Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa Iran, ya kara haifar da shakku game da aniyar Washington na neman hanyar diflomasiyya.

“Don ci gaba a kan wannan tafarki dole ne dayan bangaren ya nuna kyakkyawar niyya cewa da gaske ya ke,” in ji shi, kafin ya ce: “Iran, a matsayinta na mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), dole ne ta ci moriyar makamashin nukiliya don dalilai na zaman lafiya.”

Ministan na Iran ya kara jaddada cewa, domin cimma daidaito, da kuma dawwamamiyar yarjejeniya, tilas ne dukkan bangarorin su kaurace wa duk wasu bukatu da suka saba wa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.

Abbas Araghchi ya kuma yi tsokaci kan gazawar Amurka wajen cika alkawuran da ta dauka karkashin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015, yana mai jaddada cewa dole ne sauran bangarorin su ba da tabbacin dage takunkumin da aka kakaba iran.

A nasa bangaren babban sakataren MDD ya jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa har sai an samu sakamako.

Mr. Guterres ya kuma yaba da sabbin hanyoyin da ministan harkokin wajen Iran ya bi wajen bayyana abubuwan da ke faruwa a tattaunawar ta tsakanin Iran da Amurka.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.

Dangane da sanarwar da Amurka ta fitar ta kakaba takunkumi kan jami’an hukumar kare hakkin Falasdinawa da mambobin kungiyar ‘yantar da Falasdinu, Guo Jiakun ya bayyana cewa, Sin ta kadu da hakan, kuma tana nuna takaici da rashin fahimta cewa, Amurka ta yi watsi da kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya ga Falasdinu. Kuma kasar Sin ta dage wajen goyon bayan tsari mai adalci ta al’ummar Falasdinu don maido da halastaccen hakkin al’ummar, kuma za ta ci gaba da yin namijin kokari a wannan fanni tare da sauran kasashen duniya.

Dangane da umarnin da shugaban Amurka Trump ya bayar na kara haraji kan kasashen duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin na adawa da cin zarafi na kudaden haraji ba zai canza ba, domin babu wanda zai yi nasara a yakin haraji, kuma ra’ayin amfani da kariyar cinikayya yana cutar da muradun kowane bangare.

Dangane da rahotannin da ke nuni da cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare ta yanar gizo kan kasar Sin, Guo Jiakun ya ce, wannan ya fallasa munafuncin Amurkan na koken “kama barawo” a fannin tsaron intanet. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kare tsaron intanet.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi: Abokantaka Da Ke Tsakanin Iran Da Pakistan Wata babbar Jari Ce Nan Gaba
  • Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine
  • Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna
  • Osimhen Ya Kammala Komawa Galatasaray
  • Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya
  • Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres
  • Man Utd Na Tattaunawa Da Golan PSG, Chelsea Ta Nace Wa Garnacho
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata
  • Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine