2025-07-11@12:22:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 117
«ta ware Naira biliyan»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...
Yanzu haka, an kara tura manyan injuna domin gudanar da aikin ceto a wurin da zaftarewar kasa ta auku a lardin Sichaun na kasar Sin. Da farko za su kwashe duwatsu da kasa da suka lullube wurin, kuma da zarar an ga alamun gini, za a sanar da ma’aikatan dake wurin domin kara bincike. Zuwa karfe 11:00 na safiyar yau agogon Beijing, an tabbatar da kasa ta binne gidaje 10 da wata masana’ata 1, sanadiyyar zaftarewar kasar, wadda ta auku a gundumar Junlian ta birnin Yibin na lardin Sichuan. Haka kuma, mutum 1 ya rasa ransa yayin da 28 suka bata. Zuwa yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da aikin ceto. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu. Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a – hanyar Tsangamawa. Hanyar Tsangamawa da ke Babban Rafi, Karamar Hukumar Danja, Jihar Katsina, ta haddasa mutuwar mata masu juna biyu da jariransu, musamman a lokacin damina. Duk da yawan koke da rokon gwamnati, har yanzu ba a dauki matakin gyara hanyar ba. A wata hira da suka yi da Radio Nigeria, wasu daga cikin matan yankin sun bayyana cewa mata masu...
Kazalika, a Arewacin Nijeriya, Robar Tumatir mai nauyin kilo 25 yanzu, ana sanar da ita kan Naira 6,500. Shugabar kungiyar masu noman Tumatair da sarrafa shi ta kasa, Rabiu Zuntu ta sanar da cewa, an samu girbin Tumatir mai yawan gaske, duba da cewa; yanzu ana cikin watan Fabrairu, lokacin da ake samun yawaitarsa. A cewar tata, tarin yawan nasa ne ya sa aka samu faduwar farashinsa a kasuwanni, wannan dalili ne ma ya sanya, don gudun kada manoman su yi asara; suke sayar da shi kan farashi mai sauki. “Daga watannin Janairu, Fabrairu zuwa Maris; ana samun kwantan Tumatir, yanzu kuma muna da injinoni masu kyau na sarrafa Tumatirin, wanda hakan zai sa a samu raguwar farashin”, in ji...
Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi. An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan ƙungiyar Ruben Amorim ya bayyana a matsayin babbar matsala. A ranar Alhamis ƙungiyar ta ce har yanzu ana duba yanayin raunin domin sanin yadda ya fi dacewa a yi masa magani da kuma tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinya. Sanarwar ta ce kowa a ƙungiyar yana yi wa Lisandro Martinez fatan warkewa sarai, kuma za su ci gaba da tallafa masa a kodayaushe. Rashin...
Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja Gobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya buƙaci makarantu...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ya yi shahada, a yakin baya-bayan nan kan kasar Lebanon, shi ne tsohon wakilin mai martaba Imam Khamenei a kasar Lebanon kafin shahadarsa.
Kasar Afirka Ta Kudu ta ga yadda Palasdinawa suka jajirce wajen kare kansu daga HKI ne, ya sa ta gurfanar da HKI a gaban kutun ICC don kawo karshen kissan kiyashin da yahudawan suke masu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kasar Afirka ta gudu dai tana dade tana goyon bayan masu gwagwarmayan neman yencinsu a duniya daga ciki da da kasar Falasdinu da aka mamaye. Har ila yau da kuma ganin tarihin da kasar take da shi, na yaki da wariyar launin fata a kasar, duk sun hadu sun karfafa ta wajen daukar wannan matakin kan HKI. Jakadan kasar Afirka ta kudu a nan Tehran, Francis Moloi ne ya fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Iran...
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 “Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan...
Majalisar Zartarwa ta ware naira biliyan 4.8 domin yaƙi da yaɗuwar cutar HIV a Nijeriya. Wannan na daga cikin matsayar da aka cimma a taron Majalisar Zartarwa da ya gudana a ranar Litinin kamar yadda Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar. Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa Ministan ya ce wannan yana daga cikin manufofin gwamnatin na inganta kiwon lafiya a matakin farko. A cewarsa, an tsara kashe kuɗaɗen ne a fannin ɗaukar ma’aikatan lafiya da ba su horo domin samun ƙwarewa da kuma tabbatar da an bayar da kulawar da ta dace domin hana yaɗuwar cutar HIV a sassan ƙasar....
An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara. Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar aiki ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirgar bikin bazara, wanda aka fi sani da chunyun. Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe Zirga-zirgar fasinjoji ya karu tun daga ranar 30 ga watan Janairu, inda adadin tafiye-tafiyen ya zarce miliyan 300 a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da Gwamnatin Kano ta sanar cewa ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aura da ’yan mata da zawarawa a jihar batun ke ta shan suka daga ɓangarori daba-daban. Wasu na ganin jihar na da wasu buƙatun da suka fi auren gatan muhimmanci da ya kamata gwamnatin ta fi mayar da hankali a kansu. NAJERIYA A YAU: Anya Jam’iyyar PDP Za Ta Kai Labari A Fagen Siyasar Najeriya Kuwa? DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya A Yau na wannan rana ya yi nazari ne kan dalilan da Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aurar da ’yan mata da...
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna. Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Kazakhstan a wata ganawa da firaministan kasar Kazakhstan Olzhas Bektenov. A yayin taron na ranar Alhamis, Aref ya bayyana bukatar samar da karin kwamitocin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Bayan goron gayyata day a samu a hukumance daga Bektenov, mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya isa kasar Kazakhstan a ranar Alhamis domin halartar taron koli na shugabannin gwamnatoci mambobi a kungiyar tattalin arzikin Eurasia (EAEU) da taron Almaty Digital Summit 2025, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 1 ga Fabrairu. Iran wadda a baya-bayan nan ta samu matsayin mamba mai sanya ido a...

Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...