Jajircewar Mutatnen Gaza Ne Ya Sa Afirka Ta Kudu Ta Shigar Da Karar HKI A Kotun Kasa Da Kasa Ta ICC
Published: 5th, February 2025 GMT
Kasar Afirka Ta Kudu ta ga yadda Palasdinawa suka jajirce wajen kare kansu daga HKI ne, ya sa ta gurfanar da HKI a gaban kutun ICC don kawo karshen kissan kiyashin da yahudawan suke masu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kasar Afirka ta gudu dai tana dade tana goyon bayan masu gwagwarmayan neman yencinsu a duniya daga ciki da da kasar Falasdinu da aka mamaye.
Jakadan kasar Afirka ta kudu a nan Tehran, Francis Moloi ne ya fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Iran Press’ na kasar Iran a nan Tehran a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa, wannan dan kadan Kenan daga abinda kasar Afrika ta kudu za ta iya gabatarwa da karfafa wa al-ummar Falasdinawa.
Yakin gaza dai ya farkar da mutane da dama a duniya gaba daya, kan al-amarin Gaza da kuma yadda HKI ta ke amfani da dukkan karfinta a cikin watannin 15 da sukagabata don kashe Falasdinawa da kuma rusa yankin nasu gaba daya.
Kasashen duniya musamman ita Afrika ta Kudu ta dauki wannan matakin ne, saboda yadda HKI ta ki mutunta dokokin kasa da kasa, musamman wadanda suka shafi
mutuncin bil’adama da kuma hakkin rayuwa ga Falasdinaw.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
A cewarsa, wajibi ne shirin ya mayar da hankali kan burin cimma zamanantarwa irin ta gurguzu da nufin gina babbar kasa da samun ci gaba wajen farfado da ita. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, wanda shi ne daftarin dake zaman jigon jagorantar ci gaba na matsakaici da dogon zango a bangaren tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, yana zayyana baki dayan burikan kasar da manyan ayyuka da manufofin da ake aiwatarwa a dukkan bangarori cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp