An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis
Published: 21st, April 2025 GMT
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya, FIGC, ta sanar da jingine wasannin gasar gasannin Serie A, B, da C, saboda alhinin rasuwar shugaban ɗarikar Katolika, Fafaroma Francis.
Shugaban hukumar FIGC, Gabriel Gravina ya ce, “Harkar ƙwallon ƙafa ta Italiya tana taya jimami ga miliyoyin al’umma kan rasuwar Mai Alfarma Fafaroma Francis.
Ƙungiyoyin da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Juventus, Lazio, Parma Calcio, Cagliari, Fiorentina, Genoa, Torino, Udinese.
A safiyar Litinin 21 ga Afrilu ne Fadar Cocin Katolika da ke Vatican City ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis mai shekaru 88, wanda ke shugabantar Cocin, kuma shugaban birnin Vatican City.
Miliyoyin mutane a Italiya da kuma faɗin duniya sun shiga alhini saboda rasuwar malamin adinin.
Wannan ya sa aka ɗauki matakin jingine duka lamuran wasanni don nuna girmamawa ga rasuwar.
An soke duka wasannin da aka shirya bugawa ranar Litinin ta Easter, inda a babbar gasar Serie A ta Italiya, Juventus za ta kara da Parma, Lazio da Genoa, Torino da Udinese, Cagliari da Fiorentina.
Haka ma a ƙananan gasannin Italiya na Serie B da Serie C su ma an soke buga wasannin da aka tsara a baya.
Hukumar ta FIGC ta fitar da sabon jadawali da ke nuna cewa za a buga wasannin a ranar 23 ga wannan watan.
A halin yanzu dai galibi ƙungiyoyin suna da sauran wasanni biyar ne kafin kammala kakar gasanni ta bana.
Tarihi ya nuna cewa ko a 2005 da Fafaroma John Paul II ya rasu, an ɗauki irin wannan mataki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fafaroma Francis Italiya Wasanni Fafaroma Francis
এছাড়াও পড়ুন:
Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
Wata kotu da ke birnin Madrid ta yi watsi da ƙarar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Turai UEFA, LaLiga da Hukumar Kwallon Kafa ta Sipaniya suka shigar kan ƙin amincewa da gasar Super League.
Wannan yana nufin yanzu Real Madrid da sauran ƙungiyyoyin za su iya neman diyyar kudi Euro Milyan 4.
Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar Christopher MusaReal Madrid ta ce, wannan hukuncin ya tabbatar da cewa UEFA ta karya dokokin gasa, kuma ƙungiyyoyi sun rasa maƙuden kuɗaɗe tun daga lokacin da aka dakatar da gasar.
Gasar wacce aka shirya farawa a shekarar 2021 tare da manyan ƙungiyoyin Turai, an yi hasashen zata samar da kusan Yuro miliyan 200 ga ƙungiyoyin da suka shiga.
A nata martanin hukumar UEFA ta dage cewa wannan sabon hukuncin ba ya nufin an dawo ko an amince da a buga gasar Super League ba ne.