Martinez zai yi jinya har Karshen kaka
Published: 7th, February 2025 GMT
Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi.
An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan ƙungiyar Ruben Amorim ya bayyana a matsayin babbar matsala.
A ranar Alhamis ƙungiyar ta ce har yanzu ana duba yanayin raunin domin sanin yadda ya fi dacewa a yi masa magani da kuma tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinya.
Sanarwar ta ce kowa a ƙungiyar yana yi wa Lisandro Martinez fatan warkewa sarai, kuma za su ci gaba da tallafa masa a kodayaushe.
Rashin Martinez babban ƙalubale ne ga Amorim wanda ke fama kan ganin ya dawo da ƙungiyar ta Old Trafford kan ganiyarta.
Yanzu United tana ta 13 a teburin Premier bayan kashin da ta sha a hannun Palace – rashin nasarar da shi ne na bakwai a wasa 13 na gida a bana.
A gobe Juma’a ne United za ta karɓi baƙuncin Leicester City, a karawar zagaye na huɗu ta cin kofin FA.
Martinez ya tafi jinyar ne yayin da United ɗin ke ɗari-ɗarin dawo na Luke Shaw, da ake ganin bai gama warkewa ba sarai, daga raunin da ya ji na ƙarshe.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Wasannni
এছাড়াও পড়ুন:
Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?
Duk da cewar an yi yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, rikici ya sake ɓarkewa bayan NUPENG ta ce Dangote bai cika alƙawari ba.
Amma matatar ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa ma’aikatanta na da damar shiga ƙungiya idan sun so, amma ba dole ba ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp