Aminiya:
2025-07-31@17:46:14 GMT

Sarki Sanusi ya ziyarci unguwar da mutane suka rasu a dalilin rusau

Published: 5th, February 2025 GMT

Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon.

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43

“Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan ya zama karo na ƙarshe da irin haka za ta sake aukuwa.”

Sarkin ya buƙaci mazaunan da su kai zuciya nesa su bai wa mahukunta na shari’a su yi aikin da rataya a wuyansu, yana mai cewa babu abin da rikici zai haifar face ƙarin wahala.

“A duk lokacin da tarzoma ta tashi mutanenmu ne ke kwanana ciki. Babu yadda za a yi zubar da jini ko tashin-tashina su iya warware wannan matsala. Dole ne mu haɗa kai mu kare rayuwa da dukiyar al’ummarmu.

Sarkin ya hori dukkan ɓangarorin da lamarin ya shafa su warware tankiya da ke tsakaninsu ta hanyar shari’a tare da gabatar wa kotu ƙwararan hujjoji

A ƙoƙarin shiga tsakani don ganin an zauna lafiya, Sarkin ya sanar da kafa wani kwamiti da zai yi ruwa da tsaki da zai haɗa da wakilan dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da ciki har da Gwamnatin Kano, mahukuntan Jami’ar Bayero da jami’an tsaro da kuma shugabannin yankin.

Sarkin ya ƙara nanata kiran a zauna lafiya yana mai cewa babu wani fili ko wata dukiya da za ta yi daidai da darajar ran ɗan Adam.

Aminiya ta ruwaito cewa tuni dai ƙura ta lafa kuma jama’a sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum bayan ƙazamin rikicin da aka yi tsakanin mahukunta da mazauna yankin.

Yadda rikicin ya auku

Aƙalla wasu mutum huɗu aka ce riga mu gidan gaskiya sakamakon ƙazamin rikicin da ya hautsine tsakanin mahukunta da mazauna unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.

Bayanai sun ce an harbe mutanen huɗu ne yayin da suka fito tirjiya kan rusau ɗin gine-ginensu da jami’an hukumar tsara birane ta Jihar Kano KNUPDA suka aiwatar.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa galibin gidajen da rusau ɗin ya shafa tuni KNUPDA ta shafa musu alamar cewa aiki zai biyo ta kansu.

Ana dai zargin cewa gine-ginen aƙalla 40 da mahukuntan suka rushe an yi su ne a kan fulotan Jami’ar Bayero da ke Kano.

Sai dai wani mazaunin yankin da ya zanta da Aminiya, ya ce tun da jimawa Hukumar ta KNUPDA ta warware wannan matsala kuma ta jaddada musu cewa a halastaccen matsuguninsu suke domin bai shiga harabar jami’ar ba.

“Mun jima da warware wannan matsala da KNUPDA. Sun tabbatar mana cewa gine-ginenmu ba su shiga harabar jami’ar ta Bayero ba.

“Amma kwatsam sai ranar Lahadi da daddare jami’an KNUPDA suka zo suka fara rusau.

“A yayin da wasu daga cikin mazauna suka yi ƙoƙarin tirjiya ne suka harbi mutum huɗu da yanzu an yi musu jana’iza. Wannan abun takaici ne.

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Manajan Darekta na KNUPDA amma lamarin ya ci tura.

Kazalika, wakilinmu da ya ziyarci ofishin KNUPDA ya tarar da shi fayau a yayin da duk manyan jami’an sun ƙauracewa zuwa aiki sakamakon fargabar abin da ka iya zuwa ya komo kamar yadda wani ƙaramin ma’aikaci ya tabbatar.

“Ana cikin wani yanayi na fargaba a ofishin nan. Shi ya sa ko wurin ajiyar motoci ya zama fayau don duk manyan ma’aikatan babu wanda ya shigo.

“Yanzu haka ƙananan ma’aikata ne kawai suke zaman dabaro a ofishin ba tare da sanin madafar da za a kama ba.

Wani babban Darektan KNUPDA da Aminiya ta tuntuɓa, ya ce ba ma’aikatansu ne suka yi rusau a unguwar ba, inda ya ba da tabbacin cewa jami’ai ne daga Ma’aikatar Ƙasa da Tsara Birane ne suka aiwatar da aikin.

Haka kuma, wani jami’i daga ma’aikatar wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce wuraren da aka yi rusau mallakin Jami’ar Bayero ne kuma nan gaba kaɗan za a fitar da sanarwa a hukumance.

Mutum uku ne suka mutu — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta bakin Kwamishinan Labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ta tabbatar da cewa mutum uku ne suka mutu yayin da jami’an tsaro aƙalla 30 suka jikkata a sanadiyyar tankiyar da auku a dalilin rusau ɗin.

Kwamishinan ya bayyana cewa tun farko Jami’ar Bayero ce ta nemi gwamnatin ta shiga lamarin, wanda jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, DSS da na Sibil Difens suka yi ruwa da tsaki.

Waiya ya ce an shafe fiye da shekaru 40 ana wannan kwakwazo kan halascin mallakar fulotan tsakanin mazauna yankin da kuma jami’ar ta Bayero.

Sai dai ya ce jami’ar ta fuskanci ƙalubale a ƙoƙarin da ta riƙa yi don ganin ta karɓe haƙƙinta duk da gargaɗi da wa’adin da aka bayar na neman mazaunan su tashi.

Kwamishinan ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da salwantar rayukan da aka samu duk da cewa mazauna yankin sun wuce gona da iri.

Sai dai a cewar Kwamishinan, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa jami’an tsaro ’yancin kare kansu a duk lokacin da rayuwarsu ta fuskanci barazana.

Ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa da cewa gwamnati za ta gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jami ar Bayero Jihar Kano Rimin Auzinawa Rimin Zakara Sarki Sanusi II Jami ar Bayero jami an tsaro da lamarin ya

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri

Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu.

Daga bisani ’yan sanda sun sun bi su, inda suka fatattake su suka gudu zuwa cikin kungurmin Dajin Madam.

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da mutuwar mutanen a yayin taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Nahutan Darazo a kokarinsa na sasanta rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya da ya yi sanadin jikkatar wassu mutane a Darazo.

Gwamnan ya kuma nuna matuqar damuwarsa kan bisa yadda mafarauta da a baya suke goyon bayan ayyukan tsaro na kare dazuzzukan jihar a yanzu haka suka shiga cikin rikici da manoma.

Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata  ’Yan sa-kai aƙalla 100 da ’yan sanda 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati

Gwamna ya ce gwamnatinsa tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da kungiyoyin ’yan banga sun dukufa wajen kwato dabbobin da aka sace da kuma wanzar da zaman lafiya a yankunan karkara.

Ya yaba wa mafarautan yankin bisa ci gaba da goyon bayan da suke bayarwa wajen tabbatar da kare dazuzzukan. “Kun taimaka mana wajen kare dazuzzukanmu a Toro, Ningi, Duguri, Yankari, Kirfi, ba a Darazo kadai ba.

“A ranar Litinin ne ’yan bindiga suka kashe mutane biyar a Dajin Madam, wanda ke kan iyaka da Taraba, Filato, da Bauchi-Alkaleri.

“Me ya sa ba ku taimaka mana a can ba? Muna fuskantar kalubale sosai a dazuzzukanmu. Bauchi tana da dazuzzukan sama da hekta miliyan hudu da tsaunukan da ba kowa zai iya shiga ba, sai ku.”

Gwamna Bala ya alaqanta wannan tashin hankali da kwararowar jama’a daga wasu jihohi zuwa Bauchi, tare da qaruwar yawan jama’a, lamarin da ya qara matsin lamba ga kasa da albarkatun kasa.

Yace Yan bindigan yanzu Suna cikin Jihar Taraba ne,kuma Gwamnan Taraba munyi Magana dashi zamu Yi hadin guiwar Domin a fatattakesu a wurin”

Kan rikicin manoma da makiyaya a Darazo da Sade kuma, gwamna yya kaddamar da wani babban kwamiti da zai binciki rikicin na dajin Aliya, Yautare, da Farin Ruwa na Karamar Hukumar Darazo.

Mataimakin gwamnan jihar, Muhammad Auwal Jatau, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin ne ya kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati da ke Bauchi, inda ya kuma bukaci ’yan kwamitin da su gudanar da ayyukansu cikin himma, adalci, da rashin son kai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC
  • Shugabannin Arewa Sun Tattauna Sabon Hanyar Ci Gaba – Minista Uba Maigari Ya Yaba
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • APC Zamfara Ta Taya Sabon Sarkin Katsinar Gusau Murna
  • Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata 
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • ’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati
  • Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa