Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Published: 30th, January 2025 GMT
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar.
Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi.
Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya.
Yansan da a birnin Stokhom sun tabbatar da c ewa sun ji karar bindiga a kudancin birnin a daren laraba, amma a lokacinda suka isa wurin sai suka sami wani mutum da harbin birnin. Amma bai dade bay a mutu.
Mai sharia Goran Lundahl na birnin ya tabbatar da cewa gawar ta Sewan ne amma har yanzun basu da masaniya kan yadda aka kashe shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon: Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut
Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu.
Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara.
A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata.
A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama.
Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.