Iran ta yi ta’aziyya game da rasuwar Paparoma Francis
Published: 22nd, April 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya mika ta’aziyya game da rasuwar shugaban ‘yan darikar katolika na duniya Paparoma Francis.
A wani sako da ya aike a jiya Litinin, Pezeshkian ya ce Paparoma Francis a matsayinsa na shugaban darikar Roman Katolika ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yada koyarwar Yesu Almasihu.
Shugaban ya ce Paparoma ya yi kokari wajen samar da zaman lafiya a duniya, da yekuwar samar da adalci, da ‘yanci, da mu’amala da tsaro a tsakanin addinai.
Daya daga cikin shi ne bayyanannen matsayinsa na yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza da kuma kiran da ya yi na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa mata da kananan yara Falasdinawan da ba su ji ba ba su gani ba.
A jiya Litini ce Cocin Vatican ta sanar da rasuwar shugaban majami’ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya.
A shekarar 2023 ne cocin ya zabi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan mukamin.
Fafaroman ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya, inda a baya ya shafe makonni a wani asibiti, inda aka bayyana cewa yana fama da sanyin hakarkari mai tsanani.
Francis, shi ne Paparoma na 266 na Cocin Roman Katolika, kuma an bayyana cewa ya rasu ne sakamakon bugun jini.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa.
Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba.
Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe uku na turai wato Faransa da Jamus da kuma Burtaniya, saboda samun fahintar juna da kuma daukewa kasar takunkuman tattalin arzikinn da turawan suka dora mata.