i ya jaddada cewa manufarsa ita ce ganin an tabbatar da gaskiya da bin doka a ƴansandan Nijeriya, domin tabbatar da jami’an suna aiki da gaskiya da biyayya ga ƙa’ida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar dokokin Faransa ta kada kuri’ar yankan kauna wadda ta kawo karshen gwamnatin Firaministan kasar Francois Bayrou. Yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri’ar yanke masa kauna da kashi biyu cikin uku a jiya Litini. Bayrou dai ya shafe watanni 9 kacal akan wannan kujera a matsayin Firaminista na shida karƙashin shugabancin Emmanuel Macron da ya kama aiki a shekarar 2017, wanda a halin yanzu jam’iyyarsa ke fuskantar gagarumin rikicin siyasa. Tuni ofishin Macron ya sanar da shirinsa na nada sabon Firaminista da zai maye gurbin Bayrou nan da kwanaki masu zuwa, yayin da Bayrou ke shirin mika takardar ajiye aiki ga shugaban kasar yau Talata. Tuni dai jam’iyyar RN ta masu tsattauran ra’ayi da kuma masu sassaucin ra’ayi a...
    An bude taron sauyin yanayi na Afirka karo na biyu a birnin Addis Ababa, na kasar Habasha mai manufar samar da hanyoyin magance matsalolin yanayi a nahiyar. Wannan taro na tsawon kwana biyu, wanda Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da gwamnatin Habasha suka shirya, na samun halartar wakilai 25,000 da kuma shugabannin kasashe 45. Haka kuma, taron na neman karfafa murya guda daya ta Afirka a fagen duniya kan rage illolin sauyin yanayi, tare da bunkasa tsare-tsaren da ke da amfani ga kasashen Afirka kafin taron COP da za a gudanar a Brazil a watan Nuwamba mai zuwa. Bayar da kudi da tabbatar da adalci na yanayi a na daga cikin ajandar babban taron. Bankin raya kasashen Afirka ya...
    Hukumomi sun shawarci jama’a su tabbatar da cewa gidajensu suna da tsaro da karko, tare da kaucewa gina gidaje a kan magudanan ruwa a wannan lokacin na damina. Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa Kirikasamma na daga cikin wuraren da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministar shari’a ta kasar Sin He Rong, ta ce kasar Sin ta zama wurin da aka fi zaba na warware takkadamar cinikayya da ta shafi kasa da kasa, tana mai bada misali da karuwar adadin irin wadannan batutuwa cikin shekaru 5 da suka gabata. Yayin wani taron manema labarai a yau, He Rong ta ce an warware sama da takkadama 16,000 dake da alaka da kasashen waje, da suka shafi jimilar kudi yuan biliyan 730 (kimanin dala biliyan 102.8) a kasar, a lokacin. Ta kara da cewa, a shekarar 2024 kadai, kasar ta karbi irin wadannan batutuwa sama da 4,400, wadanda suka shafi kusan yuan biliyan 200. Idan aka kwatanta da shekarar 2020, adadin batutuwan ya karu da kaso 100,...
    Ya ce: “A Zamfara an kashe ‘yan ta’adda 30 a hare-haren sama da kasa, yayin da masu tada kayar baya 76 da suka hada da mata da kananan yara suka mika wuya ga jami’an tsaro.   “Rundunar ‘yansanda ta bayar da rahoton kama mutane 1,950 da ke da alaka da munanan laifuka, garkuwa da mutane, da kuma fashi. An kubutar da jimillar mutane 141 da aka yi garkuwa da su.   Ya ce hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama sama da kilo 66,000 na miyagun ƙwayoyi.   A ɓangaren Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC), ya ce hukumar ta yi nasarar gurfanar da ƙorafe-ƙorafe 588 ga kotu a cikin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu mazauna unguwar Oworonshoki da ke ƙaramar hukumar Kosofe a Jihar Legas, sun datse wani sashe na gadar Third Mainland a ranar Litinin, a wata zanga-zanga da suka gudanar don nuna adawa da rushe musu gidaje. Datse hanyar da suka yi ya haddasa cunkoson masu ababen hawa da fasinjoji, lamarin da ya tilasta wa ’yan sanda tarar hanzarin lamarin, inda suka riƙa harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zangar-zangar. MDD ta buƙaci hukumomin Najeriya su kamo waɗanda suka kai hari a Bama Yarima Harry ya ziyarci kabarin Sarauniya Elizabeth II Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Yulin 2023 aka soma rusau ɗin, lamarin da ya raba wasu mazauna unguwanni kamar Oke-Eri, Odunfa Lane, Ogo-Oluwa, Precious Seed, Coker da kuma...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Kamfanin Aero Engine Corporation na kasar Sin, ya fitar da sabon injin aiki a manyan na’urori mai aiki da iskar gas mai karfin gaske, wanda ke iya samar da karfin megawatt 110. Kamfanin ya fayyace sashen kirar injin mai suna Taihang 110, a yankin kira na kamfanin a Litinin din nan, kuma ana fatan fara shigar da injin kasuwa. Fitar da injin zuwa kasuwanni na nufin kasar Sin ta cimma nasarar gabatar da inji kirar gida mai matukar karfi, wanda manyan na’urori za su rika amfani da shi ta hanyar sarrafa iskar gas. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah-wadai da harin da ’yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, da ke yankin Bama na Jihar Borno. Harin wanda ya faru a yammacin ranar Juma’a 5 ga watan Satumba ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 60 tare da sace wasu da dama ciki har da sojoji da fararen hula. A wata sanarwa da Mohamed Malick Fall, babban jami’i mai kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya fitar, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin. MDD ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gano waɗanda suka kai wannan harin tare da ɗaukar mataki a kansu. Fall ya ce: “Ina kira ga hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka...
    A yau Litinin, wasu rahotanni na cewa, yayin wani taron manema labaru na musamman kan zuba jari ga sassan ketare da aka gudanar a taron tattauna harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25, cewa a shekarar 2024 adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kai dalar Amurka biliyan 50.99, adadin da ya karu da kashi 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023. A dai yau din, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar kula da musayar kudin waje ta kasar, sun fitar da sanarwar “kididdiga ta shekarar 2024 kan...
      Ya bayyana karya ka’idojin da aka shimfiɗa kan amso basussukan a matsayin “babban abin damuwa da fargaba kan ɗorewar tattalin arzikin kasar,” yana mai jaddada cewa, akwai buƙatar samar da “sabbin tsaruka masu ƙarfi, da za su daidaita hanyoyin karɓar rance na gaskiya, da kuma ƙuduri na bai ɗaya don tabbatar da cewa, duk kuɗin da aka karɓo ya dace da buƙatar shirin inganta zamantakewar ‘yar Nijeriya”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yarima Harry wanda ya koma rayuwa a Jihar California ta Amurka, ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, a fadar Windsor da ke yammacin birnin Landan a ranar Litinin. Shekaru uku ke nan daidai da rasuwar Sarauniya Elizabeth II wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga Satumba, 2022, kuma aka binne ta a cikin cocin St. George’s Chapel da ke fadar Windsor. An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan Matatar Dangote ta musanta dakatar da aiki Mai magana da yawunsa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Harry ya kai ziyara shi kaɗai domin girmama mahaifiyarsa. A halin yanzu dai abin tambayar shi ne ko Yarima Harry zai gana da mahaifinsa, Sarki Charles III,...
    “Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.   Kwamishinan ya ƙara da cewa jagorancin Gwamnan na bai wa haɗin kan al’umma muhimmanci a matsayin ginshikin shugabanci na dimokuraɗiyya.   “Wannan ƙoƙarin wayar da kai yana nuna hangen nesa na Gwamna na gudanar da mulki mai maida hankali kan bukatun jama’a, inda kowace murya ke da muhimmanci, kuma kowane ɗan ƙasa yana da rawar da zai taka wajen gina makomar Jihar Kaduna.   “...
    An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan da ya yi murabus, inda tsohon Ministan Harkokin Waje ya bayyana takarar neman kujerar mai tasiri a kasar wadda take sahun gaba na kasashe masu arziki a duniya. Tsohon Ministan Harkokin Wajen kasar Japan, Toshimitsu Motegi ya zama mutum na farko da ya nemi ’yan majalisar dokoki na jam’iyya mai mulki ta Liberal Democratic Party (LDP) su ba shi damar zama sabon Firaminista, domin ya maye gurbi Firamnista Shigeru Ishiba mai barin gado wanda ya bayyana yin murabus daga kan mukamin. Sojoji sun kashe kasurgumin dan ta’adda da yaransa 5 a Kogi Yiwuwar yajin aikin direbobin tankar mai kan rikicin Matatar Dangote Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Lahadi ce Firaministan Japan,...
    Dakarun sojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda wanda aka fi sani da suna Kachalla Bala da yaransa biyar a Jihar Kogi. Sojojin Birget ta 12 da ke Lakwaja, hedikwatar jihar sun kuma yi nasarar ceto wasu mutanen da gungun ’yan bindigar suka yi garkuwa da su. Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi ya ce samamen da sojojin ke kaiwa a sassan jihar domin kakkabe ayyukan ’yan binidga yana samun nasara a yankunan Tunga da Aleke da Ungwan Soni da Ungwan Nyaba da kuma Ankomi. Yankin gadar Agbede–Adankoo (Mosalanci Boka) da ke yankunan Lokoja, Kabba-Bunu, da kuma Karamar Hukumar Yagba sun yi iyaka da jihohin Kwara da Neja,  wanda hakan ya sa suka zama mafaka ga ayyukan ’yan bindiga....
    Najeriya na iya shiga cikin matsalar ƙarancin man fetur daga yau Litinin, muddin Gwamnatin Tarayya ba ta warware rikicin da ya kunno kai tsakanin Ƙungiyar Direbobin Tankar Mai (PTD) ta ƙarƙashin NUPENG da kamfanin Matatar Mai ta Dangote ba. Direbobin sun sanar da shiga yajin aiki saboda shirin kamfanin Ɗangote na fitar da motoci 4,000 da ke amfani da gas ɗin CNG domin kai mai kai tsaye ga kasuwa ba tare da direbobin da ke ƙarƙashin NUPENG ba. Ƙungiyar ta yi zargin cewa wannan tsari zai rusa ayyukan dubban direbobi, ya hana ’yancin kafa ƙungiya kuma ya haifar da “mulkin danniya” a harkar rarraba man fetur. Gwamnati ta shiga tsakani Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Muhammad Maigari Ɗingyadi, ya tabbatar a...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jami’an kasar suna kiyaye shawarwarin Jagoran juyin juya halin Musulunci Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Jami’an zartaswa na kasar suna kiyaye shawarwari da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran. Shugaba Pezeshkian ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a shafin sada zumunta na X cewa: Jami’an zartaswa na kasar suna kiyaye shawarwari da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci yayin ganawarsa a jiya (Lahadi) da wakilan gwamnati. Ya kara da cewa: Da yardar Allah za a shawo kan matsaloli tare da hadin kan kasa da gwiwar al’umma da taimakon al’umma da kuma saukakawa Jagoran juyin juya halin Musulunci. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke ƙara tsada yayin komawan ’ya’yansu makaranta a sabuwar shekarar karatu. Makarantu na ƙara ɓullo da sabbin hanyoyin karɓar kuɗi daga hannun yara da sunan koyarwa. NAJERIYA A YAU: Yadda ake gudanar da bukukuwar Sallar Gani yayin Mauludi DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da ke sa ilimi ƙara tsada yayin da yara ke komawa makaranta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Saboda tsabar gudunsu da kuma zilliya inda suke da sauri ninki biyar na gudun sauti makamai ne da ka iya sauya yadda ake fafata yaki a yanzu. Hakan ta sa yanzu kasashe ke rige-rigen samar da su. Rasha, China, Amurka: rigegeniyar nuna iko Bikin faretin na Beijing ya jawo rade-radi game da barazanar da China ke yi wa kasashen Yamma da makamanta masu linzami. Yanzu ita ce kan gaba wajen samar da su, sai kuma Rasha da ke biye mata. Amurka kuma, na kokarin kamo su ne, yayin da Birtaniya kuma ba ta da su. William Freer, wani mai nazarin harkokin tsaro a cibiyar Council on Geostrategy, na ganin dalilin da ya sa Rasha da China suka zarce saura abu...
    Jimilar kudin asusun ajiya na kasar Sin a ketare ya kai dala triliyan 3.3222 zuwa karshen watan Agusta, inda ya karu da dala biliyan 29.9 ko kaso 0.91, idan aka kwatanta da na karshen watan Yuli. Hukumar kula da musayar kudi ta kasar Sin ta alakanta karuwar da tasirin sauyin kudi da sauyin farashin kadarori. Ta kara da cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da habaka yadda ya kamata, cike da juriya da kuzari, da samar da goyon bayan mai karfi ga asusun ajiyar kasar na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna. Hari  ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, inda suka yi ta harbe-harbe. Harin Borno: Dole ’yan Najeriya su haɗa kai su fuskanci Boko Haram — Atiku Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna  Har ila yau, sun yi garkuwa da wasu mazauna garin, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadinsu ba. Waɗanda suka rasu a harin sun haɗa da: Elisha Paul, Japhet Bitrus, Obadiah Joshua, Luka Augustine,...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da sabon harin da Boko Haram suka kai a Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama; ciki har da sojoji. Atiku, ya bayyana halin da ’yan Najeriya ke shiga sakamakon hare-haren ta’addanci. Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna  Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal A cikin saƙon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Atiku ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai wajen yaƙi da matsalar tsaro ta hanyar haɗin kan al’umma. Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, jama’ar Jihar Borno, da kuma Gwamna Babagana Umara Zulum. Ya kuma yaba wa gwamnan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Sin da Tarayyar Afrika (AU), sun yi alkawarin karfafa goyon bayan juna wajen gina tsarin jagorantar harkokin duniya bisa adalci tare da tabbatar da zaman lafiya a duniya. An yi alkawarin ne a ranar Juma’a yayin wani taron manyan jami’ai a Addis Ababa na Habasha, albarkacin cika shekaru 80 da Sinawa suka yi nasarar turje wa harin Japan da yakin duniya na II. Da yake jawabi ga taron, Jiang Feng, shugaban tawagar kasar Sin a AU, ya nanata bukatar tunawa da tarihi da karfafa hadin gwiwa a duniya domin shawo kan kalubalen tsaro da duniya ke fama da su. Da yake jawabi a madadin kwamishinar kula da harkokin lafiya da jin kai da ci gaban al’umma Amma Twum-Amoah, babban...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ta samu nasarar ceto wasu mata biyu da wata jaririya da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jihar Kaduna. Shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook. Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikata Ta ce ambaliyar ta auku ne sakamakon ruwan sama mai yawa da aka yi a ranar Juma’a. Ta ce sama da gidaje 160 da magidanta 500 ne ambaliyar ta shafa a unguwanni irin su Kabala Doki, Bachama, Kigo, Ramat, da Unguwar Dosa/Nasarawa/Mali. Rahoton ya nuna cewa ruwan kogin Kaduna ne ya yi sama, ya shiga unguwanni,...
    Ministan yakin HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sun yi kokarin kashe jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a yakin kwanaki 12 amma bayanan da suke da shi ya kasa kaiwa ga manufarsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko wanda HKI take tabbatar da cewa ta yi kokarin mai matsayi mafi girma a kasar Iran, wanda kuma ya kasa kaiwa na sarara. Kazt ya bayyana haka wa tasoshin talabijin ta Chennel 13, Kan da kuma Channel 12, kan cewa sun yo kokari har sau 2 amma bayayan da ke hannummu sun kasa tabbatar da abunda muke nema. Yace da mun sami da mun kasheshi tuni. Bayanan da gwamnatin...
    Zahra Kiana yar wasan Wushu ta lashe lambar Zinari a wasar Wushu ta shekara ta 2025 a kasar Barazil. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Kiyani ta lashe lambar Zinari ne a dai-dai lokacinda wannan wasan take sabo a kasar Iran, kuma tana cike da masu taka rawa a cikinta da dama daga gabacin kasashen Asia. Labarin ya kara da cewa Kiyani ta daukaka kasar Iran a gasar Wushu, sannan ta kwadaitar da sauran mata wadanda suke sha’awar yi wasar. A rana ta 4 da fara gasar Wushu ta kasa da kasa kuma karo na 17th ta shekara ta 2025 a kasar Brazil Kina ta lashe lambar Zinari, wanda ya bawa Iran matsayi a wannan wasan...
    Bictor Boniface Wani dan wasan da ya tafi zaman aro shi ne Bictor Boniface wanda ya bar Bayer Leberkusen ya koma Werder Bremen a matsayin aro na tsawon kaka guda a ranar da za a rufe cinikin yan wasa, dan wasan na Nijeriya ya saka hannu akan kwantiragin da zai sa ya zauna a Werder har zuwa watan Yuni na shekarar 2026, kungiyoyin biyu ne za su biya albashin Boniface.   Tolu Arokodare Wolbes ta sanar da daukar Arokodare daga kungiyar KRC Genk ta kasar Belgium dake buga gasar Belgian Pro League a ranar karshe ta musayar yan wasa, dan wasan mai shekaru 24 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu da kungiyar ta Firimiya tare da zabin karin shekara,...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Darajamal da ke Ƙaramar Hukumar Bama, domin jajanta wa iyalan mutanen da Boko Haram suka kashe. Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun hallaka aƙalla mutum 63, yayin da dakarun soja suka kashe 30 daga cikinsu. Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikata Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya Da yake magana da mazauna garin Zulum ya ce: “Abin takaici ne sosai. An dawo da wannan al’umma nan ba daɗewa, amma sai ga shi an sake fuskantar mummunan hari a daren jiya.” Gwamnan ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙarfafa jami’an tsaro a dazuka, inda ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙara...
    Domin kuwa wasu matan kwanciya kan iya zama sanadi na lalacewar cikin. So, akan ce ma a rage ko a bari a watanni uku na farkon ciki. Don haka idan ka ga wadannan matsalolin kar ka ce wai kirkira take, ko da gangan take. Ba gaskiya bane. Lalura ce babba, kuma da take bukatar kallo na musamman. Idan kaga wannan lokacin yazo, anan ne ake so ka nuna soyayyarka, da kulawarka, da taimakonka. Wajibi ka bata hadin-kai don ta wuce wannan watanni uku na farko din. Domin cikin jikinta a wannan lokacin kamar akan siratsi yake, duk abinda aka ce ana halittarta ’yan Adam a cikinsa ai yaga taka kansa. Komai zai iya faruwa. Namiji dan kirki shine sai kaga...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnati, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta sake duba mafi ƙarancin albashi, domin Naira Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ta isa wajen tafiyar da al’amuran yau da kullum. A cewarsu tashin farashin kayan abinci, sufuri, haya, da wutar lantarki ya ƙara jefa su cikin wahalar da rayuwa. Sojoji sun bankaɗo mafakar ’yan ta’adda da makamai a Taraba Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya A wasu jihohi kamar Imo, Legas da Ribas sun riga sun ƙara mafi ƙarancin albashi sama da wanda gwamnatin tarayya ke biya. Mista Benson Upah, Sakataren riƙo na NLC, ya ce: “Naira 70,000 ba za ta iya ɗaukar nauyin rayuwa a wannan yanayi na tattalin...
    Kazalika, an amince da amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar karo na 12, wanda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Katsina. Da yake karin haske ga manema labarai bayan taron, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ya ce, an sanar da matakin ne sakamakon mawuyacin halin da jihar ke ciki, wanda ya kawo babban kalubale ga ababen hawa na yau da kullum wajen shiga wasu yankunan, musamman na karkara da marasa galihu. “Gwamnati ta bayyana matsayinta a fili: tsaro shi ne fifiko na farko, na biyu da na uku na wannan gwamnati shi ne, mun kudiri aniyar magance rashin tsaro baki-daya.” in ji Dakta Danmusa. Baya ga...
    Sojojin runduna ta 6 da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, sun gano wata mafakar ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai da dama a ƙauyen Ikyaior da ke ƙaramar hukumar Wukari, a kan iyakar Taraba da Benuwai. Bayanan sirri da sojojin suka samu ne suka taimaka musu wajen kai farmakin da ya kai ga gano mafakar da kuma ƙwato makaman. Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya DSS ta bai wa shafin X wa’adin goge saƙon Sowore da ke ƙaryata Tinubu Mataimakin mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Umar Mohammed, ya tabbatar wa da wakilin Aminiya cewa sojojin sun gudanar da bincike a yankin, inda suka gano makamai masu tarin yawa. “Mun samu makamai daban-daban, ciki har da bindigogi...
    Wasu cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook sun tabbatar da cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ƙasar ke da Musulmai kimanin mutane miliyan 124. Ƙididdigar ta waɗannan cibiyoyi ta nuna Musulunci na ci gaba da zama addini na biyu mafi girma a duniya, wanda yawan mabiyansa suka kai kusan mutane biliyan 2.45 zuwa shekarar 2023. Firaministan Japan Shigeru Ishiba ya yi murabus DSS ta bai wa shafin X wa’adin goge saƙon Sowore da ke ƙaryata Tinubu Ƙasar Indonesia ce ke kan gaba da Musulmai miliyan 242, sai kuma Pakistan mai miliyan 235. Sai kuma ƙasar India da miliyan 213 sa’annan kuma Bangladesh da miliyan 150. Daga nan kuma sai Najeriya wacce...
    Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya (DSS) ta bai wa shafin sada zumunta na X wa’adin sa’o’i 24 da ya goge wani saƙo da mai fafatuka Omoyele Sowore ya wallafa yana ƙaryata Shugaba Bola Tinubu. Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da Hukumar DSS ɗin ta aike wa kamfanin X Corp mallakin fitaccen attajirin nan Elon Musk. Firaministan Japan Shigeru Ishiba ya yi murabus ’Yan ta’adda sun kashe mutum 63 a Borno A wasiƙar da DSS ta wallafa shafinta na X ranar Asabar, hukumar ta zargi Mista Sowore da yin amfani da saƙonsa na X wajen cin fuskar shugaban ƙasa Tinubu da yi masa rashin mutunci da ba’a. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar 25...
    Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya sanar da murabus dinsa a matsayin shugaban jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP), watanni kaɗan bayan jam’iyyarsa ta sha mummunan kaye a zaɓen watan Yuli. Ishiba ya sanar da matakin ne a ranar Lahadi, duk da cewa a baya ya yi ƙoƙarin kaucewa matsin lambar ‘yan jam’iyyarsa da ke neman ya sauka sakamakon rashin nasarar zaɓen, inda ya dage cewa yana son tabbatar da yarjejeniyar haraji da ƙasar ta ƙulla da Amurka ta fara aiki yadda ya kamata. ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo ’Yan ta’adda sun kashe mutum 63 a Borno “Tun da Japan ta sanya hannu kan wannan yarjejeniya, kuma shugaban Amurka ya rattaba hannu a matsayin doka, mun tsallake...
    Daruruwan kungiyoyin sa kai ne suka gudanar da zanga-zanga a kasar malesiya domin nuna adawa da ziyarar shugaban Amurka Donal Trump a karshen watan gube saboda nuna goyon bayan isra’ila kan kisan kare dangi da take yi a Gaza, ,  sun bukaci gwamnati da ta soke gayyatar wanda suka bayyana shi a matsayin babban mai laifin yaki dake da hannu wajen kisan kare dangi da isra’ila ke yi wa alummar Gaza, da hakan ya sabama dukkan dokokin kasa da kasa. Mazu zanga zangar sun daga kwalaye da a ciki aka rubuta cewa trump kada ka zo,kuma mafiywancin wadanda suka halarci zanga-zangar mata ne da yara, kuma kungiyar dake nuna goyon bayan falasdinu ce ta jagoranci zanga-zangar, fira ministan malesiya anwar...
    Rahotani sun bayyana cewa an rufe kamfanin kera makamai na HKI dake birtaniya mai suna  Elbit system sakamakon zanga-zangar da kungiyoyin sakai da masu goyon bayan palasdinu suka yi karkashin dokar yaki da ta’addanci a birtaniya. Wannan mataki yayi tasiri sosai a duniya inda dubban mutane ke ci gaba da matsin lamba ga gwamnatocinsu da su yanke duk wata alakar kasuwanci da isra’ila sakamakon ci gaba da kisan kare dangi kan alummar Gaza. Shi dai kamfanin Elbit System dake birtaniya na yanar gizo na Bristol ya fara aiki ne a karkashin wata yarjejeniyar tun a shekara ta 2019 zuwa ta2029  Kamfanin shi ne babban mai samar da jirage marasa matuka da sojojin Isra’ila ke amfani da su, musamman a yankin...
    ’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin NNPP na ƙasa ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo Wannan harin ya faru ne da daddare a ranar Juma’a, inda maharan haye a kan ɗaruruwan babura, suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje. Wani mazaunin garin, Malam Bukar, ya shaida wa manema labarai cewa: “Sun shigo suna ta kabarbari da harbi kan mai uwa...
    A jawabin ‘yan jaridu wanda darekta na bangaren manema labarai da al’amuran da suka shafi jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya Folasade Boriowo, abin ya bayyana; “A sashen Firamare , ‘yan aji 1- 3 za su byi darussa 9–10, su kuma wadanda suke aji 4–6 zasu yi darussa 10–12.Sai bagaren karamar Sakandare, abin ya fara ne daga darussa 12–14; Babbar Sakandare kuma dalibanta za su yi darussa 8–9; yayin da su kuma fannin fasaha za su yi darussa 9–11.”   Ahmad ya bayyana manhajar an tsara ta ne saboda an rage abubuwan da ta kunsa, aka kara maida hankali ga koyo domin tabbatar da cewa lamarin da ya shafi ilimi ya ci gaba da zama yana tafiya daidai zamanin da...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun hallaka jami’ai takwas na Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) da ke aiki a kamfanin siminti na BUA da ke Okpella, karamar hukumar Etsako East ta Jihar Edo. An kai harin na kwanton ɓauna ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a, 5 ga Agusta, 2025, lokacin da jami’an suka fita raka wasu ma’aikatan kamfanin ’yan ƙasar China guda biyar bayan kammala aikin gadi a ƙofar kamfanin. Wani babban jami’in rundunar a jihar ne ya bayyana haka a ranar Asabar, inda ya ce ’yan bindigar sun kuma jikkata jami’ai huɗu waɗanda ke karɓar magani a asibiti a halin yanzu.
    Tsagin Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ƙi amincewa da korar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Oginni Sunday ya raba wa ’yan jarida ranar Asabar. Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya gaskiya Bikin naɗin Sarkin Ibadan yan hana Musulmi Sallar Juma’a — MURIC Oginni ya yi Allah wadai da korar ɗan majalisar, yana mai cewa babu wata hujja kuma ba su ba da izini ko wani iko na ɗaukar wannan hukunci ba. Sunday ya ce tuni an sallami shugaban jam’iyyar na Kano, Hashim Dungurawa tare da rukunin tsagin Kwankwasiyya daga jam’iyyarsu ta NNPP. A bayan nan ne...
    Ƙungiyar Al’ummar Musulmi ta Kudancin Kaduna mai suna ‘Concerned Muslim Ummah’ ta zargi wasu manyan mutane a yankin da haifar da rarrabuwar kawuna da kuma juya tarihi domin cimma manufofin siyasa. A taron manema labarai da ta gudanar a Kaduna, ƙungiyar ta yi watsi da iƙirarin cewa Kudancin Kaduna na da Kiristoci ne kaɗai. Ta jaddada cewa Musulunci ya daɗe da wanzuwa a yankin tun ƙarnoni da suka gabata, inda ta ce Musulmi sun kai kusan kashi 40 cikin ɗari na al’ummar yankin. Ƙungiyar ta ce tashe-tashen hankula kamar na Zangon Kataf a 1992 da rikicin bayan zaben 2011 sun tabbatar da cewa rikice-rikicen yankin ba wai na yanzu ba ne. Bikin naɗin Sarkin Ibadan yan hana Musulmi Sallar Juma’a...
    Ƙungiyar Kare Hakkokin Musulmi ta Kasa (MURIC) ta buƙaci kwamitin shirya bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan da ya soke ranar Juma’a, 26 ga Satumba, da aka shirya gudanar da bikin. Ƙungiyar ta ce wannan rana za ta iya hana ɗaruruwan Musulmi gudanar da Sallar Juma’a da suke yi a kowane mako. Shugaban MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi wannan kira cikin wata sanarwa da aka aika wa manema labarai a ranar Asabar. Farfesa Akintola ya ce sau biyu irin wannan matsala ta taɓa faruwa a baya: lokacin da aka yi bikin miƙa sandar sarauta ga marigayi Olubadan Oba Akinloye Owolabi Olakulehin da kuma lokacin da aka kaddamar da sabuwar hanyar Iseyin zuwa Ibadan...
    Adadin Falasdinawa da suka yi shahada suna da yawa a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan sassa daban-daban na Zirin Gaza a jiya Asabar Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da gwabza kazamin yakin da take yi a zirin Gaza a rana ta 701, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama da kuma jikkatan wasu, da suke cikin masifar yunwa da kuma tilastawa Falasdinawa sama da miliyan biyu gudun hijira, a daidai lokacin da kasashen duniya suka yi shiru da kuma ci gaba da goyon bayan Amurka. Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda suka auka wa unguwanni da dama da makamai masu linzami,...
    Shugaban kasar Tunisiya ya bayyana cewa: Afirka na bukatar sabuwar hanya don tunkarar son ran ‘yan mulkin mallaka Shugaban kasar Tunusiya Qa’is Saeed ya bayyana a ranar Alhamis cewa: Tunisiya tana alfahari da hadin kan kasashen Afirka, kuma ta tsaya tsayin daka kan burin kafa kungiyar tarayyar Afirka mai inganci, duk kuwa da kalubalen da nahiyar ke fuskanta, kamar tashe-tashen hankula, fadace-fadace, laifuffukan safarar bil adama, da rashin samar da muhimman abubuwan rayuwa. A jawabin da ya gabatar a wajen bude taron baje kolin kasuwanci a kasar Aljeriya karo na 4, Saeed ya ce: “Nahiyar Afirka na da dimbin arziki, amma a lokaci guda tana fuskantar talauci da ke sanya matasanta shiga cikin hanyoyin safarar mutane.” Ya ci gaba da...
    Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira). Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Khalifofin mazhabobin Darikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya a Ibadan su ne suka jagoranci manyan malaman addinin Musulunci tare da dimbin mabiya wajen yin tattaki na tsawon kilomita 10 da ya zagaya wasu sassan birnin domin nuna farin ciki da murnar wannan rana. An ga ƙungiyoyin Musulmi daban-daban masu halartar zagayen Maulidi sanye da sutura iri ɗaya (amko) suna rera...
    Shugaban yace jihar Kaduna itace akan gaba daga cikin jihohi 36 da Birnin tarayya Abuja wajen tara kudin fatun layya Wanda ta tara Naira miliyan 23 sai jihar Kebbi wacce tazo ta biyu da Naira milliyan 21 sai kuma jihar Sakkwato wacce tazo ta uku.   Yace kudadan da aka tara za’ayi amfani dasu wajen ci gaba da aiwatar da Ayyukan Jami’ar musulunci mallakin kungiyar dake Hadejia a jihar Jigawa wacce ake kan ginawa.   Yace irin Wannan sadaka da alumma suke bayarwa zasu tabbatar da cewa anyi amfani da su yadda ya kamata musamman ginin Jami’ar mallakar kungiyar da wasu bangarori domin ciyar da addinin musulunci gaba.   Da yake bayani akan taron da kungiyar ta gudanar a jihar...
    Wannan ya nuna yadda a halin yanzu irin yanayin da masu zaman a gidajen Yarin ke ci gaba da zama a gidajen, musamman saboda rashin kulawa da su yadda ya kamata. Sai dai, Dakta Essien ya dora laifin kan rashin samu ‘yanci ga masu zaman gidan Jarun din. Gidajen Yarin kasar guda 246 yau shekaru 100 ke nan da gina su, wadanda akasarinsu, duk sun tsufa, inda kuma dakunan da ‘yan jarun din ke kwana, ba su da wani sararin da masu zaman jarun din za su iya wani watayawa. A cewar Essien, jimlar masu zama a gidan jarun ciki har da wadanda aka ajiye da suke jiran Shari’a, sun kai 81,122, wanda a ka’ida kamata ya yi su kai...
    “Abin da Jibrin ya faɗa ba wai adawa da jam’iyya ba ne. Kowane ɗan siyasa yana da ‘yancin sauya jam’iyya. Ko Shugaba Bola Tinubu ya taɓa sauya jam’iyya kafin ya zama shugaban ƙasa,” in ji Doguwa. Ya kuma gargaɗi Dungurawa da ya daina korar ‘ya’yan jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba, inda ya ce za su kai ƙara kotu idan ɓangaren nasa ya ci gaba da yin haka. Wannan sabon rikici ya sake nuna yadda NNPP ke ƙara tarwatsewa a Kano tun bayan zaɓen 2023, inda har yanzu ake taƙaddama kan shugabanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    Game da babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya kin tafarkin murdiya, wanda aka gudanar a ranar 3 ga wannan wata, mutane daga kasa da kasa masu halartar bikin sun ba da ra’ayoyinsu ciki har da kalmomin hadin kai, da yin kokari tare, da sauransu don nuna kyakkyawar fata ga makoma. Bayan shekaru 80 da gama yakin duniya na biyu, an canja burin dan Adam. Zaman lafiya da samun bunkasa sun zama babban jigo na halin yanzu, kasa da kasa suna kokarin samun zamanantarwa. Amma a sa’i daya kuma, ra’ayin mai karfi ya cinye maras karfi ya sake bullowa, an kawo illa ga...
    Wasanni uku ne kacal suka rage a rukunin. Ƙasar da ta fi kowa maki a ƙarshen zagaye ita ce kawai za ta je gasar Kofin Duniya da za a yi a Amurka, Mexico da Canada. Saboda haka, dole ne Nijeriya ta doke Afirka ta Kudu don cikar burinta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A jiya Jumma’a 5 ga wannan wata, babban taron MDD karo na 79 ya jefa kuri’a tare da zartas da kudurin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da kasar Sin da dukkan kasashe membobin kungiyar SCO kimanin 40 suka gabatar tare. Kudurin ya amince da muhimmiyar rawar da kungiyar SCO ta taka wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasa da yin imani da juna da kuma hadin gwiwa a yankin, kana ya yaba wa kungiyar SCO bisa kokarin nuna goyon baya ga ayyukan MDD, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da tsarin MDD. Mukaddashin shugaban tawagar dindindin ta Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana yayin da yake bayani game...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana mamakinsa game da korarsa daga jam’iyyar NNPP. Shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana korar Kofa kan zargin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa da kuma rashin biyan kuɗaɗen da ake bin sa. Boko Haram sun kashe gomman mutane da sojoji a ƙauyen Borno NNPP ta kori Kofa daga jam’iyyar, ta yi barazanar maka shi a kotu Ya kuma yi barazanar kai shi kotu idan bai biya kuɗaɗen da ake bin sa ba. A martaninsa, Kofa, ya ce: “Korata daga NNPP ta zo da mamaki sosai. Ban yi tsammanin tattaunawar da na yi a kafafen yaɗa labarai za ta jawo irin wannan hukunci ba. “Babu wata gayyata da...
    Yawancin waɗanda aka kashe sun fito ne daga sansanin ’yan gudun hijira da ke Makarantar Sakandare ta Kimiyya ta Gwamnati. Wata majiyar ta ce: “Aƙalla mutanen gari 56 da sojoji biyar aka kashe. An ƙone gidaje fiye da 20 da kuma motoci 10. Har yanzu ana neman wasu da suka ɓace.” Har yanzu, babu wata sanarwa da hukumomi suka fitar game da harin. A ranar Asabar, Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara Bama domin samun cikakken bayani da kuma jajanta wa waɗanda abin ya shafa. A shekarar 2004, Boko Haram ta mamaye garin Bama tare da ayyana shi a matsayin wani ɓangare na “daularsu” kafin daga baya dakarun sojin Nijeriya suka ƙwato garin. Daga kanmu, magana...
    Ana zargin mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Darul Jamal da ke Karamar Hukumar Bama, a Jihar Borno, inda suka kashe gomman mutane da sojoji. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Juma’a. ’Yan bindiga sun kashe mutum 7 a Katsina Yadda makarantu ke tatsar kuɗaɗe daga iyayen ɗalibai Mutane da hukumomin tsaro sun tabbatar da aukuwar harin. A kwanakin baya, Gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum, ya mayar da wasu mutane ƙauyen. Shekaru da dama suna zaman ’yan gudun hijira a sansanoni daban-daban kafin a dawo da su. Wani daga cikin mazauna yankin ya ce: “Rana ce mai matuƙar baƙin ciki. Ɗana da ɗan uwana sun mutu. “Mun kirga gawarwaki 63 kuma mutane da dama...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga zaman taro na 15 na kwamitin sada zumunta da bunkasa zaman lafiya da ci gaba tsakanin Sin da Rasha, da aka gudanar yau Asabar a birnin Vladivostok na Rasha. Xi ya jaddada cewa, tun kafuwarsa a cikin shekaru 28 da suka gabata, kwamitin sada zumunta da bunkasa zaman lafiya da ci gaba tsakanin Sin da Rasha, ya nace ga bin turbar ainihin burin da ake so da manufar karfafa sada zumunta da hadin gwiwa, tare da cikakkyar hidimta wa dukkan yanayin dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha, da kafa ginshiki mai karfi na raya huldar kasashen biyu a tafarkin ra’ayin al’umma. Ana fatan kwamitin zai dauki wannan taro...