Lalacewar Hanya Na Janyo Yawan Mutuwar Mata Masu Juna Biyu Da Jariransu A Katsina
Published: 8th, February 2025 GMT
Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu.
Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a – hanyar Tsangamawa.
Hanyar Tsangamawa da ke Babban Rafi, Karamar Hukumar Danja, Jihar Katsina, ta haddasa mutuwar mata masu juna biyu da jariransu, musamman a lokacin damina.
Duk da yawan koke da rokon gwamnati, har yanzu ba a dauki matakin gyara hanyar ba.
A wata hira da suka yi da Radio Nigeria, wasu daga cikin matan yankin sun bayyana cewa mata masu juna biyu da jariransu ne suka fi fuskantar barazana, musamman a lokacin damina, saboda wahalar kai su asibiti sakamakon mummunan halin da hanyar take ciki.
Duk da cewa akwai cibiyar kiwon lafiya a yankin, ginin ya lalace, kuma yawancin ma’aikatan jinya da na lafiya ba sa iya zuwa aiki akai-akai saboda matsalar hanya.
Wata uwa mai ‘ya’ya hudu a yankin, Hajara Ibrahim, ta bayyana bakin cikinta, tana mai cewa har yanzu babu wata gwamnati da ta nuna musu tausayawa, duk da cewa suna da hakkin rayuwa mai inganci.
Malama Tayyiba Muktari daga Babban Rafi ta bada labarin yadda ta tsira da kyar a cikin juna biyunta na baya, inda ta ce nufin Allah ne ya sa ta tsira, sannan ta roki Gwamnatin Jihar Katsina da ta dauki matakin gaggawa kan hanyar.
Haka kuma, wata mata daga yankin, Fatima Abdullahi, ta koka kan yadda mummunan yanayin hanyar ke hana mazajensu fita neman abin dogaro da rayuwa.
Haka nan, wani tsohon jami’in lafiya a Jihar Katsina, Dr. Haruna Abubakar, ya bukaci Gwamnatin Jihar Katsina da ta saka aikin gina hanyar Tsangamawa, Babban Rafi a kasafin kudin bana saboda mahimmancinsa ga al’umma.
Matan yankin sun roki Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda, da ya tausaya musu da iyalansu ta hanyar gyara hanyar.
Duk da cewa hanyar tana da kimanin kilomita 23 kacal, gwamnatocin baya sun kasa gyarata. Dole ne gwamnati ta fara fifita yankunan karkara wajen bayar da kwangiloli domin inganta rayuwar al’umma.
Cov/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jariransu
এছাড়াও পড়ুন:
Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba.
Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah ya jikansu da rahama ya gafarta musu kurakuransu, ya kuma saka musu da Aljannar Firdaus”.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA