Leadership News Hausa:
2025-11-02@17:03:57 GMT

An Tura Manyan Injuna Domin Shiga Aikin Ceto A Lardin Sichuan

Published: 10th, February 2025 GMT

An Tura Manyan Injuna Domin Shiga Aikin Ceto A Lardin Sichuan

Yanzu haka, an kara tura manyan injuna domin gudanar da aikin ceto a wurin da zaftarewar kasa ta auku a lardin Sichaun na kasar Sin. Da farko za su kwashe duwatsu da kasa da suka lullube wurin, kuma da zarar an ga alamun gini, za a sanar da ma’aikatan dake wurin domin kara bincike.

Zuwa karfe 11:00 na safiyar yau agogon Beijing, an tabbatar da kasa ta binne gidaje 10 da wata masana’ata 1, sanadiyyar zaftarewar kasar, wadda ta auku a gundumar Junlian ta birnin Yibin na lardin Sichuan.

Haka kuma, mutum 1 ya rasa ransa yayin da 28 suka bata. Zuwa yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da aikin ceto. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.

Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.

Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

Ya ce an tsara wannan asusu  ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.

Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.

Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin  ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.

Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a  wuraren.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara